Fulani Makiyaya Sun Kai Hari Jihar Benue, Sun Kashe Masu Ibada Ranar Juma'a
- Ana fargabar wasu Fulani makiyaya dauke da mugayen makamai sun farmaki jihar Benue, suka kashe 10 da ke kan hanyar coci
- Wani mazauni ya bayyana cewa an kai harin da misalin karfe 6:00 na safe, inda aka harbe mata da yara, tare da jikkata mutane 25
- Kwamishinan yada labarai ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa an samu yawaitar makiyaya dauke da makamai a kwanaki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Benue - Wasu mahara dauke da mugayen makamai da ake zargin Fulani makiyaya ne sun kai wani sabon hari da safiyar ranar Juma’a, a jihar Benue.
An ce sun yi wa wasu Kirista kwanton-bauna yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa bikin tunawa mutuwar Yesu Almasihu, inda suka kashe mutane 10 nan take.

Asali: Twitter
Makiyaya sun farmaki masu ibada Benue
Leadership ta rahoto cewa mabiya addinin Kirista din da suka nufi coci don gudanar da ibadar 'Good Friday' sun gamu da ajalinsu ne a unguwar Gbagir da ke karamar hukumar Ukum.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mazaunin yankin mai suna Tersur Iornenge ya shaidawa jaridar ta wayar salula cewa maharan dauke da manyan makamai sun kai harin ne da safiyar Juma’a.
“Maharan sun mamaye unguwarmu da misalin karfe 6:00 na safe yayin da jama’a ke kan hanyar zuwa coci don gudanar da ibadar 'Good Friday', suka bude masu wuta,”
- Tersur.
Makiyaya sun kashe masu ibada 10
Majiyar ta kara da cewa jama’a sun kwashi gawarwakin wadanda aka kashe zuwa fadar sarkin garin domin nuna rashin jin dadin su, tare da korafin cewa gwamnati ta yi watsi da su.
Majiyar ta kara da cewa:
“Maharan sun kai hari a wani kauyen makwabta, Chito, a ranar Alhamis, suka kashe manoma biyu. A yau (Juma'a) kuma sun shigo garinmu, suka kashe manoma 10 ciki har da mata da yara."
Ya kara da cewa fiye da masu ibadar 25 ne suka jikkata da raunuka iri-iri yayin da wasu da dama ba a san inda suke ba har yanzu.
Gwamnatin Benue ta magantu kan harin makiyayan
Da yake tabbatar da harin da kashe-kashen, kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar, Mathew Abo, ya ce an gano gawarwaki biyar yayin da wasu uku ke karbar magani a wani asibiti a garin Zaki Biam.
A cewar Mathew Abo:
“Akwai yawaitar Fulani makiyaya dauke da makamai a karamar hukumar Ukum a ‘yan kwanakin nan kuma suna shigar da shanu da tumaki masu yawa cikin gonakin mutane.”
Kwamishinan ya ce hare-haren sun shafi kananan hukumomin Logo da Katsina-Ala, duk da cewa yanzu haka an samu dan kwanciyar hankali a yankunan.

Asali: Original
'Yan sanda sun tura jami'ai yankin
Shi ma da yake bayani, shugaban karamar hukumar Katsina-Ala, Justine Shaku, ya shaida wa manema labarai cewa, garuruwan da ke iyaka da Ukum na fuskantar barazana daga hare-haren.
Da aka tuntube ta, jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Benue, Catherine Anene, ta ce an tura jami’an tsaro yankin.
Kamar yadda Daily Post ta rahoto, Catherine Anene ta ce kuma ana ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro a wuraren da abin ya shafa.
Boko Haram sun kai hari a jihar Borno
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar Boko Haram ta kai hari a garin Yamtake da ke cikin karamar hukumar Gwoza, suka kashe sojoji biyu tare da fararen hula da dama.
Sanata Ali Ndume ya nuna damuwarsa kan lamarin, ya ce mutanen garin Yamtake ba da dadewa ba suka dawo daga zaman gudun hijira.
Ya yabawa dakarun Najeriya bisa kokarinsu na kare rayuka da dukiyoyi, tare da bukatar kafa rundunar tsaro ta al’umma don taimakawa yaki da Boko Haram.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng