"Mun San Ana Shan Wuya": Ganduje Ya Fadi Tasirin Gyaran Tattalin Arzikin Tinubu

"Mun San Ana Shan Wuya": Ganduje Ya Fadi Tasirin Gyaran Tattalin Arzikin Tinubu

  • An kaddamar da shugabannin jam'iyyar APC a Faransa, inda aka yi kira ga ‘yan Najeriya mazauna waje su goyi bayan Shugaba Bola Tinubu
  • Abdullahi Ganduje, ya jaddada cewa goyon bayan ‘yan Najeriya mazauna waje zai taimaka ga nasarar sauye-sauyen tattalin arziki da bunkasar APC
  • Shugabar APC reshen Faransa, Hajiya Amina Baba Suzuki ta nemi a goyi bayan bukatar ba ‘yan Najeriya mazauna waje damar kada kuri’a

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Faransa - APC ta kara samun ƙarfi a duniya yayin da Abdullahi Umar Ganduje, ya kaddamar da shugabannin sabon reshen jam’iyyar a Faransa.

Ganduje ya bukaci ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje da su mara wa Shugaba Bola Tinubu baya wajen aiwatar da tsare-tsaren gyaran ƙasa.

Abdullahi Ganduje ya nemi 'yan Najeriya mazauna waje sun marawa manufofin Tinubu baya
Abdullahi Ganduje, yayin da ya kaddamar da shugabannin APC reshen Faransa. Hoto: @Dawakiii
Asali: Twitter

Ganduje ya kaddamar da shugabannin APC a Faransa

Jaridar The Nation ta rahoto Ganduje yana cewa hadin kai da goyon bayan ‘yan jam’iyyar na kasashen waje na da matukar muhimmanci ga nasarar manufofin tattalin arzikin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da ya amince sauye-sauyen tattalin arziki sun jawo wahala a kasar, Ganduje ta bakin mai magana da yawunsa, Edwin Olofu, Ganduje ya ce dole ne a aiwatar da su don samar da ci gaba mai dorewa.

Ya yabawa ‘yan Najeriya da ke zaune a kasashen waje bisa rawar da suke takawa wajen yaɗa manufofin jam’iyyar APC da ƙara yawan mambobinta a ƙasashen duniya.

Ganduje ya tallata manufofin Tinubu a Faransa

Ganduje ya jaddada cewa gwamnatin Tinubu na kokarin tabbatar da cikakken haɗin kan ‘yan Najeriya mazauna waje, ciki har da damar kada kuri’a a zaɓe.

Ya bayyana farin cikinsa da yawan mahalarta taron daga sassan Turai, yana mai bayyana hakan a matsayin babban ci gaba ga jam'iyyar APC.

“Mun yaba da irin goyon bayan da ku ke bai wa Shugaba Tinubu, musamman wajen aiwatar da sauye-sauyen da ke faruwa yanzu,” inji Ganduje.

Ya bayyana wa mambobin APC na kasashen waje irin cigaban da aka samu a tarukan kwamitin gudanarwa na jam’iyya da kuma na NEC.

Ganduje ya fadi ci gaban da APC ta samu

Ganduje ya ce kwamitin NEC ya amince da sahalewa Shugaba Tinubu saboda manyan sauye-sauyen da ya kawo, musamman a fannin tattalin arziki.

Ya kara da cewa zaman lafiyar da ake ciki a APC ya jawo 'yan adawa na shiga jam'iyyar yanzu wanda hakan ke ci gaba da ƙara mata karfi gabanin zaɓen 2027.

“Ina tabbatar muku da cewa jam’iyyar APC na kan tsarin dimokuradiyya da bin kundin tsarin mulkinta, sabanin wasu jam’iyyun da ke cikin rikici,” inji Ganduje.
'Yan Najeriya mazauna waje na so a basu damar kada kuri'a a zabukan kasar nan
Shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje tare da shugabannin jam'iyyar reshen Faransa. Hoto: @Dawakiii
Asali: Twitter

Mazauna waje na son su rika kada kuri'a

Sabuwar shugabar APC reshen Faransa, Hajiya Amina Musa Baba Suzuki, ta jaddada rawar da ‘yan Najeriya mazauna waje ke takawa wajen cigaban ƙasa.

Hajjiya Amina ta roki shugabannin jam’iyyar da su marawa batunbai wa 'yan Najeriya mazauna waje damar kada kuri’a da aka dauko a gwamnatin Tinubu.

Taron ya samu halartar Haj. Hafsat Ganduje, Dr Mary Alile, Hon. Tunde Doherty da Oba Aderounmu Bamidele Sadiq, sarkin Yarbawan Faransa.

Ganduje ya yi martani ga kalaman Buba Galadima

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya mayar da martani game da kalaman Buba Galadima, wanda ya ce Ganduje ba shi da wani tasiri a siyasa.

Cif Oliver Okpala, babban mai taimaka wa Ganduje, ya bayyana cewa Galadima mutum ne da yawancin ‘yan siyasa suka raina, tare da rashin wani tasiri a kasar.

A cewarsa, kasancewar Ganduje ya yi gwamna a Kano har sau biyu, kuma yanzu yana shugabantar APC, hakan ya nuna karara cewa yana da babban matsayi da tasiri a siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.