Rai Bakon Duniya: Fitaccen Mawakin Yabo a Najeriya Ya Mutu Yana da Shekaru 50

Rai Bakon Duniya: Fitaccen Mawakin Yabo a Najeriya Ya Mutu Yana da Shekaru 50

  • Fitaccen mawaƙin yabo, Bolaji Olarewaju (Big Bolaji), ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya, inda ya bar babban gibi a harkar waƙar yabo
  • An bayyana rasuwarsa da cewa "abin alhini ne mai girma," yayin da iyalansa suka ce za a sanar da lokacin jana’izarsa a nan gaba kadan
  • Marigayi Bolaji ya kasance jagora a cocin RCCG, kuma ya taka babbar rawar gani a fagen shirya bukukuwan waƙokin bishara a Ibadan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Osun - Fitaccen mawaƙin yabon Yesu kuma shahararren mai gabatar da shirin rediyo, Bolaji Adedotun Olanrewaju, wanda aka fi sani da Big Bolaji, ya rasu.

Ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya a ranar Asabar, 19 ga Afrilu, 2025, kamar yadda iyalansa suka tabbatar a wata sanarwa.

Fitaccen mawakin yabo, Big Bolaji ya rasu yana da shekaru 50
Mawakin yabo a addinin Kirista, Big Bolaji. Hoto: @HPmusicgang
Asali: Twitter

Fitaccen mawakin yabon Kirista ya rasu

Jaridar The Nation ta rahoto iyalan marigayi Big Bolaji, a cikin sanarwar, sun bayyana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Cikin kuncin da ba za a iya misaltawa ba muke sanar da rasuwar Bolaji Olarewaju, wanda aka fi sani da Big B, uba, miji, kuma shugaban addini da al’umma."

Sun kara da cewa:

"Ya rasu ne a ranar Asabarin Easter, bayan gajeriyar rashin lafiya. Rasuwarsa ta bar giɓi da ba za a iya cikewa ba.
“Rayuwar Bolaji ta kasance wani misali na soyayya ga wake, bangaskiyar sa mai ƙarfi, da jajircewarsa wajen faranta wa jama’a rai.

Iyalansa sun bayyana cewa za a sanar da cikakken bayani kan lokacin jana’iza a gaba, yayin da ake shirin tunawa da irin gagarumin gudummawar da ya bayar a yabon addinin Kirista.

Tasirin Big Bolaji ga wakar yabo a Ibadan

Marigayi mawaki Bolaji ya shafe tsawon lokaci yana shirya taron kiɗa da wake na shekara-shekara da ake kira "Turn It Up With Big Bolaji" a birnin Ibadan.

An rahoto cewa marigayi Bolaji dan asalin jihar Osun ne, amma ya girma a Ibadan. Shi ƙwararren mai nazarin harkar kadarori ne.

Bolaji ya samu shiriya ne a cocin Sword of the Spirit Ministries karkashin jagorancin Bishop Francis Wale Oke, inda aka karfafa masa gwiwa a cikin addinin Kirista.

Har ila yau, Bolaji jagora ne da aka naɗa a cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), kuma yana cikin kwamitin gudanarwa na baje kolin wakoki Living Spring Music.

Mutane sun yi alhinin mutuwar Big Bolaji

Legit Hausa ta tattaro kadan daga cikin sakonnin mutane kan mutuwar mawakin yabo, Big Bolaji.

Gbenga Philips ya wallafa a shafinsa na X cewa:

"Na kasa yarda da cewa ka tafi ka bar mu. Wai yanzu shikenan Big Bolaji ka mutu?"

@shola_olushola ya wallafa a X cewa:

"Big Bolaji, abin takaici ne jin labarin rasuwarka. Kai mutum ne na musamman a harkar waƙokin bishara, musamman a Ibadan.

"Tasirin da ka yi ga matasa yana da girma, kuma tarihin rayuwarka zai dade yana kasancewa cikin zukatanmu.
"Allah ya ba iyalanka da abokanka haƙuri da ƙarfin zuciya na jure rashinka."

Omoluabi Ibadan, @ibadan_pikin shi ma ya yi alhinin mutuwar Big Bolaji a X yana mai cewa:

"Duniya waƙar bishara ta rasa ɗaya daga cikin fitattun taurari a cikinta. Mashahurin mawaƙin kirista, Olarewaju Bolaji wanda aka fi sani da Big B, ya rasu."

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.