APC Ta Maida Martani Matasan Arewa da Suka Ce ba Za Su Zabi Tinubu a 2027 ba
- APC ta Kano ta caccaki yan kungiyar matasa ta APC Northern Youth Forum da suka fito suka janye goyon baya ga Tinubu, ta ce bakin haure ne
- Jam’iyyar ta kare gwamnatin Tinubu, tana mai cewa an samu ci gaba a tsaro da tattalin arziki duk da ƙalubalen da ake fuskanta
- Kakakin APC a Kano, Auwalu Soja, ya ce binciken da suka yi kan kungiyar ya gano cewa mutasan ba ’yan Najeriya ba ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta yi zargin cewa mambobin ƙungiyar APC Northern Youth Forum, waɗanda kwanan nan suka nuna adawa da burin Shugaba Bola Tinubu na zarcewa a wa’adi na biyu, ’yan ƙasashen waje ne.
Jam’iyyar ta kuma kare ayyukan gwamnatin Shugaba Tinubu, tana mai cewa an samu ci gaba a fannin tsaro da tattalin arziki duk da ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.

Source: Facebook
Kakakin APC a Kano, Auwalu Soja, ne ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da jaridar Leadership, yayin da yake mayar da martani kan sanarwar ƙungiyar cewa ta janye goyon bayanta ga Tinubu a 2027.
Sakataren ƙungiyar, Umar Chanji, ya sanar da janye goyon bayansu ga shugaban ƙasar, yana mai danganta matakin da tabarbarewar tsaro, matsin tattalin arziki, zargin yin watsi da ilimi da kiwon lafiya, da rashin cika alƙawuran yaƙin neman zaɓe.
APC ta maida martani ga matasa
Sai dai Soja ya yi watsi da zarge-zargen ƙungiyar matasan, yana mai cewa wani kwamiti da shugaban APC na Kano, Haruna Doguwa, ya kafa ya gudanar da bincike kan wannan kungiya.
Ya kara da cewa kwamitin ya gano cewa mambobin kungiyar ba ’yan Najeriya ba ne, kuma ba su da rajistar zama mambobin jam’iyyar APC kwata kwata.
Ya ce:
“Bayan sun gudanar da taron manema labarai, APC ta kafa kwamiti, kuma bayan mun gudanar da bincike, mun gano cewa ba ’yan ƙasa ba ne. A gaskiya, ba ma ’yan Najeriya ba ne, balle a ce ’yan Kano ne ko mambobin APC.”
Ya kuma yi zargin cewa kwamitin bai gano wata shaida da ke nuna cewa mutanen sun shigo Najeriya ta hanyar da doka ta tanada ba.
APC ta kare gwamnatin Tinubu
Dangane da matsalar tsaro, kakakin APC ya amince cewa har yanzu Najeriya ba ta kai ga samun cikakken tsaro ba, amma ya dage cewa an samu sauƙi idan aka kwatanta da halin da Tinubu ya gada a 2023.
A matsayin misali, ya ambaci dawowar zirga-zirgar ababen hawa a kan hanyar Kano zuwa Abuja, yana mai cewa yanzu matafiya na iya yin wannan tafiya cikin sauƙi fiye da da.

Source: Getty Images
Soja ya kuma kare manufofin tattalin arzikin gwamnatin, yana mai cewa farashin buhun shinkafa ya sauka daga sama da N120,000 kafin Tinubu ya hau mulki zuwa tsakanin N50,000 da N60,000.
Ya dage cewa Tinubu da APC na da gagarumin goyon bayan siyasa a Kano, inda ya ƙara da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da kasancewa cikin ƙarfin jam’iyyar a jihar.
APC ta karyata zargin tura wasika INEC
Kun ji cewa jam’iyyar APC ta musanta sahihancin wata wasiƙa da ake zargin shugabanta na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya rubuta wa hukumar INEC .
Wasiƙar ta yi zargin cewa shugaban APC ya buƙaci INEC ta tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
Asali: Legit.ng

