Awanni bayan An Yi Yunkurin Kashe Shi, Kotu Ta Soke Tikitin Dan Takarar Sanata a Zaben 2027
Delta, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke Warri a Jihar Delta ta soke zaɓen Sanata Ovie Omo-Agege, a matsayin ɗan takarar jam’iyyar NDC na kujerar sanatan Delta ta Tsakiya a zaɓen 2027.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Kotu ta soke tikitin tsohon mataimakin shugaban Majalissr dattawan ne bisa dalilin rashin bin tanade-tanaden dokar zaɓe.
Leadership ta rahoto cewa kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Hyeladzira Ajiya Nganjiwa, ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta cire sunan Omo-Agege daga jerin ’yan takara.
Sannan ta hana tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan bayyana kansa a matsayin ɗan takarar NDC na kujerar sanatan.
A wani hukunci da ya ƙara jefa NDC cikin matsala, kotun ta ce wa’adin doka na gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani domin zaɓen wani ɗan takara ya riga ya ƙare. Ta lura cewa dokar zaɓe ta tanadi wa’adin kwanaki 180 kafin babban zaɓe.
Ku saurari karin bayani...
Asali: Legit.ng