‘Kafin Na Mutu Zan Saki Bidiyo’; Yar TikTok da Aka Kora daga Soja Za Ta Yi Bankada
- Ruth Ogunleye, wata tsohuwar jami’ar sojin Najeriya da aka sallama daga aiki, ta jawo magana bayan wallafa wani bidiyo
- Ta nemi mahaifinta ya yafe mata kan rashin bin shawararsa, tare da bayyana yadda take son a yi jana'izarta
- Wannan na zuwa ne bayan wata kotun tarayya da ke Kaduna ta yanke mata hukuncin ɗaurin shekara ɗaya kan wasu tuhume-tuhume
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Wata tsohuwar jami’ar sojin Najeriya, Ruth Ogunleye, ta jawo hankalin jama’a bayan wani bidiyo da ta wallafa a kafafen sada zumunta.
Tsohuwar sojar ta yi magana kan mutuwa da yadda take son a yi jana'izarta idan rai ya yi halinsa.

Source: Facebook
A cikin bidiyon da TheCable ta gano, Ogunleye ta nemi afuwar mahaifinta saboda rashin bin shawarwarinsa a lokacin da take rikici da rundunar sojin Najeriya.

Kara karanta wannan
Sanata ya ji kalaman da 'yan bindiga suka faɗa lokacin da suka bude wa tawagarsa wuta
Ta ce kafin mutuwarta za ta wallafa wasu bidiyoyi a kafafen sada zumunta domin jama’a su gani, sannan ta bayyana cewa ta fahimci mahaifinta yana faɗin gaskiya.
Yar TikTok din ta kuma roƙi iyalanta da su birne ta a cikin akwatin gawa mai launin shuɗi, su sanya mata gashin kanta na ƙari, tare da gyara farcenta kafin jana'izarta kuma a binne ta a Oto, kusa da gefen titi.
Hukuncin kotu kan Ogunleye
Wannan bidiyo ya fito ne makonni bayan wata babbar kotun tarayya da ke Kaduna ta same ta da laifi kan tuhume-tuhume biyar da suka shafi wallafa bidiyoyin ɓata suna kan Oluyemi Thomas Olatoye, kwamandan makarantar horas da sojoji ta NDA.
A ranar 10 ga Nuwambar 2026, Mai shari’a Rilwanu Aikawa ya yanke mata hukuncin ɗaurin shekara guda kan kowanne tuhume-tuhume, inda hukuncin zai gudana lokaci guda.
Sai dai alkalin ya dakatar da aiwatar da hukuncin ɗaurin na tsawon shekaru uku bisa yarjejeniyar amincewa da laifi. Kotun ta kuma ci tarar ta.

Kara karanta wannan
Abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da matar da ake zargin Sarkin Daura ya taɓa jikinta
Ogunleye, wadda aka tsare tun watan Satumban 2026, ta bayyana cewa tana ganin an yi mata rashin adalci a shari’ar, tana mai cewa ba ta aikata laifukan da ake zarginta da su ba.

Source: Original
Yadda rikicin ya fara
Rikicin Ruth Ogunleye da rundunar sojin Najeriya ya samo asali ne bayan an tura ta aiki a cibiyar kula da lafiya ta Cantonment Medical Centre da ke Ojo, Lagos, inda ta haɗu da Kanal Ishiaku Abdulkareem.
A wani bidiyo da ta wallafa a TikTok a watan Janairun 2024, ta zargi babban jami'in sojin da neman yin lalata da ita, amma ta ƙi amincewa.
Ta yi zargin cewa bayan ta ƙi amincewa, kanal ɗin ya yi barazanar korarta daga aikin soja, ya hana ta damar zuwa kwas ɗin ɗaukaka matsayi, tare da ƙin amincewa da buƙatarta ta samun izinin fita.
Ta kuma yi zargin cewa duk lokacin da ta kai ƙara ga manyan jami'an soji, Abdulkareem yana gaya musu cewa tana fama da matsalar tabin hankali, cewar Punch.
Sai dai a watan Nuwambar 2024, rundunar sojin Najeriya ta wanke Kanal Abdulkareem daga dukkan zarge-zargen da Ogunleye ta yi masa.
Kakakin rundunar a lokacin, Onyema Nwachukwu, ya bayyana cewa binciken rundunar 'yan sandan soji ya nuna cewa kanal ɗin bai aikata laifukan da ake zarginsa da su ba.
Yadda yar Nollywood ta zama sojar Amurka
A baya, an ji cewa jarumar fina-finan Nollywood ta bayyana cewa wasu ‘yan Kamaru da ta haɗu da su a coci ne suka ƙarfafa mata gwiwar shiga aiki soja.
Ta ce kasancewarta sojan Amurka na fuskantar ƙalubalen sauyin al’ada, amma tana alfahari da asalin Najeriya.
Matashiyar ce idan yaƙi ya ɓarke tsakanin Najeriya da Amurka, za ta kasance cikin mawuyacin hali.
Asali: Legit.ng