NiMet: Za a Sha Ruwa da Tsawa a Kaduna, Kwara da Wasu Jihohi a cikin Kwanaki 3

NiMet: Za a Sha Ruwa da Tsawa a Kaduna, Kwara da Wasu Jihohi a cikin Kwanaki 3

  • NiMet ta yi hasashen za a samu saukar ruwa da tsawa gami da iska daga Lahadi zuwa Talata a Taraba, Ekiti, da wasu jihohin Najeriya
  • Ana sa ran za a samu ruwan sama da tsawa a jihohin Filato, Abuja, Nasarawa, Kwara, Neja, Kogi, da kuma sassan Kudu maso Yamma
  • Hukumar ta shawarci jama’a su yawaita shan ruwa, su guji fita waje idan ana tsawa, sannan su dauki matakan kare lafiyarsu a ranakun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta bayyana hasashen saukar ruwan sama hade da tsawa a sassa daban-daban na kasar daga Lahadi zuwa Talata.

A cikin sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Asabar a Abuja, an nuna yiwuwar samun hadurra sakamakon iska mai karfi a Taraba, Adamawa da Kaduna ta Kudu.

Hukumar NiMet ta lissafa jihohin da za su fuskanci ruwa da tsawa na kwanaki 3
Yayin da ake zabga ruwan sama hade da tsawa. Hoto Angelo F
Asali: Getty Images

NiMet ta yi hasashen ruwa da tsawa

NiMet ta ce za a samu ruwa hade da tsawa a jihohin Filato, Abuja, Nasarawa, Kwara, Neja da Kogi da hadari a Arewa ta Tsakiya, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A Kudu, an yi hasashen haduwar hadsari da safiyar Lahadi tare da yiyuwar hadari hade da tsawa a Cross River, Akwa Ibom, Rivers da Delta.

Har ila yau, hukumar ta yi hasashen cewa za a iya samun ruwa hade da tsawa a wasu sassa na jihohin Anambra, Oyo, Edo, Imo, Abia, Ekiti, da sauransu.

Hasashen yanayin NiMet na ranar Litinin

A ranar Litinin, NiMet ta ce za a samu rana mai zafi a yawancin arewacin Najeriya, sannan za a iya samun ruwa hade da tsawa a wasu sassan Adamawa, Taraba da Kaduna da yamma.

Arewa ta Tsakiya kuwa za ta iya fuskantar zafin rana da kuma hadari da safiyar Litinin, sai kuma tsawa da yamma a jihohin Filato, Abuja, Benue, Kogi, Kwara da Nasarawa.

A kudu kuma, za a samu hadari hade da zafin rana, tare da yiyuwar tsawa a Akwa Ibom, Rivers da Cross River da safe, sannan hakan na iya faruwa a jihohin Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas da Yamma.

Jihohin da ruwa zai sauka a ranar Talata

A safiyar Talata kuwa, NiMet ta ce za a samu hasken rana da dan hadari a Arewa, sai dai ana hasashen samun hadari mai hade da tsawa a Taraba da Yamma.

Za a kuma iya samun ruwa a Taraba, Adamawa da Kaduna. A Arewa ta Tsakiya kuwa, za a samu hadari da safe, da kuma tsawa da yamma a Benue, Kogi, Kwara, Nasarawa da Abuja.

A Kudu, za a samu hadari da safe tare da hadari hade da tsawa a Cross River, Akwa Ibom da Lagos. Daga baya, za samu tsawa a Abia, Imo, Ebonyi, Anambra, Oyo, Edo, Delta da sauransu.

Jihohin Najeriya da ruwan sama zai sauka hade da tsawa daga Lahadi zuwa Talata
Yadda ruwan sama ke sauka tare da tsawa. Hoto: Angelo F
Asali: UGC

Hukumar NiMet ta ba 'yan Najeriya shawara

NiMet ta shawarci jama’a su zauna a wurare masu iska da sanyi tare da shan ruwa sosai saboda zafin rana da ka iya janyo gajiya ko rashin lafiya.

Ta kuma shawarci jama’a su yi allurar rigakafin cutar sankarau, su rika wanke hannu akai-akai, guje wa cunkoso da saka takunkumi, da nisantar masu fama da cututtuka.

Haka kuma ta bukaci jama’a su guji fitowa daga rana daga karfe 12:00 na rana zuwa 3:00 na yamma, su kuma kula da guguwar da ka iya tasowa kafin zuwan ruwa.

Hukumar ta bukaci kamfanonin jirgin sama su rika tuntubar NiMet domin samun rahoton yanayi na filin jirgi kafin tashinsu.

Ruwan sama ya yi gyara a jihar Kebbi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gidaje sama da 240 sun lalace sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da ya sauka a ƙaramar hukumar Shanga ta Kebbi a makon farko na Afrilu.

An bayyana cewa ruwan ya sauka da ƙarfi fiye da yadda aka saba gani, wanda ya jawo rushewar gine-gine da dama tare da jefa mazauna yankin cikin ƙunci.

Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana jimami kan lamarin tare da alƙawarin samar da agajin gaggawa domin tallafa wa waɗanda ambaliyar ta shafa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.