Me Zai Faru da Fafaroma Francis Ya Rasu? An Ji Yadda Ake Zaben Jagoran Kiristoci
- Fafaroma Francis ya rasu yana da shekaru 88 bayan shekara 12 yana jagorantar cocin Katolika, wadda ke da mabiya biliyan 1.4 a duniya
- Rasuwarsa ta janyo an soma bin tsarin zaɓen sabon Fafaroma da aka gada tun kaka da kakanni, wanda manyan jami'ai 138 ke gudanarwa
- A wannan rahoton, Legit Hausa ta yi bayanin yadda ake zaben sabon Fafaroma, masu zaben da wanda ya cancanci zama jagoran Katolika
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Vatican - Fafaroma Francis ya rasu yana da shekaru 88, bayan ya shafe shekara 12 yana jagorantar cocin Katolika ta duniya.
Rasuwarsa ta sa aka fara aiwatar da tsarin da aka gada tun ƙarni da dama na zaɓen sabon Fafaroma.

Asali: Getty Images
Menene aikin Fafaroma?
Fafaroma shi ne shugaban cocin Katolika na duniya, kuma mabiya Katolika na ganin cewa yana da alaƙa kai tsaye da Yesu Almasihu, inji rahoton BBC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana ɗaukar Fafaroma a matsayin magajin Saint Peter, wanda shi ne babban almajirin Yesu.
Wannan yana ba shi cikakken iko a kan cocin Katolika gaba ɗaya, kuma hakan ya sa yake da girman iko ga mabiya Katolika kimanin biliyan 1.4 na faɗin duniya.
Duk da cewa da dama daga cikin mabiya Katolika na karanta Littafi Mai Tsarki don shiriya, amma ana ganin, suna dogaro da koyarwar Fafaroma ne, wanda ke jagorantar akidar da ayyukan cocin.
Kusan rabin mabiya Kiristanci a duniya mabiya cocin Katolika ne. Amma Sauran mazhabobi irin su Protestants da Orthodox ba su yarda da ikon Fafaroma ba.
Fafaroma na zaune ne a birnin Vatican, ƙaramar ƙasa mai cin gashin kanta da ke cikin Roma, babban birnin Italiya.
Fafaroma baya karɓar albashi, amma ana daukar nauyin duk kuɗin tafiye-tafiye da kuma buƙatun rayuwarsa daga baitul malin Vatican.
Me ke faruwa idan Fafaroma ya rasu?
A baya, ana gudanar da jana'izar Fafaroma ne cikin wani irin tsari mai sarkakiya, amma Fafaroma Francis ya amince da saukaka duk wasu wahalhalu na jana'izarsa.
An birne Fafaroma na baya a cikin akwatuna uku: na itacen cypress, na ƙarfe (lead) da kuma na itacen oak. Amma Francis ya zaɓi a birne shi a akwatin katako mai ratsin (zinc).
Ya kuma soke tsarin nuna gawar Fafaroma a kan wani dandalin da ake kira 'catafalque' a cikin cocin St Peter don jama’a su kalla, kamar yadda aka saba.
A maimakon haka, za a bar gawarsa a cikin akwatin, amma a cire murfin domin masu makoki su ga gawar yayin da suke nuna girmamawa ga gawarsa.
Francis kuma zai kasance Fafaroma na farko cikin fiye da ƙarni guda da za a binne shi a wajen Vatican.
Za a birne shi a Basilica of St Mary Major, ɗaya daga cikin manyan basilicas huɗu na Fafaroma da ke birnin Roma.
Waɗanne mutane ne ke zaɓar sabon Fafaroma?
Babban zaɓen Fafaroma na gaba na hannun manyan jami’an cocin Katolika da ake kira 'College of Cardinals'.
Dukansu maza ne da Fafaroma ya naɗa kai tsaye, kuma yawanci sukan kasance masu mukamin 'Bishof' na cocin.
A halin yanzu akwai jami'ai 252, amma 138 daga cikinsu ne kaɗai ke da haƙƙin kaɗa ƙuri’a saboda sauran sun haura shekaru 80.
Duk da cewa waɗanda suka haura shekaru 80 ba su da damar zaɓe, suna iya shiga muhawara da tattaunawa kan wanda ya dace a zaɓa.
Ta ya ya ake zaɓar Fafaroma?
Bayan rasuwar Fafaroma (ko murabus kamar yadda Pope Benedict XVI ya yi a 2013), ana kiran jami'an Katolika zuwa taro a Vatican, domin a zaɓi sabon Fafaroma.
A wannan lokaci kafin nadin sabon Fafaroma, su kungiyar masu zaben Fafaroman (College of Cardinals) ne ke tafiyar da al’amuran cocar.
Ana gudanar da zaben ne cikin sirri a cikin wani wuri da ake kira 'Sistine Chapel', wanda wani da ake kira Michelangelo ya zana hotuna masu ban mamaki a cikinta.
Jami'an na duba bayanan wadanda suka cancanta, har sai an samu wanda ya ci zaɓe, kuma wannan na iya ɗaukar kwanaki ko makonni. A baya ma an samu zaɓen da ya ɗauki watanni.
Jaridar Daily Express ta rahoto cewa, alamar da jama’a ke bi don sanin yadda zaɓen ke tafiya ita ce hayaƙin da ke tashi daga ƙona ƙuri’un jami'an.
Idan aka ga hayaƙi baƙi, to alamar ba a yi nasara ba, amma da zarar an ga hayaƙi fari to haka na nufin an zaɓi sabon Fafaroma.
Ya ya ake sanar da duniya sabon Fafaroma?
Bayan farin hayaƙin ya tashi, sabon Fafaroma yakan bayyana cikin awa guda a saman baranda da ke fuskantar babban filin taro na St Peter’s Square.
Babban jami'i da ke halartar zaben zai sanar da nasarar zaben ta hanyar furta kalmar Latin "Habemus Papam", ma’ana "mun samu sabon Fafaroma."
Zai bayyana sabon Fafaroma da sunan da ya zaɓa domin jagorancinsa, wanda ba lallai ba ne ya kasance sunan da aka rada masa na haihuwa.
Misali, an haifi Fafaroma Francis da suna Jorge Mario Bergoglio, amma ya zaɓi sunan Francis a matsayin girmamawa ga Saint Francis na Assisi.

Asali: Getty Images
Wa za a iya zaɓa a matsayin Fafaroma?
A ka’idar addini da mazhabar Katolika, kowanne namijin da ke bin Katolika da aka yi masa wankan tsari na baftisma na iya tsayawa takarar zama Fafaroma.
Amma a aikace, jami'an cocin Katolika sun fi son zaɓar daya daga cikinsu.
Lokacin da aka zaɓi Fafaroma Francis daga Argentina a 2013, ya kasance Fafaroma na farko daga Kudancin Amurka, yankin da ke da kashi 28% na mabiya Katolika.
Sai dai tarihi ya nuna cewa mafi yawan Fafaroma sun fito ne daga Turai, musamman ma Italiya.
Daga cikin Fafaroma 266 da aka taɓa zaɓa, 217 daga cikinsu Italiyawa ne.
Fafaroma Francis ya tsallake hari a baya
A wani labarin, mun ruwaito yadda, Shugaban darikar Katolika, Fafaroma Francis, ya bayyana yadda ya tsallake harin 'yan kunar bakin wake a kasar Iraqi.
Fafaroman Francis ya bayyana cewa an gargade shi da kada ya ziyarci kasar saboda barazanar tsaro da ke tattare da hakan amma ya ki saurare.
Ya ce jami’an tsaron kasar Iraqi ne suka dakile yunkurin ‘yan kunar bakin waken, inda suka tarwatsa shirin kafin su kai ga samun nasara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng