An Taso Gwamnatin Tinubu a Gaba, Ana So Minista Ya Binciki Tsohon Shugaban NNPCL

An Taso Gwamnatin Tinubu a Gaba, Ana So Minista Ya Binciki Tsohon Shugaban NNPCL

  • Masu zanga-zanga sun mamaye ofishin ministan shari’a, Lateef Fagbemi, inda suka nemi a gurfanar da Mele Kyari kan zargin rashawa
  • Ƙungiyar CCA ta bukaci a binciki yadda aka kashe biliyoyin daloli a gyaran matatun mai da kuma yarjejeniyar NNPCL da Matrix Energy
  • Kabir Matazu ya nemi gwamnati ta fito da gaskiya, ta dawo da dukiyar ƙasa, kuma a hukunta masu laifi don hana maimaita hakan a gaba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wasu masu zanga-zanga sun mamaye ofishin ministan shari’a kuma Antoni Janar na kasa, Lateef Fagbemi (SAN), a ranar Talata a Abuja.

Masu zanga-zangar na ƙarƙashin ƙungiyar CCA, kuma sun nemi a gurfanar da Mele Kyari, tsohon shugaban kamfanin NNPCL.

Masu zanga zanga sun nemi minista ya gurfanar da tsohon shugaban NNPCL kan rashawa
Masu zanga zanga dauke da fastar neman tuhumar Mele Kyari a gaban ofishin ministan shari'a. Hoto: @Barde6767
Asali: Twitter

Masu zanga-zanga na so a binciki Mele Kyari

Shugaban ƙungiyar, Kabir Matazu, ya bukaci Lateef Fagbemi da ya binciki duk wasu harkokin NNPCL cikin shekaru biyar da suka wuce, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matazu ya ce:

“Mun gamsu da cire Mele Kyari daga mukaminsa, amma rashin bincike kan ayyukansa ya raunana yunkurin gwamnati kan yaki da rashawa.”

Ya bayyana cewa akwai zarge-zargen almundahana a ayyukan gyaran matatun mai, inda aka kashe biliyoyin daloli ba tare da wani taka-mai-man bayani ba.

Ƙungiyar ta ce an ce kamfanin Matrix Energy ya saka dala miliyan 400 a aikin matatar Fatakwal, alhalin gwamnati ta fitar da dala biliyan 1.5, don haka dole a binciki lamarin.

An bukaci minista ya binciki rashawa a NNPCL

Matazu ya jero tambayoyi kan wannan lamari, yana cewa:

“Me yasa gwamnati ke kulla yarjejeniyar kwangilar ayyuka ta hanyar biyan bashi da danyen mai? Wanene ya amince da hakan? Me ya sa ba a sanar da 'yan ƙasa ba?”

Kungiyar CCA da ke yaki kan rashawa ta ce akwai bukatar ministan shari’a ya binciki waɗanda suka sa hannu a yarjejeniyar, da kuma gano hanyoyin da aka bi.

“Binciken zai gano kudin da za a iya dawo da su, musamman ganin halin da tattalin arzikin ƙasa ke ciki,”

- A cewar Matazu.

Ya ce hakan zai tabbatar da an ladabtar da masu laifi kuma ya hana maimaita irin waɗannan kura-kurai a nan gaba.

Masu zanga-zanga sun nemi a binciki rasha a kamfanin NNPCL lokacin Mele Kyari
Daruruwan masu zanga zanga yayin da suka mamaye ofishin Akanta Janar a Abuja. Hoto: @Barde6767
Asali: Twitter

Bukatun masu zanga-zanga ga ministan shari'a

Shugaban kungiyar ya nemi Lateef Fagbemi da ya duba dukkanin yarjejeniyar da NNPCL ya kulla a lokacin shugabancin Mele Kyari da kwamitinsa.

Matazu ya bayyana cewa:

“Muna bukatar a kafa kwamitin bincike kan yadda aka gudanar da gyaran matatun man gwamnati, da ma yadda aka tafiyar da NNPCL na shekaru biyar.”

Masu zanga-zangar sun yi nuni da cewa dole ne gwamnati ta bayyana gaskiya game da zargin rashawa a kamfanin NNPCL da kuma masu hannu a ciki.

Sun ce za su ci gaba da matsin lamba har sai an tabbatar da gaskiya da adalci a cikin harkokin NNPCL.

NNPCL: Bola Tinubu ya sauke Mele Kyari

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya sauke Mele Kyari da Pius Akinyelure daga shugabancin NNPCL, tare da nada sababbin jagorori a kamfanin.

Bashir Bayo Ojulari ne sabon shugaban gudanarwa, ana sa ran zai jagoranci sabon salo na inganta ayyuka da tsare-tsaren kamfanin man.

Sababbin shugabannin za su mayar da hankali kan farfado da masana’antar mai, karfafa harkokin kasuwanci, da jawo sababbin masu zuba hannun jari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.