2027: Fastocin Neman Kujerar Shugaban Kasa na Gwamna Bala Sun Bazu a Bauchi
- Fostoci neman takarar shugaban kasa a 2027 na Gwamna Bala Mohammed sun mamaye manyan tituna na lungu da sakon jihar Bauchi
- An hango fostocin a manyan tituna kamar Railway Road, Sabon Titin Karofi da Kofar Dumi, inda aka manna su a wurare masu jan hankali
- Sai dai ma'abota soshiyal midiya sun yi martani mai zafi game da wadannan fastoci, har wasu ke nuna rashin cancantar gwamnan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bauchi - Fostocin da ke nuna cewa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed na neman takarar shugaban kasa a 2027 sun mamaye jihar.
An hango fastocin Kaura dauke da rubutu kamar haka, "Kaura a matsayin shugaban kasa 2027" a kan titunan Bauchi da sha-tale-talen jihar.

Asali: Facebook
2027: Fastocin gwamnan Bauchi sun bazu
Wakilin jaridar Daily Trust ya rahoto cewa an manna fastocin ne a wurare masu mahimmanci, ciki har da manyan tituna, sandunan lantarki da kuma kan allunan talla a cikin birnin jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wakilin jaridar ya lura cewa an hango fostocin a manyan titunan Railway Road, Sabon Titin Karofi, da Kofar Dumi da sauransu.
Wani matashi daga cikin wadanda aka dauki aiki domin manna fostocin, Aminu Auwal, ya yi karin haske game da wadanda suka bayar da kwangilar aikin.
Wadanda suka ba da kwangilar manna fastocin
Aminu Auwal ya bayyana cewa wasu ‘yan siyasar jihar biyu da ya bayyana sunayensu da Ya’u Ortega da Talolo ne suka dauke su aikin manna fastocin.
Aminu ya ce:
“An umarce mu da mu manna fostocin gwamnan a manyan titunan Bauchi. Mun fara aikin ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare kuma muna fatan kammalawa yau.”
Kokarin jin ta bakin Ortega da Talolo ya ci tura domin wayoyinsu ba su shiga ba har zuwa lokacin da aka hada wannan rahoto.

Asali: Facebook
"Babu gurbi a Aso Rock" - Martanin 'yan soshiyal midiya
Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin ra’ayoyin masu amfani da kafafen sada zumunta:
Abdulwaheed Ijebu Olaegbe:
“Babu gurbi a Aso Rock... 4+4... A kan amanar Tinubu nake tsaye.”
Abouvakar Dawood:
“Karshe dai yana yi wa wani aiki ne. Idan ka yarda da takarar Bala to ka jefa kanka cikin gagari.”
Abubakar Baba:
“Barayi ba za su sake mulkar ƙasar nan ba. Ya shirya, domin EFCC za ta kama shi bayan ya sauka daga mulki.”
Tabubakar Noble Valley:
“Ba na kaunar kowanne ɗan siyasa a Najeriya. Allah ya sa abin da ya sata ya kone kurmus.”
Aleeyhou Ghiade:
“A zaben baya, ya samu kuri’u 20 ne kacal daga ƙananan hukumomi 20 na Bauchi. Idan ya yi kuskuren tsayawa takarar Sanata, ko kuri'u 7 ba zai samu ba.”
Hassan Zulkifli:
“Har a zuciyarsa ya san ba zai ci ba, amma zai kwashi biliyoyin kudin Bauchi ya kashe wajen neman shugaban ƙasa.”
Jibrin Ali Kwadan:
“Idan bai kashe kudin da ya sata ba, ba zai samu salama ba. Gwamnoni da yawa sun gwada hakan bayan wa’adinsu na biyu suka kasa samun nasara.”
Lukman Isah:
“Ina da tabbacin ba zai ci kujerar Sanata ba bayan wa’adinsa, bare shugaban ƙasa.”
Sen Sabiu Musa:
“Wannan shine dalilin da ya sa bai shiga tawagar Atiku ba. Shin gwamna mai barin mulki yana mafarkin zama shugaban ƙasa?”
Fastocin Ganduje sun jawo ce-ce-ku-ce
A wani labarin, mun ruwaito cewa, fastocin takarar shugaban kasa na Abdullahi Ganduje tare da Gwamna Hope Uzodinma a matsayin mataimakinsa sun karade yanar gizo.
A cikin fastocin, an nuna cewa Ganduje zai tsaya takarar shugabancin ƙasa a zaɓen 2027, yayin da Uzodinma ke matsayin abokin takararsa.
Sai dai Ganduje ya nesanta kansa daga waɗannan fastoci, yana mai cewa wasu masu son tayar da zaune tsaye ne ke ƙoƙarin haddasa masa rikici da Shugaba Bola Tinubu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng