2027: Kotu Ta Fatattaki Karar da aka Shigar da Dan Takarar ADC a Gombe

2027: Kotu Ta Fatattaki Karar da aka Shigar da Dan Takarar ADC a Gombe

  • Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Dukku/Nafada a jihar Gombe, Hon. Abdullahi El-Raheed, ya samu nasara a shari’ar da aka shigar da shi
  • Mai shari’a a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya yi watsi da ƙarar ne saboda rashin hujjoji, kamar yadda ɗan majalisar ya bayyana
  • Biyo bayan hukuncin, El-Raheed ya gode wa Allah da magoya bayansa, sannan ya miƙa hannun sulhu ga ɗan siyasar da ya kai shi ƙara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Dukku/Nafada a jihar Gombe, Hon. Abdullahi El-Rsheed, ya bayyana farin cikinsa bayan samun nasara a shari’ar da ta shafi cancantarsa ta neman zaɓe a ƙarƙashin jam’iyyar ADC.

Dan majalisar ya ce Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da aka shigar domin ƙalubalantar kasancewarsa ɗan jam’iyyar da kuma cancantarsa ta tsayawa takarar kujerar majalisar wakilai a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku ya magantu kan Rarara, ya fadi yadda Tinubu ya zama masa ala ka kai

El-Rashid Abdulahi a kotu
El-Rashid Abdulahi da lauyansa bayan hukuncin kotu. Hoto: Hon El-Rasheed Abdullahi
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamba, 2026 a Facebook ya bayyana cewa kotun ta yi hukunci da ya ba shi nasara ne saboda rashin isassun hujjoji daga wanda ya shigar da ƙarar.

El-Rsheed ya gode wa Allah

Ɗan majalisar ya fara sanarwarsa da kalaman godiya ga Allah, inda ya ce hukuncin ya ƙara tabbatar da muhimmancin samun kotuna masu zaman kansu da adalci wajen kare bin doka da oda.

Ya kuma gode wa Dr Bala Bello Tinka, shugabannin jam’iyya, abokan aikinsa a majalisar wakilai, magoya baya, abokan siyasa da sauran waɗanda suka mara masa baya a lokacin shari’ar.

Haka kuma, ya yaba wa lauyoyinsa ƙarƙashin jagorancin Danshitta Shittu Saheed, tare da lauyoyin hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) da na ADC, bisa ƙwarewa da jajircewarsu a shari’ar.

Taswirar jihar Gombe
Taswirar jihar Gombe a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

El-Rsheed ya kuma yi amfani da damar wajen miƙa hannun abota da sulhu ga ɗan siyasar da ya ƙalubalanci cancantarsa a kotu.

Kara karanta wannan

ADC ta gamu da cikas, kotu ta kori mutumin Atiku da ke takarar gwamna

Ya gayyace shi da magoya bayansa da su haɗa kai da shi wajen gina haɗin kai domin ci gaba da muradun al’ummar mazabar Dukku/Nafada.

Abin da ya jawo shari’ar

A cewar El-Rsheed, an shigar da ƙarar ne a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja domin ƙalubalantar kasancewarsa mamba a ADC da kuma cancantarsa ta neman kujerar majalisar wakilai mai wakiltar Dukku/Nafada a zaɓen 2027.

Sai dai ya ce kotun ta yi watsi da ƙarar saboda rashin hujjoji, lamarin da ya ba shi damar ci gaba da kasancewa cikin masu neman kujerar a ƙarƙashin jam’iyyar.

Nafiu Bala ya soki Atiku

A wani labarin, kun ji cewa shugaban tsagin jam’iyyar ADC, Nafiu Bala Gombe, ya yi wa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, izgili kan rikicin shugabancin jam’iyyar.

Nafiu Bala Gombe ya buƙaci Atiku ya koma unguwarsa domin ya yi rajistar zama ɗan jam’iyyar ADC a hukumance, bayan hukuncin kotu da ya soke amincewa da shugabancin jam’iyyar da David Mark ke jagoranta.

Ya kuma yi alƙawarin cewa zai yi la’akari da naɗa Atiku a matsayin shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na ADC a zaɓen 2027, yayin wata ganawa da ’yan takarar jam’iyyar a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng