Gwamnan Nasarawa Ya Kafa Kwamitin Yakin Zabe, Ya Fadi Kujerar da Zai Nema a 2027

Gwamnan Nasarawa Ya Kafa Kwamitin Yakin Zabe, Ya Fadi Kujerar da Zai Nema a 2027

  • Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana shirin tsayawa takarar sanatan Nasarawa ta Arewa a 2027, kamar yadda Suleiman Nagogo ya sanar
  • Suleiman, wanda shi ne daraktan hukumar kula da fansho ta jihar Nasarawa, ya ce Gwamna Sule ya kafa kwamitin neman takarar
  • Ya bayyana cewa karamar hukumar Wamba gida ne na APC, kuma za su bai wa gwamnan goyon baya a kudurinsa saboda ya cancanci hakan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya bayyana shirinsa na tsayawa takarar kujerar sanata mai wakiltar Nasarawa ta Arewa a zaɓen 2027.

Daraktan hukumar kula da fansho ta jihar, Suleiman Musa Nagogo, ne ya bayyana haka yayin wata ganawa da jagororin jam’iyyar APC a karamar hukumar Wamba, a ranar Talata.

Gwamnan jihar Nasarawa ya shirya tsaf, zai fito takarar sanata a zaben 2027
Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule. Hoto: @NasarawaGovt
Asali: Twitter

Gwamnan Nasarawa zai fito takarar sanata

Suleiman Nagogo ya ce gwamnan ya sanar da shi kai tsaye cewa yana da niyyar tsayawa takarar kujerar sanata a babban zaɓen 2027, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daraktan hukumar ya bayyana cewa:

"Na zo Wamba da saƙo mai muhimmanci daga mai girma Gwamna Abdullahi Sule, domin gabatar da wani lamari na siyasa ga mutanen karamar hukumata."
"Wannan saƙon shi ne sanar da ku su cewa mai girma gwamna ya na da kwadayin tsayawa takarar kujerar sanata a 2027."

Gwamna Sule ya kafa kwamitin yakin zabe

Suleiman Nagogo ya bayyana cewa saboda wannan kuduri, Gwamna Sule ya kafa kwamitin aiki domin shiryawa tsaf don gudanar da aikin takararsa a fadin Nasarawa ta Arewa.

"Kwamitin dai har yanzu yana a mataki na shirye-shirye, domin ba a kai ga wani mataki mai zurfi ba a aiwatar da aikin.
"Amma na ga dacewar sanar da ku, kamar yadda ake cewa komai yana farawa daga gida. Ya dace in sanar da al’ummata ta Wamba a kan wannan kuduri"

- Suleiman Nagogo.

Daraktan hukumar ya jaddada cewa Wamba gida ne na jam’iyyar APC, kuma yana sa ran mutanen yankin za su ba gwamnan cikakken goyon baya don wakiltar su a majalisar dattijai.

"A matsayina na ɗan asalin Wamba, na san ba wanda ya kai Abdullahi Sule ilimi, ƙwarewa da fahimtar siyasar wannan yanki," inji Suleiman Nagogo.
Gwamnan jihar Nasarawa ya kafa kwamitin yakin neman kujerar sanata a 2027
Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule. Hoto: @NasarawaGovt
Asali: Facebook

"Wannan aikinmu ne" - Suleiman Nagogo

Ya ce Gwamna Sule ya ɗauki Wamba tamkar gidansa, don haka babu wata hujja da za ta sa wani yanki ya fi su shiga gaba wajen mara masa baya.

"Shin ba aikinmu bane mu tsaya a gaba wajen goyon bayan wannan kuduri? Wannan aikinmu ne. Aikin mutanen Wamba ne gaba ɗaya," in ji shi.

Vanguard ta rahoto Suleiman Nagogo ya kuma bayyana cewa dole ne su tunatar da jama'a irin ci gaban da gwamnan ya kawo a Nasarawa ta Arewa da ma fadin jihar gaba ɗaya.

'Abin da Arewa za ta yi wa Tinubu' - Gwamna Sule

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya ce yankin Arewa zai sake marawa Shugaba Bola Tinubu baya a zaben 2027 mai zuwa.

Ya ce mutanen Arewa za su cika alkawarin da suka ɗauka na mara wa ɗan Kudu baya domin ci gaba da rike shugabancin ƙasa.

Gwamnan ya bayyana cewa akwai wasu 'yan siyasa da ke ƙoƙarin tayar da jijiyoyin wuya da haifar da ruɗani don biyan muradunsu na kashin kai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.