Daga Karshe, An Bayyana Lokacin da Tinubu Zai Dawo Gida Najeriya daga Turai
- Gwamnatin tarayya ta mayar da martani kan sukar da ake yi game da rashin dawowar Shugaba Bola Ahmed Tinubu gida Najeriya
- Legit.ng Hausa ta tuna cewa a ranar 2 ga Afrilu, 2025, Tinubu ya bar Najeriya zuwa Faransa domin wata “ziyara ta aiki” ta mako biyu
- Yayin da fadar shugaban kasa ke fadin lokacin da Tinubu zai dawo gida, Bayo Onanuga, ya ce Tinubu na tafiyar da mulki daga kasar waje
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu yana ci gaba da gudanar da mulkin Najeriya duk da cewa yana kasar Turai.
Wannan na cikin wata sanarwa da daya daga cikin masu magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis, 17 ga Afrilu.

Asali: Twitter
An ji lokacin da Tinubu zai dawo Najeriya
Bayo Onanuga, ya yi karin bayani kan lokacin da Shugaba Tinubu zai dawo gida Najeriya a cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce rashin dawowar Tinubu gida Najeriya “na dan lokaci ne kuma ya yi daidai da lokacin da aka ce zai yi yana hutu."
A cewar Bayo Onanuga, dama tun a makonni biyu da suka gabata, an ce shugaban kasar zai dawo Najeriya ne bayan bukukuwan Easter na 2025.
Tinubu na tafiyar da mulki daga kasar waje
Onanuga ya ce:
“Shugaban kasa ya bar Paris zuwa birnin London a karshen mako, kuma yana ci gaba da mu’amala da manyan jami’an gwamnatin Najeriya.
"Tinubu yana ci gaba da tafiyar da muhimman al’amuran kasa, ciki har da bayar da umarni ga shugabannin tsaro kan barazanar da ke kunno kai a wasu yankunan kasar.
“Dawowarsa Abuja da komawarsa bakin aiki a fadar Aso Villa zai biyo bayan kammala hutun bukukuwan Easter.”
An tabbatar da jajurcewar Tinubu
Bugu da kari, hadimin shugaban kasan ya ce:
“Shugaba Tinubu na da cikakken kwarin gwiwa da jajircewa wajen gudanar da ayyukansa, kuma gwamnati tana tafiya yadda ya kamata karkashin jagorancinsa.”
Fadar shugaban kasa ta gode wa ‘yan Najeriya kan damuwar da suka nuna na rashin dawowar shugaban kasar tare da tabbatar musu cewa mulki na tafiya ba tare da tangarda ba.
Wannan dai na zuwa ne yayin da 'yan Najeriya suka fara guna-guni game da tafiye-tafiyen Tinubu Turai musamman Faransa, ba tare da mika mulki ga Kashim Shettima ba.
Tinubu ya shafe sama da kwanaki 55 a Faransa
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya shafe akalla kwanaki 59 a kasar Faransa a wasu tafiye-tafiye takwas da ya yi.
Kasar faransa ita ce kasar farko da Tinubu ya fara ziyara bayan lashe zabe, kuma ita ce kasar da ya fi ziyartar tun bayan shiga ofis a 2023.
Legit Hausa ta tattaro bayanai game da tafiye-tafiyen da Tinubu ya yi zuwa Faransa, kwanakin da ya shafe a kowace tafiya da kuma dalilin yin tafiyar.
Asali: Legit.ng