NUC za Ta Rufe Jami'o'i domin Malamai Su Shiga Aikin INEC a Zaben 2027
- Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) na shirin sauya jadawalin karatu a jami’o’in Najeriya na mako uku zuwa huɗu domin malamai su samu damar shiga aikin zaɓen 2027
- INEC na shirin haɗa kai da shugabannin jami’o’i domin samar da ƙwararrun malamai da za su taimaka wa INEC wajen gudanar da zaɓen, musamman a matsayin jami’an tattara sakamako
- Shugaban NUC, Farfesa Abdullahi Yusufu Ribadu, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, da tawagarsa zuwa hedikwatar hukumar da ke Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta ce tana duba yiwuwar sauya jadawalin karatu a jami’o’in Najeriya na tsawon mako uku zuwa huɗu domin bai wa malamai damar shiga aikin zaɓen 2027.
Shugaban NUC, Farfesa Abdullahi Yusufu Ribadu, ne ya bayyana hakan a Abuja lokacin da shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya kai masa ziyara tare da wasu jami'an INEC.

Source: Facebook
NUC za ta tattauna da jami’o’i
Vanguard ta wallafa cewa Ribadu ya ce NUC za ta tattauna da mataimakan shugabannin jami’o’i domin zaɓo ƙwararrun malamai da za su gudanar da ayyukan zaɓe.
Ya bayyana cewa za a shirya taron tattaunawa ta yanar gizo domin sauƙaƙa wannan shiri, sannan hukumar za ta aika da takardar umarni ga jami’o’i da zarar ta samu buƙatar hakan a hukumance daga INEC.
A cewarsa, sahihancin zaɓen 2027 zai dogara matuƙa kan amincin mutanen da za a ɗora wa alhakin gudanar da shi.
Farfesa Ribadu ya ce idan ana son zaɓe mai inganci a Najeriya a 2027, dole ne a samar da ma’aikata masu gaskiya da amana.
Dalilin shirin hutun mako 4
Sakataren zartarwa na NUC ya bayyana cewa sauya jadawalin karatun zai bai wa malamai isasshen lokaci domin gudanar da ayyukan zaɓe ba tare da kawo cikas ga karatun ɗalibai ba.
Ya ce hutun da ake shirin yi ba zai wuce mako huɗu ba, inda za a tuntubi shugabannin jami’o’i domin tabbatar da cewa matakin bai kawo tsaiko ga karatu ko jadawalin zaɓen da INEC ta tsara ba.
Ribadu ya kuma jaddada cewa dole ne malaman jami’o’i da sauran ma’aikatan wucin gadi da za su shiga aikin zaɓen su kasance masu cikakken tsaka-tsaki.

Source: Facebook
Bayanin INEC kan zaɓen 2027
A nasa jawabin, shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce ziyarar na da nufin ƙarfafa haɗin gwiwar da ke tsakanin hukumar zaɓe da jami’o’in Najeriya gabanin babban zaɓen 2027.
INEC ta wallafa a Facebook cewa Amupitan ya amince cewa jami’o’i sun taka muhimmiyar rawa a zaɓukan baya, musamman ta hanyar samar da mataimakan shugabannin jami’o’i da sauran manyan malamai domin zama jami’an tattara sakamako.
Sai dai Amupitan ya ce INEC na shirin aiwatar da wasu manyan sauye-sauye ta fuskar fasaha, gudanar da aiki da tsaro domin inganta tsarin zaɓe.
Za a yi zaben gwaji
A wani labarin, kun ji cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta zaɓi rumfunan zaɓe 17,676 a faɗin Najeriya domin gudanar da gwajin na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS.
Hukumar INEC ta ce za a gudanar da gwajin ne a ranar Asabar, 28 ga Nuwamba, 2026, daga ƙarfe 8:30 na safe zuwa 2:30 na rana.
Za a gudanar da gwajin ne a rumfunan zaɓe biyu a kowace mazaba, inda za a yi amfani da mazabu 8,838 a faɗin ƙasar domin shirye-shiryen babban zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng

