Gwamna Ya Fallasa Yadda APC ke Dauko Hayar Matasa Su Halarci Yakin Neman Zaben Tinubu

Gwamna Ya Fallasa Yadda APC ke Dauko Hayar Matasa Su Halarci Yakin Neman Zaben Tinubu

  • Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya zargi APC da dauko hayan magoya baya daga jihohin makwabta domin halartar gangamin kamfe a Ibadan
  • Makinde ya ce ya bayar da umarnin fesa maganin kashe ƙwayoyin cuta a Mapo Hall da filin jirgin saman Ibadan saboda fargabar yaɗuwar cutar Ebola
  • APC ta yi watsi da zargin gwamnan, tana mai cewa dubban magoya bayanta daga ƙananan hukumomi 33 na jihar ne suka halarci taron

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Oyo, Nigeria - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya zargi jam’iyyar APC da kawo magoya bayanta daga jihohin makwabta domin halartar gangamin kamfen ɗin shugaban ƙasa a Ibadan.

Ya kuma bayar da umarnin fesa maganin kashe ƙwayoyin cuta a Mapo Hall da filin jirgin saman Ibadan saboda fargabar yiwuwar yaɗuwar cutar Ebola.

Kara karanta wannan

Bayan rashin 'yan APC 15, tsohon sakataren gwamnatin Zamfara ya rasu

Gwamna Makinde.
Gwamnan jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, wanda ke neman zama shugaban kasa a inuwar jam'iyyar APM Hoto: Seyi Makinde
Source: Facebook

Makinde ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin wata hira da aka yi da shi a wani shirin rediyo da aka wallafa a Facebook, kwana biyu bayan Shugaba Bola Tinubu da sauran shugabannin APC sun halarci kamfen a Mapo Hall.

Gwamna Makinde ya zargi APC

Gwamnan ya yi zargin cewa APC ta ɗauko hayar magoya baya daga jihohin makwabta domin nuna cewa tana da gagarumin goyon baya a Jihar Oyo, alhali mafi yawan mazauna jihar ba su halarci taron ba.

Ya ce:

“A ranar Asabar, sun shigo da mutane da yawa zuwa Jihar Oyo, suna ikirarin cewa suna da goyon bayan jama’a a jihar. Amma mutanen Oyo sun kwantar da hankalinsu sosai.”

Ya kuma ce ya bayar da umarni ga jami’an gwamnati da abin ya shafa da su fesa maganin kashe ƙwayoyin cuta a filin jirgin saman da Mapo Hall, yana mai danganta matakin da fargabar cutar Ebola.

Kara karanta wannan

Sanata ya ji kalaman da 'yan bindiga suka faɗa lokacin da suka bude wa tawagarsa wuta

APC ta ƙaryata zargin Makinde

A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na jihar, Olawale Sadare, ya fitar ranar Litinin, APC ta yi watsi da bayanin gwamnan kan taron, tana mai cewa dubban magoya bayanta daga sassa daban-daban na Jihar Oyo ne suka halarta.

Jam’iyyar ta ce an samu magoya baya daga dukkan ƙananan hukumomi 33 na jihar, tare da shugabannin APC daga sauran jihohin Kudu maso Yamma da jami’an shugabancin jam’iyyar na ƙasa.

Ta yi iƙirarin cewa yawan mutanen da suka halarci taron ya tayar da hankalin Makinde da abokan siyasarsa gabanin zaɓen 2027.

Jam’iyyar ta kuma zargi gwamnan da amfani da fargabar cutar Ebola a matsayin damar bayar da kwangilolin da ta kira marasa inganci da karkatar da kuɗaɗen gwamnati.

Abin da bincike ya gano

Wani ɗan APC daga Jihar Kwara ya shaida wa Premium Gimes cewa an tattara mambobin jam’iyyar daga wannan jiha da ke yankin Arewa ta Tsakiya, ciki har da shi, domin su halarci gangamin da aka gudanar a Ibadan.

Kara karanta wannan

Mutane sun yi rugu rugu da tawagar APC ta yi hadari, an rasa rayuka da yawa

Ya ce wani shugaban jam’iyya ne ya umurce shi da ya bi sauran magoya bayan da za su je taron.

“Mun je wurin, na tafi tare da shugaban jam’iyyarmu, akwai wasu mutanen da suka haɗu da mu, har ma da motocin bas da yawa da suka tashi a wannan rana," in ji shi.
Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana jawabi a wurin kaddamar da wasu syyuka a Abuja Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Ya ƙara da cewa shiga cikin gangamin ya biyo bayan damuwar da shugabannin jam’iyyar APC suka nuna kan biyayyarss ga APC, yana mai cewa, "suna zargin ina da alaka da PDP."

Makinde ba zai yi aiki da Tinubu ba

Kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na APM, Seyi Makinde, ya ce ba zai jawo Shugaba Bola Tinubu cikin gwamnatinsa ta haɗin kan ƙasa ba idan ya lashe zaben 2027.

Makinde, gwamnan Jihar Oyo, ya zargi Tinubu da gaza cika yarjejeniyarNda suka cimma gabanin babban zaɓen 2023, wadda ta shafi kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262