Zaben 2027: Tinubu Ya Kama Sunan Jihar da Ke da Matukar Muhimmanci a Gare Shi

Zaben 2027: Tinubu Ya Kama Sunan Jihar da Ke da Matukar Muhimmanci a Gare Shi

  • Tinubu ya bayyana Legas a matsayin jiha mai matuƙar muhimmanci a zaɓen 2027, inda ya buƙaci magoya bayan APC su ƙara himma wajen wayar da kan masu zaɓe
  • Ya jaddada muhimmancin karɓar katin zaɓe na PVC, yana mai cewa samun katin shi ne hanyar da ’yan Najeriya za su yi amfani da ikonsu na zaɓe
  • A zaɓen 2023, Peter Obi ya kayar da Tinubu a Legas da ƙuri'u 582,454, duk da cewa Tinubu ya samu nasara a ƙananan hukumomi 11 cikin 20

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana jihar Legas a matsayin muhimmiyar jiha wajen zaɓen 2027.

Shugaba Tinubu ya kuma buƙaci magoya bayan APC su ƙara ƙoƙarin jawo masu zaɓe domin samun ƙuri'u masu yawa.

Tinubu ya fadi muhimmancin Legas
Mai girma Bola Tinubu a wajen yakin neman zaben APC Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Tashar Channels tv ta ce Tinubu ya yi wannan kira ne a ranar Lahadi, 22 ga watan Nuwamban 2026 yayin wani taron addu'a da aka gudanar a zauren ƙungiyar Yoruba Tennis Club da ke Legas.

Kara karanta wannan

Atiku ya janye daga takara a zaben 2027? An ji gaskiyar zance

Ya buƙaci magoya bayan jam'iyyar da su riƙa ziyartar maƙwabtansu domin wayar da kan jama'a da ƙarfafa musu gwiwar shiga harkokin zaɓe.

Tinubu ya buƙaci APC ta ƙara ƙuri'u a Legas

Shugaban ƙasar ya ce ƙalubalen da jam'iyyar ke fuskanta a yanzu bai kai na baya ba, amma hakan ba yana nufin ya kamata su yi sakaci ba.

Ya ce wajibi ne magoya bayan APC su tashi tsaye wajen tabbatar da cewa mutane da dama sun fito domin kaɗa ƙuri'a.

Tinubu ya kuma jaddada muhimmancin karɓar katin zaɓe na dindindin, wato PVC, domin kowane ɗan Najeriya ya samu damar amfani da haƙƙinsa na zaɓe.

Yayin da yake yi wa waɗanda suka halarci taron raha, shugaban ƙasar ya ce:

“Idan kana nan amma ba ka da PVC, to kawai ka zo ne domin cin amala da ewedu.”

Ya ƙara da cewa masu katin zaɓe suna da ikon amfani da shi a ranakun 16 ga Janairu da 6 ga Fabrairu, 2027.

Kara karanta wannan

"Tinubu ya gaza": An kwadaitar da 'yan Najeriya amfanin zaben Peter Obi a 2027

Tinubu ya yi magana kan ƙuri'un Legas

Shugaban ƙasar ya bayyana damuwarsa kan yadda jihar Legas ke da miliyoyin masu rajistar zaɓe, amma yawan ƙuri'un da ake samu bai kai abin da yake tsammani ba.

"A ganina, Legas ita ce babbar magana. Ta yaya za a samu masu rajistar zaɓe miliyan bakwai, amma a samu ƙuri'u 100,000 zuwa 200,000 kawai? Wannan gazawa ce.
“Ko da kun yi nasara, ku ce nasara dai nasara ce, a'a. Dole ne ku samar da mafi yawan ƙuri'un da za ku iya samu.” In ji shi
Tinubu na son a kara nemo kuri'u
Mai girma Bola Ahmed Tinubu na jawabi a wajen taro Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Tinubu zai samu kuri'u a Arewa

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa mai kula da Arewa, Dakta Ali Bukar Dalori, ya yi watsi da shakku kan yiwuwar Shugaba Bola Ahmed Tinubu samun ƙuri'u masu yawa a yankin Arewa a zaɓen 2027.

Dalori ya yi hasashen cewa Tinubu zai samu gagarumar nasara a dukkan jihohin Arewa 19 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng