Tashin Hankali: Magidanci Ya Cinna wa Matarsa da Ƴaƴansa Wuta, Ɗiyarsa Ta Mutu

Tashin Hankali: Magidanci Ya Cinna wa Matarsa da Ƴaƴansa Wuta, Ɗiyarsa Ta Mutu

  • Wani magidanci a jihar Abia, ya cinna wa kansa, matarsa da ƴaƴansa uku wuta bisa zargin matarsa Amarachi da cin amana a aurensu
  • Kungiyar lauyoyi mata ta bayyana damuwarta kan wannan aika-aika, inda ta nemi 'yan sanda su bi kadin wadanda aka ci zarafinsu
  • Yayin da aka tabbatar da mutuwar daya daga cikin ƴaƴan magidanci, wani rahoto ya nuna cewa matar da sauran ‘ya’yan biyu sun mutu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abia - An shiga tashin hankali a ƙauyen Onicha Ngwa, karamar hukumar Obingwa, jihar Abia, bayan wani magidanci ya cinna wa kansa da iyalinsa wuta.

Ƙungiyar lauyoyi mata ta duniya (FIDA) reshen jihar Abia ta yi Allah-wadai da wannann mummunan lamarin da ya faru da wannan iyali.

Ana zargin wani magidanci ya cinnawa kansa da iyalansa wuta a Abia, diyarsa ta mutu
Sufeta Janar na rundunar 'yan sanda, IGP Kayode Egbetokun. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Magidanci ya cinnawa iyalansa wuta a Abia

Rahoton Punch ya nuna cewa lamarin ya faru ne a tsakanin ƙarfe 1:00 zuwa 2:00 na daren ranar Asabar, 17 ga watan Mayun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce magidancin, mai suna Udochi Amala, mai shekara 40, ya cinna wa kansa wuta, da matarsa Amarachi da ‘ya’yansu uku, bisa zargin cin amana daga bangaren matarsa.

Rahotanni sun ce Udochi, wanda ke zaune a kauyen Amapuihe, karamar hukumar Osisioma, ya yi ƙoƙarin tserewa bayan faruwar lamarin, sai dai an cafke shi.

Wata yarinya daga cikin ‘ya’yansa ta rasu sakamakon ƙonewar da ta yi, kamar yadda rahoton ya nuna.

Abin da rahoton ƴan sandan Abia ya nuna

A cewar rahoton jaridar The Sun, Udochi ya shaida wa 'yan sanda cewa:

“Ina da matsala da matata, amma ni kai na ban san cewa matsalar za ta kai wannan matakin ba. Na gaji da rayuwar ne kawai.”

Ya kara da cewa bai taɓa kama matarsa, ‘yar asalin ƙaramar hukumar Ikwuano, da wani namiji ba, kawai yana zarginta ne.

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Abia, DSP Maureen Chinaka, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa ana ci gaba da gudanar da bincike.

Kungiyar FIDA reshen Abia, ta bayyana matuƙar damuwa da ɓacin rai kan lamarin, tana mai cewa hakan babban cin zarafin ɗan adam ne.

An nemi rundunar 'yan sanda ta gano gaskiya tare da hukunta magidancin kan kona iyalinsa
Sufeta Janar na rundunar 'yan sanda, IGP Kayode Egbetokun. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Ana zargin matar da ƴaƴanta biyu sun mutu

Matsayar kungiyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugabanta, Njideka Aniawonwa, da sakatariyarta, Eberechukwu Kanu Oji, suka fitar ranar Talata.

Ƙungiyar ta bukaci 'yan sanda da su gudanar da bincike mai zurfi tare da tabbatar da adalci ga waɗanda abin ya rutsa da su. Ta kuma yi kira da a tallafa wa waɗanda suka tsira daga harin.

FIDA Abia ta jaddada aniyarta wajen kare ‘yancin bil’adama, musamman mata da yara, tare da ƙarfafa jama’a su rika ba da rahoton duk wani lamari na cin zarafi.

Wani rahoto da ba a tabbatar da shi ba ya nuna cewa matar magidancin, Amarachi da sauran ƴaƴansa biyu sun rasu a daren Litinin yayin da suke samun kulawa a asibiti.

Fusatattu sun cinna wa jami'in NDLEA wuta

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani jami’in NDLEA, Aliyu Imran, ya mutu a Gadan-Gayan, Kaduna, bayan da wasu matasa suka banka masa wuta har lahira.

Lamarin ya faru ne bayan wani mummunan haɗarin mota da ya yi sanadin mutuwar mutum uku, inda shi Aliyu ya yi kokarin kwantar da tarzoma, amma abin ya ci tura.

An ce wasu fusatattun suka soka masa wuka tare da cinna masa wuta yayin da iyalansa suka dora alhakin mutuwarsa kan sakacin hukumar NDLEA.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.