Trump zai Gana da Abdul El Sayed da Ya Ci Zaben Sanata a Amurka

Trump zai Gana da Abdul El Sayed da Ya Ci Zaben Sanata a Amurka

  • Donald Trump, ya ce yana shirin ganawa da zaɓaɓɓen sanatan Michigan, Abdul El-Sayed, domin tattauna shirin samar da kiwon lafiya ga kowa
  • El-Sayed ya nemi a sauya sunan shirin “Medicare for All” zuwa “Trumpcare” domin jawo hankalin Trump ya goyi bayansa
  • Trump ya bayyana cewa El-Sayed mutum ne mai basira, kuma yana ganin akwai yiwuwar su cimma matsaya mai kyau kan batun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa yana shirin ganawa da zaɓaɓɓen sanatan jihar Michigan, Abdul El-Sayed, domin tattauna shirin samar da kiwon lafiya ga dukkan 'yan ƙasar.

Shirin na El-Sayed, wanda ya keɓe muhimmiyar rawa a kamfen ɗinsa, na neman tabbatar da cewa kowa zai samu damar kula da lafiyarsa ba tare da la’akari da matsayinsa na kuɗi ba.

Kara karanta wannan

Sanata ya ji kalaman da 'yan bindiga suka faɗa lokacin da suka bude wa tawagarsa wuta

Abdul El-Sayed da ya zama Sanata
Abdul El-Sayed a lokacin da ya ke kamfen. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar New York Post ta yi da shi a fadar White House ranar Talata, 24 ga Nuwamba, 2026.

Trump ya yaba wa El-Sayed

Trump ya bayyana cewa El-Sayed mutum ne mai basira, yana mai cewa ya yi ƙoƙari sosai wajen gabatar da shirin kiwon lafiyar.

Ya ce yana sa ran ganawa da shi, kuma wataƙila za su iya samun matsaya mai kyau wadda za ta gamsar da ɓangarorin biyu.

Shugaban ya kuma bayyana cewa sauya sunan shirin zuwa “Trumpcare” shawara ce mai kyau.

El-Sayed ya gabatar da wannan shawara ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a farkon watan Nuwamba, inda ya nuna hoton katin zinare mai ɗauke da sunan “Trumpcare”.

A saƙon, ya buƙaci Trump ya tabbatar da samar da kulawar lafiya ga kowa tun daga jarirai har zuwa ƙarshen rayuwarsu.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa ba zan goyi bayan Tinubu, Atiku ko Obi ba': Bulama Bukarti

Trump ya nemi haɗa kai

CNN ta wallafa cewa Trump ya ce shi da 'yan Democrat da suka samu rinjaye a majalisun dokokin ƙasar za su iya yin manyan abubuwa tare.

Sai dai ya yi gargaɗin cewa tattaunawar na iya farawa ne da saɓani, yana mai cewa zai iya ƙin amincewa da duk wasu dokoki da suka gabatar kafin su zauna su tattauna.

Ya ce a wani lokaci, 'yan Democrat za su nemi tattaunawa, kuma hakan zai iya ba su damar yin aiki tare kan harkokin kiwon lafiya da sauran muhimman batutuwa.

Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump yana yi wa 'yan Amurka bayani. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

A nasa ɓangaren, El-Sayed ya bayyana a wata hira cewa a shirye yake ya gana da Trump ko wani mutum, ba tare da la’akari da jam’iyyarsa ba, muddin hakan zai taimaka wajen cimma manufofin da ya yi wa alƙawari.

Karnuka sun kashe sojar Amurka

A wani labarin, kun ji cewa ana shirin birne Allison Lynn Anderson, wata tsohuwar soja a rundunar sojin ƙasar kuma uwa mai yara uku, bayan karnuka sun kashe ta.

Kara karanta wannan

Rashin Imani: Yan bindiga sun rutsa bayin Allah suna barci, sun bude masu wuta

Rahoton ofishin gundumar Bartow ya bayyana cewa an gano gawar Anderson mai shekaru 36 a ranar 16 ga Nuwamba, bayan karnuka sun far mata da cizo har ta mutu.

'Yar uwarta, Samantha Evans, ta ce iyalansu na cikin jimami kan abin da ya faru da tsohuwar sojar, tana mai cewa suna neman a yi musu adalci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng