'Ka Raina Doka': Matasan Arewa Sun Caccaki Tinubu kan Ƙin Miƙa Mulki ga Shettima
- Wata kungiyar matasan Arewacin Najeriya ta soki Shugaba Bola Tinubu bisa kin mika mulki ga Kashim Shettima yayin tafiyarsa waje kwanan nan
- Matasan sun bayyana cewa hakan ya saba da kundin tsarin mulkin Najeriya, kuma yana kara jefa Arewa cikin rashin jin dadin gwamnatin Tinubu
- Sun bukaci shugaban ya mutunta tsarin dimokuradiyya, tare da mika mulki ga Shettima a kowane lokaci da zai bar kasar don kare tsarin mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Kungiyar matasan Arewacin Najeriya ta caccaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa kin mika mulki ga mataimakinsa, Kashim Shettima, yayin tafiyarsa ksashen waje.
Shugaban kungiyar, Isah Abubakar, ya ce, “wannan abu ba wai ya saba wa tsarin dimokuradiyya kawai ba, har ma da karya kundin tsarin mulkin 1999.”

Asali: Twitter
Matasan Arewa sun yi wa Tinubu ta-tas kan Shettima
Isah Abubakar ya bayyana cewa tsarin mulki ya fayyace yadda za a mika mulki idan shugaban kasa ba ya nan ko kuma ba ya iya sauke nauyin ofishinsa, inji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Kin bin wannan tanadi na kundin tsarin mulki na nuna sabawa tushen dimokuradiyya da kuma kafa sabuwar al’ada mai hatsari ga shugabanci,”
- inji Isah.
Kungiyar matasan ta ce wannan lamari na kara rura wutar rashin jin dadin da Arewacin Najeriya ke ciki a gwamnatin Tinubu.
Sanarwar kungiyar ta ci gaba da cewa:
“Wannan hali na nuna halin ko-in-kula da mutanen Arewa, yana jefa shakku kan adalcin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.”
Matasa sun tuno da mulkin Jothan, Yar'Adua
Ta kawo misalin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan wanda ya taba mika mulki ga mataimakinsa, Namadi Sambo, lokacin tafiyarsa jinya a ketare.
“Jonathan ya bi doka, ya kuma nuna kima ga tsarin dimokuradiyya da bukatar dorewar shugabanci mai tsafta,” inji sanarwar.
Suka kuma ce marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua, a lokacin rashin lafiyarsa, ya mika mulki ga Goodluck Jonathan a 2010.
Sanarwar ta kara da cewa:
“Wannan mataki na Yar’Adua ya kara karfafa zaman lafiya da martabar shugabanci a lokacin da kasar ke cikin rudani."
Sai dai Legit za ta iya tuna cewa a lokacin jinyar karshe da Marigayi Yar’Adua ya yi, majalisa ce ta ba Jonathan damar rikon kwarya.

Asali: Facebook
Matasan Arewa sun ba Tinubu shawarar mika mulki
Matasan Arewacin kasar sun ce abin takaici ne yadda Shugaba Tinubu ke kokarin tarawa kansa iko, yana take girman ofishin mataimakin shugaban kasa.
“Wannan hali yana barazana ga tsarin hadin kai na kasa da kuma matakin dimokuradiyya da ke hade mu duka a matsayin kasa daya,” inji kungiyar.
Kungiyar ta ce lokaci ya yi da “dukkan ‘yan Najeriya za su nemi a tabbatar da bin doka da adalci daga shugabannin da suka zaba.”
Ta bukaci Tinubu da ya sauke nauyin mulki cikin gaskiya ta hanyar mika iko ga Shettima duk lokacin da zai fita daga Najeriya.
2027: APC ta nemi Tinubu ya tafi da Shettima
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jam’iyyar APC reshen jihar Borno ta bayyana goyon bayanta ga yiwuwar Shugaba Bola Ahmed Tinubu sake tsayawa takara a zaben 2027.
Shugabannin jam’iyyar sun jinjinawa Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, tare da bukatar a sake daukarsa a matsayin abokin takara.
Sun kuma bukaci Tinubu da ya ci gaba da maida hankali bangaren hakar mai da kuma gyaran hanyoyi a shiyyar Arewa maso Gabas.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng