Sarakunan Arewa da aka taba tsigewa, kora ko sallama kafin dakatar da Sarkin Daura a 2026

Sarakunan Arewa da aka taba tsigewa, kora ko sallama kafin dakatar da Sarkin Daura a 2026

Katsina - Daga shekarar 1960 zuwa 2026, an samu manyan sarakuna a Arewacin Najeriya da gwamnatoci dabam-dabam suka cire wa rawani.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Wasu sarakunan sun gamu da dakatarwa yayin da kuma aka cire wa wasunsu rawani, an kuma yi sarkin da aka tilasta masa sai da ya yi murabus.

Legit Hausa ta yi nitso cikin tarihi, ta kawo jerin sarakunan da aka raba da gadon sarauta da kuma dalilan da suka jawo matakin da hukuma ta dauka.

Sarakunan da suka rasa rawaninsu a tarihi

1. Muhammadu Sanusi I

A shekarar 1963 Gwamnatin Arewacin Najeriya ta tilasta wa Muhammadu Sanusi I yin murabus, a dalilin haka aka nada Sarki Muhammad Inuwa.

Gwamnatin Ahmadu Bello ta kafa hujja ne da matsalar taba kudin al’umma. A karshe ya tare a garin Azare kafin ya koma zama a garin Wudil.

Kara karanta wannan

Obi na zargin ana shirin alakanta shi da 'yan ta'adda don bata shi a Arewa

2. Umaru Abba Tukur

Yohanna Madaki ya tsige Sarkin Muri, Umaru Abba Tukur lokacin yana gwamnati a mulkin soja, hakan ya faru ne a watan Agustan shekarar 1986.

Sojan ya zarge shi da taba kudin da aka ware wa wasu kauyawa da za a canza matsuguni. A dalilin hakan mai martaba ya shigar da kara aka yi ta shari’a.

2. Ibrahim Dasuki

Janar Sani Abacha ya sauke Ibrabim Dasuki daga sarautar sarkin Musulmi. Gwamnatin Yakubu Mu’azu ta sanar da wannan mataki a Sokoto.

A sakamakon haka aka nada Muhammadu Maccido a matsayin Sultan a 1996, daga nan shi kuma Dasuki ya tare can nesa a cikin jihar Taraba.

3. Mustapha Haruna Jokolo

Mai martaba Mustapha Haruna Jokolo ya rasa rawaninsa a shekarar 2005 lokacin Muhammad Adamu Aliero yana gwamnan farar hula a Kebbi.

An zargi Sarkin Gwandu da yin kalamai da za su zama barazana ga hukuma kuma, ya kalubalanci cire shi da nada Muhammadu Iliyasu Bashar a kotu.

Kara karanta wannan

Barau Jibrin ya hada kan malaman Musulunci 2,000 saboda Tinubu, Abba Kabir

4. Muhammadu Sanusi II

Lokacin da Abdullahi Umar Ganduje yake mulki a Kano ne aka tunbuke Muhammadu Sanusi II saboda laifin saba wa hukuma da kuma rashin biyayya.

Da farko an yi waje da shi daga gidan gwamnati kuma aka ajiye shi a wani kauye a jihar Nasarawa. Bayan shekaru hudu kuma ya sake koma wa gadon mulki.

Sarakunan Kano da aka sake tsigewa

A watan Mayun 2024 Majalisar dokokin Kano ta rusa dokar masarauta ta shekarar 2019 wanda ta kirkiro sababbin sarakuna biyar a zamanin Ganduje.

Rusa dokar ya jawo aka yi waje da sarakunan da gwamnatin jihar ta nada a wancan lokaci. Sarakunan su ne:

5. Aminu Ado Bayero – Kano.

6. Nasiru Ado Bayero – Bichi.

7. Aliyu Abdulkadir – Gaya.

8. Abubakar Ibrahim – Karaye.

9. Kabiru Mohammed Inuwa – Rano.

Kara karanta wannan

'Tinubu ya goyi baya na kare kasar Yarabawa daga 'yan ta'adda,' Sunday Igboho

Daga baya gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi dokar da ta sake kirkiro sarakuna a Gaya, Karaye da Rano amma ba a ba a sake ba Bichi masarauta ba.

Nasiru Ado Bayero bai koma kujerar shi ba yayin da ake ta takaddama da Aminu Ado da aka canza.

10. Umar Faruk Umar

Ranar 24 ga watan Nuwamba 2026 aka ji Gwamnatin Katsina ta dakatar da Umar Faruk Umar daga duk wasu ayyuka da kuma tafiye-tafiye a matsayin sarki.

An yi hakan ne domin a binciki zargin da wata baturiya ta yi masa na neman yin lalata da ita lokacin da ta ziyarci fadar Sarkin Daura da ta zo yawon bude ido.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng