'Yan Bindiga Sun Mamaye Jihar Benue, Gwamna Ya Fadi Halin da Mutanensa Suke ciki

'Yan Bindiga Sun Mamaye Jihar Benue, Gwamna Ya Fadi Halin da Mutanensa Suke ciki

  • Gwamna Hyacinth Alia ya bayyana damuwa kan matsalolin tsaro da ke kara tsananta a jihar Benue, musamman da damina ta karato
  • Ya ce wasu miyagu na ƙoƙarin korar jama'a daga garuruwansu domin su mamaye su, inda ya roƙi gwamnatin tarayya ta kai masu dauki
  • Gwamnan Benue ya gargadi 'yan siyasa da ke amfani da rikicin, ya kuma ce duk wanda ya yi laifi dan ta’adda ne kuma za a tona asirinsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benue - Gwamnan Benue, Hyacinth Alia, ya bayyana damuwa kan ƙaruwa da tsanantar matsalolin tsaro a jihar, musamman da ake tunkarar daminar bana.

Ya koka cewa jihar na cikin tsaka mai wuya sakamakon wasu miyagu da ke ƙoƙarin korar jama’a daga garuruwansu, da nufin mamaye gidajensu.

Gwamnan Benue ya fadi yadda 'yan ta'adda ke kokarin mamaye jihar Benue
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia. Hoto: @HyacinthAlia
Asali: Facebook

Gwamnan Benue ya koka da harin 'yan bindiga

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga masu ibada a Chapel of Grace da ke gidan gwamnati a Makurdi, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi kira ga 'yan jihar da su kasance masu sa ido tare da dakile masu neman tada zaune tsaye ta hanyar kai rahoton duk wani motsin da ba su yarda da shi ba ga jami’an tsaro.

A baya-bayan nan ne gwamnan ya kai ziyara a ƙananan hukumomin Ukum da Logo na jihar, inda 'yan bindiga suka farmaki mutanen yankin a daren Alhamis da safiyar Juma'a.

Hare-haren sun yi sanadin mutuwar fiye da manoma 50, yayin da wasu da dama suka jikkata, har lamarin ya sa gwamnan ya roki dauki daga gwamnatin tarayya.

"Miyagu na kokarin mamaye garuruwa" - Gwamnan Benue

Mataimaki na musamman ga gwamna kan harkokin watsa labarai, Isaac Uzaan, ya ruwaito cewa Alia ya nuna matuƙar damuwa kan ci gaba da hare-haren da ake kai wa manoma a Benue.

Cikin fushi Gwamna Alia ya ce:

“Jiharmu na fama da hare-hare. Mutanenmu na fuskantar barazana koyaushe, kuma waɗanda ke kai mana hari ba aljanu ba ne; mutane ne, kuma suna da manufa.
“Suna fito da mutane waje, suna kashe su domin su mamaye ƙasarsu. Ba za mu lamunci wannan lamari ba."

Ya gargadi 'yan siyasa da ke amfani da ke fakewa da rikicin don cimma wata manufarsu, yana mai cewa, “muna da hanyoyin gano waɗanda ke da hannu cikin lalata jiharmu.”

Gwamna Alia ya gargadi 'yan siyasa da ke rura wutar ta'addanci a Benue
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia. Hoto: @HyacinthAlia
Asali: Twitter

Gwamna Alia ya gargadi 'yan siyasar Benue

Gwamnan ya kara da cewa:

“Ina la’antar duk wani nau’in laifi a cikin jihar nan, dan ta’adda dai dan ta’adda ne, ko daga wace kabila ko addini ya fito.
"Laifi dai laifi ne. Duk wanda ya aikata shi, to ta’addanci ya aikata kuma bai cancanci ya zauna tare da mu ba."

Sai dai Gwamna Alia ya ƙarfafa wa al’ummar jihar Benue gwiwa da su ci gaba da zama masu juriya, tare da ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta dawo da zaman lafiya a fadin jihar.

Matasa sun tare motar gwamnan Benue

A wani labarin, mun ruwaito cewa, matasa sun tare tawagar Gwamna Hyacinth Alia a garin Afia, da ke Ukum, yayin ziyarar da ya kai don tallafa wa wadanda harin ‘yan bindiga ya shafa.

Ana dai zargin 'yan siyasa ne suka shirya wannan bore, inda suka toshe hanya suna kwala ihu da cewa, “ba za mu yarda ba,” domin hana gwamnan shiga dakin taro.

Sai dai an samu ɗan ƙaramin rikici yayin da gilashin motar Kwamishinan 'yan sanda ya fashe, amma rundunar ta tabbatar da dawo da zaman lafiya ba tare da an rasa rai ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.