'Yan Takara 8 Sun Janye, Sun Hakura da Neman Mulki a Babban Zaben 2027

'Yan Takara 8 Sun Janye, Sun Hakura da Neman Mulki a Babban Zaben 2027

’

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

  • ’Yan takarar kujerar Sanatan Zamfara ta Yamma takwas sun janye daga shiga zaɓen 2027 tare da mara wa Sanata Abdulaziz Yari baya
  • ’Yan takarar na jam'iyyun adawa daban-daban sun yi alƙawarin yin aiki domin ganin Yari da APC sun yi nasara a zaɓe mai zuwa
  • Zanata Yari ya shigar da su cikin kwamitin yaƙin neman zaɓensa na majalisar dattawa nan take

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Nigeria - ’Yan takarar kujerar Sanatan Zamfara ta Yamma takwas sun janye daga takara tare da bayyana goyon bayansu ga Sanata mai ci, Abdulaziz Yari Abubakar, na jam’iyyar APC.

’Yan takarar sun sanar da janyewarsu ne a ranar Talata a Gusau, inda suka yi alƙawarin yin aiki domin ganin Sanata Yari da APC sun yi nasara a zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Bayan rashin 'yan APC 15, tsohon sakataren gwamnatin Zamfara ya rasu

Sanata Yari.
Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben APC kuma Sanata mai wakiltar Zamfara ta Yamma, Abdulaziz Yari Hoto: Abdulziz Yari
Source: Facebook

Yan takara 8 sun janyewa Abdulaziz Yari

Leadership ta1 ruwaito cewa ’yan takarar sun haɗa da Alhaji Sani Abdullahi na APP, Alhaji Ibrahim M. Anka na NDP, Alhaji Sanusi Mohammed na YPP, da Alhaji Yahaya Aliyu na LP.

Sauran sun haɗa da Alhaji Abdulmalik Adamu na APM, Alhaji Murtala Abubakar na jam'iyyar Accord, Alhaji Anas Usman na SDP da Hajiya Aishat S. Pawa ta ADP.

Da yake magana a madadin ’yan takarar takwas bayan kowannensu ya sanar da janyewarsa, Abdullahi ya ce sun ɗauki matakin ne domin amfanin al’ummar Zamfara ta Yamma.

Ya bayyana naɗin Sanata Yari a matsayin Darakta Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC a matsayin karramawa da ta cancanci goyon bayan ’yan jihar Zamfara masu kishin ƙasa, ba tare da la’akari da bambancin jam’iyyunsu ba.

Abdullahi ya kuma yi alƙawarin cewa ’yan takarar za su yi aiki tukuru domin tabbatar da nasarar Sanata Yari da APC a zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnoni 5 suka yi wa Atiku buƙulu, aka hana PDP samun nasara a zaben 2023

Abdulaziz Yari ya yi martani

A nasa martanin, Sanata Yari ya yaba wa ’yan takarar kan matakin da suka ɗauka, tare da tabbatar musu cewa ba za su yi nadamar goyon bayansa ba.

Ya ce matakin nasu ya nuna ƙudurinsu na taimakawa wajen gina Najeriya mafi kyau.

Sanata Yari ya kuma sanar da shigar da su cikin kwamitin yaƙin neman zaɓensa na majalisar dattawa nan take, inda ya yi alƙawarin ba su dama da karramawa daidai da sauran ’ya’yan jam’iyyar.

Yari.
Sanata Abdulaziz Yari tare da yan takara 8 da suka janye masa a mazabar Zamfara ta Yamma Hoto: Mubarak Hassan
Source: Facebook

Ya bayyana burin Shugaba Bola Tinubu na sake tsayawa takara a wa’adi na biyu a matsayin wata dama ta haɗa kan ƙasar, ƙarfafa zaman lafiya da jituwa, da kuma bunƙasa jin daɗin ’yan Najeriya baki ɗaya.

Sanata Yari ya tara malamai a Zamfara

Kun ji cewa daraktan kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulaziz Yari ya karɓi baƙuncin malaman addinin Musulunci 1,500 a garin Talata Mafara.

Yari, ya taɓa zama gwamnan jihar Zamfara, ya ce malaman sun taru ne domin yin addu’ar samun zaman lafiya da kuma yi wa Gwamna Dauda Lawal addu’a yayin shirye-shiryen fara yaƙin neman zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262