DSS Ta Sake Cafke Wani Riƙakken Ɗan Bindiga da ke Ƙoƙarin Tafiya Aikin Hajji a Sokoto
- Jami'an hukumar DSS sun samu nasarar cafke Sani Aliyu Galadi a filin jirgin Sokoto yayin da yake shirin tafiya aikin Hajji zuwa Saudiyya
- Galadi wanda aka fi sani da “Mai Boxer,” yana cikin jerin waɗanda DSS ke nema na tsawon shekara guda kan zargin garkuwa da mutane
- DSS ta cafke shi a lokacin da ake yi wa alhazai tantancewar ƙarshe, yayin da hukumar ta ce za a gurfanar da shi da zarar an kammala bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto: Hukumar DSS ta kama wani da ake zargi da zama babban shugaban masu garkuwa da mutane, Sani Aliyu Galadi, a filin jirgin sama na Sultan Abubakar da ke Sokoto.
An cafke Sani Galadi a ranar 18 ga Mayu, 2025, da misalin ƙarfe 11:15 na safe, lokacin da yake shirin hawa jirgi zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana.

Asali: Facebook
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asali: Twitter
An cafke dan bindiga a sansanin alhazan Sokoto
An ce jami'an DSS sun gano Sani Galadi a wajen tantance alhazai na ƙarshe, kasancewar yana cikin jerin wadanda ake nema ruwa a jallo, sama da shekara guda, inji rahoton Premium Times.
Sani Galadi, wanda aka fi sani da "Mai Boxer," ɗan jihar Zamfara ne da ake zargin yana da hannu a hare-haren ‘yan bindiga da sace-sacen mutane a tsakanin hanyar Sokoto da Zamfara.
Wata majiya ta tsaro da ba ta so a bayyana sunanta ta shaida wa jaridar cewa DSS ta kama Sani Galadi ne a wajen tantance alhazai kafin tashin jirgi.
A cewar majiyar:
“An cafke shi a wajen tantancewa ta ƙarshe kafin jirgi ya tashi. Ana tsare da shi yanzu domin bincike kuma za a gurfanar da shi gaban bayan kammala komai.”
'Ba maniyaccin Sokoto ba ne - Hukuma
Faruk Umar, jami’i a hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Sokoto, ya shaida wa Punch cewa Sani Galadi ba maniyyacin Sokoto ba ne, ya fito a sunayen alhazan Zamfara da aka shirya tafiya da su ranar.
A cewarsa:
“Ba alhazan Sokoto ke tafiya yau ba, na jihar Zamfara ne. Jirgin alhazan Sokoto zai tashi ne gobe. Don haka wanda aka kama daga alhazan Zamfara ne.”
Ya ƙara da cewa binciken DSS wani bangare ne na yarjejeniyar da aka kulla da hukumomin alhazai domin tabbatar da tsaro a filayen jirgi.

Asali: Original
Yadda DSS ta cafke 'yan bindiga a 2023 da 2024
An rahoto cewa wannan aiki na DSS ya samo asali tun daga kama Abubakar Aliyu a 2024 a sansanin alhazai, wanda shi ma ake zargi da zama ɗan ta’adda daga Zamfara.
A shekarar 2023 ma jami’an tsaro sun kama wasu da ake zargi da ta’addanci tare da kama matansu da masu ba su bayanai a filin jirgin Sultan Abubakar bayan sun dawo daga Hajji.
Wadannan matakai suna daga cikin kokarin hana yawaitar garkuwa da mutane musamman a Arewa maso Yammacin Najeriya, inda Sokoto da Zamfara ke fama da matsalar.
An cafke dan bindiga a sansanin alhazan Abuja
A wani labarin, mun ruwaito cewa, DSS ta kama wani mutum da ake zargi da garkuwa da mutane, Yahaya Yakubu, a sansanin alhazai da ke Abuja a lokacin tantance alhazai.
Yakubu, mazaunin kauyen Paikon-Kore a Gwagwalada, Abuja, yana cikin jerin wadanda DSS ke nema kan laifin garkuwa da mutane a Abuja da kewaye.
Wadannan kamen ya nuna yadda DSS ke ƙara zurfafa bincike a sansanonin alhazai don cafke masu laifi da ke yunƙurin tserewa daga kasar da sunan aikin Hajji.
Asali: Legit.ng