Najeriya Ta Sake Girgiza: Gini Mai Hawa 3 Ya Ruguje, Ya Rufta kan Mutane

Najeriya Ta Sake Girgiza: Gini Mai Hawa 3 Ya Ruguje, Ya Rufta kan Mutane

  • Wani gini mai hawa uku ya rushe a yankin Ojodu-Berger, Legas, mutane da dama suka makale, wasu kuma aka ceto su da rai
  • Ginin da ya rushe na da gidan cin abinci Equal Rights a kasa, yayin da sauran hawaye uku ba su da mazauna a ciki
  • A zantawarmu da masani kan harkar gine-gine, Arch. Abdullahi Rabiu a Abuja, ya bayyana abubuwan da ke jawo gini rugujewa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Rahoton da muke samu yanzu na nuni da cewa wani gini mai hawa uku ya ruguje a jihar Legas tare da ruftawa kan mutane.

Yayin da ake fargabar cewa rushewar ginin ya yi ajalin mutane da dama, an ce lamarin ya faru ne a yau (Asabar) a yankin Ojodu-Berger da ke Legas.

Ana fargabar mutane sun mutu da gini ya rufta kan mutane a Legas
Wani gini mai hawa hudu da ya rushe a Abuja. An yi amfani da hoton don misali kawai. Hoto: @FctFema
Asali: Twitter

Gini mai hawa 4 ya rushe a jihar Legas

Gidan Talabijin na TVC ya rahoto cewa wani fitacccen gidan cin abinci na da matsugunni ne a wannan gini da ya rufta da misalin karfe 8:00 na safiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, wani rahoton ya nuna cewa ginin da ya rufta ba wai kammalalle ba ne, kuma mutane da dama sun makale a cikin baraguzansa.

An rahoto cewa gidan cin abinci na Equal Rights ne ya ke da matsugunni a wannan gini da ke titin Oremeta, Ojodu Legas.

Wani bidiyo da gidan talabijin ya fitar a safiyar yau ya nuna cewa jami'an kai daukin gaggawa na kokarin ceto wadanda suka makala a ginin.

An samu karin bayani kan rushewar ginin Legas

An ceto mutane tara daga cikin ginin da ya rushe a safiyar yau, a yankin Ojodu-Berger na jihar Lagos, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Rahotanni sun nuna cewa masu amfani da ginin ba su da yawa, kuma babu kowa a hawa na uku, sai dai gidan abincin Equal Right da ke a kasa.

Da karfe 2:00 na rana, jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Legas da kuma hukumar bada agajin gaggawa ta LASEMA na ci gaba da kokarin ceto wadanda suka makale.

Mutanen da aka ceto sun samu kulawar gaggawa daga LASAMBUS, kuma an garzaya da su asibiti domin samun karin kulawa daga likitoci.

Har zuwa lokacin da aka fitar da rahoton, ba a bayyana musabbabin rushewar ginin ba.

Gini mai hawa 3 ya ruguje kan mutane a Legas, yanzu an ceto mutane 9.
Ma'aikata na ci gaba da aikin ceto wadanda gini mai hawa 3 ya rufta kansu a Legas. Hoto: @followlasema
Asali: Twitter

Hukumar kashe gobara ta yi karin bayani

Daraktar hukumar kashe gobara ta Lagos, Margaret Adeseye, ta tabbatar da adadin wadanda aka ceto, tana mai cewa ana zargin akwai sauran mutane da har yanzu ba a gansu ba.

A cewar hukumar:

“Gini mai hawa uku ne ya rushe a safiyar yau. Mun ceto mutum tara, kuma har yanzu ba a samu asarar rai ba.
"Mutanen da aka ceto sun samu raunuka daban-daban. LASAMBUS ne suka fara ba su kulawa kafin a dauke su zuwa asibiti.

“Ginin mai hawa uku ne, amma kasa ne kawai ake amfani da shi a matsayin mashaya da wurin cin abinci da ajiye motoci.”

Me ke jawo yawan ruftawar gine-gine?

A zantawarmu da masani kan harkar gine-gine, Arch. Abdullahi Rabiu a Abuja, ya ce ana samun yawaitar rushewar gine-gine saboda wasu dalilai da dama.

Arch. Abdullahi ya ce:

"Ana iya samun kuskuren farko daga wanda ya zana gidan, domin kura-kurai a wajen kayyade adadin nauyin da gini zai iya dauka na jawo ruftawarsa."

Mai zane-zanen gidan ya ce idan ba a samu matsala daga zane ba, to ana iya samun matsala daga wadanda za su yi ginin, walau kin bin tsarin zanen, ko amfani da kayan aiki marasa kyau.

Ya yi nuni da cewa:

"Kin kiyaye tsarin amfani da siminti, ruwa, yashi, duwatsu ko kuma kin yin amfani da kayan aiki masu kyau na sa gini ya rufta tun kafin ma a kammala shi."

Masanin gine-ginen ya ce mutane na amfani da wadanda basu kware ba a wajen gini saboda gudun biyan kudi masu yawa, wanda hakan ke jawo rushewar gini da asarar rayuka.

Kalli bidiyon a kasa:

Gini ya rufta kan mutane 2 a Abuja

A wani labarin, mun ruwaito cewa, an shiga firgici a unguwar Prince and Princess da ke Abuja bayan wani gini da ake ginawa ya ruguje tare da ruftawa kan mutane.

Rahotanni sun nuna cewa ma’aikatan da ke aikin sun yi saurin barin harabar ginin bayan sun lura da alamun zai rugujewa kafin lamarin faruwa.

Hukumar agajin gaggawa ta birnin tarayya (FEMD) ta tabbatar da cewa an ceto mutane biyu da ginin ya rufta kansu cikin nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.