Ana Rade Radin An Hana Shi Shiga Aso Villa, Shettima Zai Gana da Mutanen Filato

Ana Rade Radin An Hana Shi Shiga Aso Villa, Shettima Zai Gana da Mutanen Filato

  • Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima zai kai ziyara Filato ranar Litinin, domin duba halin da ake ciki bayan hare-haren 'yan bindiga
  • Ministan jin kai na Najeriya ya ce Shettima zai gana da masu ruwa da tsaki domin tattauna hanyoyin kawo ƙarshen rikice-rikice a jihar
  • A hannu daya, ministan tsaro, Mohammed Badaru ya jaddada cewa gwamnati za ta cafke wadanda ke kai hare-haren domin a hukunta su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, zai kai ziyara jihar Filato a ranar Litinin, domin duba halin da ake ciki bayan hare-haren 'yan bindiga.

Rahoton Amnesty International ya nuna cewa sama da mutane 50 ne aka kashe a hare-hare daban daban da aka kai kananan hukumomin Bokkos da Bassa.

Gwamnati ta sanar da cewa Shettima zai ziyarci Filato kan kashe kashen da aka yi
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima. Hoto: @officialSKSM
Asali: Facebook

Shettima zai ziyarci Filato kan hare-hare

Ministan jin kai da rage Talauci, Dr Nentawe Yilwatda, ne ya bayyana haka yayin wata ziyara da ministan rsaro, Mohammed Badaru, ya kai Filato, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce Mohammed Badaru ya ziyarci garuruwan da hare-haren 'yan bindigar ya shafa a karamar hukumar Bassa a ranar Asabar.

Dr Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa:

"Hakika muna tare da ku, haka kuma shugaban kasa ya damu matuka kan halin da kuke ciki, shi ya sa ya umarce mu da mu zo, ni da ministan tsaro don duba ku.
"Makon da ya gabata, NSA ya kawo ziyara. Kuma a ranar Litinin, mataimakin shugaban kasa zai zo ya gana da masu ruwa da tsaki domin kawo karshen kashe-kashen da ke faruwa a Filato."

Abin da minista ya fada wa mutanen Filato

Jaridar ta rahoto cewa yayin ziyarar, Shettima zai jagoranci wani taron masu ruwa da tsaki domin tattauna dabarun tsaro da tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Ministan tsaro, Mohammed Badaru, wanda ya samu rakiyar babban kwamandan runduna ta 3 na sojojin Najeriya, Manjo Janar Folusho Oyinlola, da wasu manyan jami’an tsaro, ya tabbatar wa jama’a da kudirin gwamnatin tarayya na kawo karshen kashe-kashen.

Badaru ya jaddada cewa gwamnati za ta dauki matakin gaggawa wajen magance matsalar tsaro domin dakile asarar rayukan jama'a.

Ministan tsaro, Mohammed Badaru ya yi magana kan tsaro a Filato
Ministan tsaro, Mohammed Badaru lokacin da ya sauka jihar Filato. Hoto: @OAlmarkazy
Asali: Twitter

Gwamnati ta fara ba mutanen Filato tallafi

Mohammed Badaru ya bayyana cewa:

“Shugaban kasa ya damu matuka da abubuwan da ke faruwa, kuma ya umurce mu da kamo wadanda ke da hannu a wadannan laifuffuka domin su fuskanci hukunci.”

Ya kara da cewa jami’an tsaro na gudanar da bincike sosai, kuma da yardar Allah, za a kamo masu laifin, a gurfanar da su gaban shari’a.

Ministan ya kuma bayyana cewa an riga an fara ba da tallafi ga wadanda lamarin ya shafa, ciki har da shirin kula da matan da mazajensu suka mutu.

'Yan ta'adda sun kashe utane 50 a Filato

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan al’ummar Zike da ke karamar hukumar Bassa, inda suka kashe mutane 40 a wani sabon hari a Filato.

Rahotanni sun tabbatar da cewa mutane da dama sun jikkata yayin harin, kuma ana kula da su a asibitoci daban-daban na fadin jihar.

Shugabannin Kiristoci sun shirya yin zanga-zangar lumana ranar Litinin 21 ga Afrilu domin nuna fushinsu kan kashe-kashen da suka addabi jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.