Amurka Ta Kara Sunayen 'Yan Najeriya 24 cikin Wasu 157 da Za a Fatattako daga Kasar
- Amurka ta kara ’yan Najeriya 24 a cikin jerin mutanen da take shirin fatattaka, adadin wadanda ake zargi ya kai 157 a yanzu
- Ana zargin mutanen da laifuffuka da suka hada da damfara, safarar kwayoyi, satar bayanan sirri da halatta kudin haram
- Sai dai DHS ba ta bayyana lokacin korarsu ba, kuma sanya sunayensu a jerin bai nufin cewa kotu ta same su da aikata laifi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
America - Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka (DHS) ta kara sunayen ’yan Najeriya 24 cikin jerin mutanen da take shirin kora daga kasar wajen.
Abin da hakan yake nufi shi ne adadin wadanda ake nema a fatattaka daga kasar a karkashin gwamnatin Donald Trump ya kai mutane 157.

Source: Getty Images
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, bisa bayanan da ta tattaro daga shafin yanar gizon DHS a ranar Litinin, an sake yin ram da wasu da za a koro su.
An cafke sababbin mutanen ne bisa zargin aikata laifuffuka da suka hada da damfara, halatta kudin haram da safarar miyagun kwayoyi a Amurka.
Sauran laifuffukan da ake tuhumarsu da aikatawa su ne satar bayanan sirri da cin zarafin yara.
'Yan Najeriya sun shiga bakin jeri a Amurka
An sanya sunayen ’yan Najeriyan a shafin ma'aikatar da taken “Worst of the Worst”, wanda ke nuna sunayen baki da aka samu da mafi munin laifi.
Hukumar kula da shige da fice ta Amurka (ICE) ta kama su bisa zargin aikata manyan laifuffuka, kuma ake fuskantar matakin korarsu daga kasar.
Jerin ya kunshi zunubai daban-daban kamar damfarar mutane ta hanyar wasiku da intanet, yin amfani da sunan wani da kirkirar takardun bogi.
Ana zarginsu da kai hari da kuma laifuffukan da suka shafi mallakar makamai a kasar Amurkan.
Mutanen Najeriya da za a koro daga Amurka
Daga cikin wadanda aka ambata akwai Emmanuel Omowaiye, wanda aka kama a Richmond, Texas, bisa zargin damfarar mutane da wasiku.
Akwai Laurene Onwuka, wadda aka kama a Chantilly, Virginia, bisa zargin amfani da sunan wani wajen damfara; da Olusegun Shonekan a Newark.
Sauran sun hada da Olusegun Olaseni, wanda aka kama a Greencastle, Indiana, bisa zargin sayar da muguwar kwaya mai suna amphetamine.
Sai Peter Ude, wanda aka kama a Atlanta, Georgia, bisa zargin damfara ta intanet; da Newton Jemide, wanda aka kama a Fort Dix, New Jersey.
Sai Shedrack Umukoro, wanda aka cafke shi a Yazoo City, Mississippi, bisa zargin halatta kudin haram.
An cafke Olasoji Akinbode a Kearny, New Jersey da zargin sai Oluwatosin Afolabi, wanda aka kama a Conroe, Texas, shi ma bisa zargin damfara.
Jaridar Daily Post ta ce ma'aikatar ta sanya sunayen Alameen Adetunji Tokosi, wanda aka kama a Chicago, Illinois, bisa zargin mallakar hodar Iblis.
Akwai Joshua Ipoade, wanda aka kama a Atlanta, Georgia, bisa zargin damfara ta intanet.
Wani dan Najeriya mai suna Michael Orji da aka kama a Oxford na cikin jerin wadanda ake zargi da laifuffukan mallakar makamai, damfara da sauransu.
Sauran sun hada da Ahmadu Apooyin, Teslim Kiriji, Onomen Uduebоr, Charles Ochi da Daniel Eta.
An kuma sa sunan Ifeanyi Ibennah, Kazeem Runsewe, Fatiu Lawal, Justin Akubueze, Moyinoluwaseun Okeowo da Babajide Oluwaseun Faseyi.
Sunayen sababbin mutanen da aka fitar
1. Michael Orji
2. Bright Eigbedion
3. Justin Akubueze
4. Peter Ude
5. Shedrack Umukoro
6. Moyinoluwaseun Okeowo
7. Emmanuel Omowaiye
8. Laurene Onwuka
9. Olasoji Akinbode
10. Newton Jemide
11. Oluwatosin Afolabi
12. Alameen Adetunji Tokosi
13. Ahmadu Apooyin
14. Olusegun Olaseni
15. Ifeanyi Ibennah
16. Babajide Oluwaseun Faseyi
17. Fatiu Lawal
18. Teslim Kiriji
19. Onomen Uduebor
20. Charles Ochi
21. Daniel Eta
22. Kazeem Runsewe
23. Joshua Ipoade
24. Oluwaseun Faseyi
Asali: Legit.ng


