Matasa Sun Fusata, Sun Tare Tawagar Gwamna a kan Titi, An Rotsa Motar Kwamishina

Matasa Sun Fusata, Sun Tare Tawagar Gwamna a kan Titi, An Rotsa Motar Kwamishina

  • Tawagar Gwamna Hyacinth Alia ta gamu da bore daga matasa, mata da yara a Afia, Ukum, yayin ziyarar tallafi ga wadanda suka fuskanci hari
  • Wasu da ake zargin 'yan siyasa ne suka dauki nauyin bore. Sun tare hanya suna ihun “ba za mu yarda ba” domin hana Gwamnan shiga dakin taro
  • An samu tasgaro kadan, inda aka rotsa gilashin motar CP. Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da dawo da zaman lafiya, ba a rasa rai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benue - Tawagar gwamnan jihar Benue Hyacinth Alia ta gamu da bore daga wasu matasa, mata da yara a garin Afia da ke karamar hukumar Ukum.

An rahoto cewa, garin na Afia ya shiga cikin firgici a lokacin da matasan suka tare tawagar motocin gwamnan yayin da ya kai ziyara garin da makiyaya suka farmaka.

Matasa sun tare ayarin gwamnan jihar Benu, Hyacinth Alia, an rotsa motar 'yan sanda
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia yana jawabi a wajen wani taro. Hoto: @HyacinthAlia
Asali: Facebook

Matasa sun tare tawagar gwamnan Benue

Mai sharhi kan lamuran tsaro a shiyyar Arewa maso Gabas da kuma yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya fitar da rahoton a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar tsaro ta shaida wa Makama cewa matasa, mata da kananan yara sun tare tawagar gwamnan Benue da misalin karfe 3:30 na ranar Asabar, 19 ga Afrilu.

An ce tawagar gwamnan ta kunshi kwamishinan 'yan sandan Benue, CP Steve Hassan Yabanet, da wasu manyan hafsoshin tsaro.

Haka kuma, an rahoto cewa gwamnan ya ziyarci wannan yanki da suka fuskanci harin makiyaya domin ganin barnar da aka yi da tallafin da za a ba su.

An lalata motar kwamishinan 'yan sanda

Wata mjiyar 'yan sanda ta shaida cewa masu zanga-zangar da ake zargin 'yan siyasa ne suka dauki nauyin su, sun tare hanyar da gwamnan zai bi zuwa dakin taro.

Majiyar ta ce matasa, mata da yara sun tare hanyar suna cewa "ba za mu yarda ba" a wani kokari na hana tawagar gwamnan zuwa dakin taron.

Sai dai an ce jami'an tsaro sun yi amfani da dan karamin karfi wajen dakile mutane daga zama barazana ga tawagar ta hanyar tarwatsa su don samun hanyar wuce wa.

An rahoto cewa ba a samu rauni ko asarar rayuka ba, har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, amma an ce an rotsa gilashin motar kwamishinan 'yan sandan jihar.

'Yan sanda sun fara bincike kan tare tawagar gwamnan Benue
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia. Hoto: @HyacinthAlia
Asali: Facebook

'Yan sanda sun fara bincike kan lamarin

Tun da fari, wannan tawaga dai ta ziyarci wasu da harin makiyayan ya shafa a karamar hukumar Logo kafin zarce wa zuwa karamar hukumar Ukum.

Rundunar 'yan sanda ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike domin gano wadanda suka dauki nauyin tare ayarin gwamnan a Ukum.

Hakazalika, rundunar ta shaida cewa an dawo da zaman lafiya, doka da oda a wannan yanki na Ukum, yayin da gwamnan ya kammala abin da ya kai shi ya koma birnin jihar.

Makiyaya sun kashe masu ibada 10 a Benue

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu Fulani makiyaya dauke da mugayen makamai sun farmaki jihar Benue, inda suka kashe mutane 10 da ke kan hanyar zuwa coci.

Wani mazaunin Ukum ya bayyana cewa an kai harin da misalin karfe 6:00 na safe, inda aka harbe mata da yara, tare da jikkata mutane 25.

Kwamishinan yada labarai na jihar Benue ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa an samu yawaitar makiyaya dauke da makamai a jihar, a 'yan kwanakin nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.