Boka Haram Sun Kai Sabon Hari Borno, Sun Kashe Sojoji da Fararen Hula Masu Yawa

Boka Haram Sun Kai Sabon Hari Borno, Sun Kashe Sojoji da Fararen Hula Masu Yawa

  • Boko Haram sun kai hari a garinYamtake da ke Gwoza, inda suka kashe sojoji biyu da fararen hula da ba a san adadinsu ba tukuna
  • Sanata Ali Ndume ya bayyana damuwarsa kan harin, yana mai cewa kwanan nan mutanen Yamtake suka koma gidajensu daga gudun hijira
  • Ya yaba da kokarin sojoji wajen kare Borno, ya kuma bukaci kafa rundunar tsaron al'umma don taimaka musu a yaki da Boko Haram

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Ana fargabar wasu mayakan kungiyar Boko Haram sun kai mummunan hari a garin Yamtake da ke karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

Wasu majiyoyin tsaro da ke a yankin Yamtake, sun bayyana cewa 'yan ta'addan sun kashe sojoji biyu da kuma fararen hula da ba a tantance adadinsu ba.

Boko Haram sun kai hari Borno da ya yi ajalin sojoji biyu da fararen hula
Dakarun sojojin Najeriya na musamman da CDS ya kafa domin kawo karshen Lakurawa a Sokoto, Kebbi. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Boko Haram sun kashe sojoji, farar hula a Borno

Rahoton jaridar Daily Trust, ya nuna cewa maharan sun kutsa garin Yamtake da misalin karfe 11:15 na daren ranar Alhamis, inda suka bude wa jama'a wuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya daga rundunar soji ta ce kafin a samu isowar karin dakarun taimako daga Gwoza, maharan sun kai farmaki kan sansanin soji da ke Yamtake.

“Muna jiran karin bayani daga dakarun da suka je kai dauki, amma an tabbatar da mutuwar sojoji biyu da wasu fararen hula. Ya kamata mu jira karin bayani,” inji majiyar.

Sanata Ndume ya magantu kan farmakin Yamtake

Sanata Ali Ndume, dan majalisar dattawa daga Borno ta Kudu, ya bayyana cewa yana kan tattaunawa da al’ummar Yamtake tun bayan faruwar harin.

“Abin takaici ne matuka yadda Boko Haram suka farmaki mutanen Yamtake da tsakar dare. Kwanan nan mutanen garin suka dawo gidajensu daga gudun hijira.
“Sannan, mun yi Allah-wadai da kisan sojoji biyu da fararen hula da ba a kai ga bayyana adadinsu ba. Muna addu'ar Allah ya jikan su.”

Sanata Ndume ya jijinawa sojoji a Borno

Sanata Ndume ya yaba da kokarin kwamandan hadaddiyar tawagar jami'an tsaro ta 26, Birgediya Janar Nasir Abdullahi da dakarunsa wajen dakile hare-hare da dama a garin Gwoza.

“Bayan maharan sun kai hari a Yamtake, sun yi yunkurin kutsawa cikin garin Gwoza, amma dakarun soji sun yi nasarar fatattakar su.
“A lokuta da dama, sojoji suna kafa tarko a kusa da Gwoza domin hana maharan da ke kokarin tarwatsa mutanen garin daga gidajensu, wannan ya na da tasiri sosai.
“A cikin watan da ya gabata, Boko Haram sun kai hare-hare da dama a yankunan Borno ta Arewa, Kudu da Tsakiya ba tare da jami'an tsaro sun mayar da martani mai karfi ba."

- Sanata Ndume

Sanata Ndume ya nemi a kafa rundunar SWC

Dan majalisar dattawan ya nuna bukatar kafa rundunar tsaro ta jiha (SWC) da za ta rika taimakawa dakarun soji a yaki da 'yan ta'adda, musamman Boko Haram.

“Saboda haka, ina amfani da wannan dama domin kira da a kafa wata rundunar tsaro ta al’umma domin taimakawa dakarun soji.
“Mun san cewa dakarun CJTF, maharba da masu sintiri suna kokari, amma suna da iyaka, domin galibinsu da kwari da sanda kawai suka ke aiki, wanda hakan yana hana su tunkarar 'yan ta'adda kai tsaye.
“Ina kuma kara nanata kira ga gwamnatin tarayya da rundunar sojin Najeriya da su yi amfani da fasaha, ingantanttun kayan aiki, bindigogi (TEAAM) domin kawo karshen barnar Boko Haram da ta shafe fiye da shekaru goma a Borno, Arewa maso Gabas da sauran sassan kasar."

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.