Sani Hamza
5185 articles published since 01 Nuw 2023
5185 articles published since 01 Nuw 2023
Majalisar tarayya ta mika sunayen mutum 11, ciki har da ‘ya’yan manyan ‘yan siyasa, domin ba su mukaman daraktoci a hukumar Cigaban Arewa maso Yamma (NWDC).
Dakarun Operation Fansan Yamma sun kashe Kachalla Na Faranshi a dajin Zurmi. Na Faranshi ya shahara wajen safarar makamai da kai hare-hare a Arewa maso Yamma.
'Yan bindiga sun kai hari karamar hukumar Sabuwa da ke Katsina, inda suka kashe mutane biyu, suka sace wasu, amma 'yan sanda sun ceci mutane 13 yayin dakile harin.
Mummunar gobara ta kashe dabbobi 78 a Danzago, jihar Kano. Hukumar kashe gobara ta ceto dabbobi da kayan amfani, yayin da jami’inta daya ya ji rauni a kafa.
Dakatar da ayyukan USAID ya kawo cikas ga rarraba kayan tazarar haihuwa a Bauchi, amma gwamnatin jihar ta ware N50m don tallafawa UNFPA wajen samar da kayayyakin.
Malaman Ebonyi sun shiga yajin aikin sai baba-ta-gani bayan wasu shugabannin kananan hukumomi sun gaza biyan albashin watanni uku na malaman firamare.
Gwamnatin Tarayya ta sanar da soke JSS da SSS, ta kuma gabatar da tsarin karatun bai daya na shekaru 12 wanda zai taimaka wajen inganta ilimi a Najeriya.
Marcelo ya sanar da ritayarsa daga kwallon kafa bayan shekaru 16 a Real Madrid, inda ya lashe Champions League 5 da La Liga sau 6. Ya bugawa Brazil wasanni 58.
Manjo Janar Chris Jemitola, tsohon mai tsaron lafiyar Olusegun Obasanjo, ya rasu bayan ya yanke jiki ya fadi a Abuja. Iyalinsa ba su sanar da lokacin jana’izarsa ba.
Sani Hamza
Samu kari