Gwamna Ya Kara Albashin Ma'aikata, Likitoci Za Su Fara Karbar N500,000 duk Wata

Gwamna Ya Kara Albashin Ma'aikata, Likitoci Za Su Fara Karbar N500,000 duk Wata

  • Gwamna Francis Nwifuru ya ƙara wa sababbin likitocin da aka dauka aiki a cibiyoyin kiwon lafiya na jihar Abonyi zuwa N500,000
  • Ya ce an kashe sama da Naira biliyan 10 wajen sabunta asibitoci da kayan aiki, tare da ɗaukar ma’aikatan lafiya 195 a fadin jihar
  • Gwamnatin ta raba kayan aiki na zamani da kaddamar da shirin da zai samar da ingantattun magunguna masu rahusa ga al’umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya sanar da ƙarin albashin N500,000 ga sababbin likitocin da aka ɗauka aiki a cibiyoyin kiwon lafiya na farko a faɗin jihar.

Nwifuru ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da shirye-shiryen farfaɗo da harkokin lafiya a jihar, da kuma rabon kayan aikin asibiti da kaddamar da shirin tallafin magunguna.

Gwamnan jihar Ebonyi ya kara wa sababbin likitoci albashi zuwa N500,000
Gwamnan jihar Ebonyi, Rt. Hon. Francis Ogbonna Nwifuru. Hoto: @FrancisNwifuru
Asali: Twitter

Gwamnan Ebonyi ya zuba N10bn a fannin lafiya

A cewarsa, gwamnatin jihar ta zuba sama da N10bn domin inganta asibitoci, samar da kayan aiki, da horar da ma’aikatan lafiya, kamar yadda rahoton Vanguard ya bayyana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Domin magance karancin ma’aikatan lafiya, gwamnan ya ce gwamnatinsa ta ɗauki kwararru 195 da suka haɗa da likitoci, nas-nas, ma’aikatan dakin gwaje-gwaje da masu bada magani.

Ya ce an tura sababbin ma’aikatan lafiyar zuwa asibitocin da ke gaba ɗaya fadin jihar domin tabbatar da ingantaccen aikin lafiya ga al’umma.

Gwamna Nwifuru ya ce:

“Wannan ba bikin ƙaddamarwa kawai ba ne, hujja ce ta aniyar mu ta gyara sashen lafiya a jihar mu. Kuma na daga cikin alkawuran da muka daukar wa al’ummarmu.”

Gwamna ya kaddamar da shirin tallafin magunguna

Gwamnan ya bayyana cewa an dade ana fama da ƙarancin kuɗi, kayan aiki, da ƙwararrun ma’aikata a fannin lafiya, kuma lokaci ya yi da wannan lamarin zai sauya.

“A yau muna ɗaukar matakan da suka dace ta hanyar ƙaddamar da shirin tallafin magunguna da za su isa ga asibitoci. Wannan zai tabbatar da cewa asibitocinmu ba za su sake rasa muhimman magunguna ba.
“Wannan shiri ne na ceton rayuka, musamman ga al’ummomin karkara, inda za su samu magunguna masu inganci a farashi mai rahusa.
"Tuni mun riga mun kammala fiye da kashi 60% na rabon magunguna, kuma ana ci gaba yin hakan har zuwa lokacin da za mu wadatar da asibitocin.”

- Gwamnan Ebonyi.

Gwamnan jihar Ebonyi zai gina asibitocin zamani bayan ya kara albashin likitoci zuwa N500,000
Gwamnan jihar Ebonyi, Rt. Hon. Francis Ogbonna Nwifuru. Hoto: @FrancisNwifuru
Asali: Facebook

Gwamna zai gina asibitocin zamani a Ebonyi

Gwamna Nwifuru ya ƙara da cewa gwamnati tana rabon kayan aikin asibiti na zamani irin su gadaje, matasai, na’urar auna lafiyar marasa lafiya, da sauran kayan amfani na gaggawa.

Ya bayyana cewa:

“Wadannan ba kayan ado ba ne, kayan aikin ceton rai ne. Wannan kudin da muka kashe da suka haura N10bn zai taimaka wajen farfaɗo da fannin lafiya a Ebonyi.”

Ya ce burin gwamnatin shi ne kafa asibitoci na musamman a kowanne yanki cikin yankuna uku na jihar, domin rage zuwa waje neman magani.

Gwamnan Ebonyi ya amince da albashin N75,000

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Ebonyi, Hon. Francis Ogbonna Nwifuru ya amince da N75,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan jihar.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun gwamnan, Monday Uzor, ya fitar a birnin Abakaliki.

Gwamna Nwifuru ya ce za a fara aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin ne a ranar Litinin, 28 ga watan Oktoban 2024, la'akari da halin da tattalin arzikin ƙasar nan ke ciki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.