Atiku Ya Janye daga Takara a Zaben 2027? An Ji Gaskiyar Zance
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya yi magaba kan batun cewa ya janye takararsa ta shugaban ƙasa a zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Atiku ya zargi masu yaɗa labarin janyewar da ƙoƙarin yi wa Shugaba Bola Tinubu aiki, ta hanyar kawar da babban abokin hamayyarsa
Ya buƙaci magoya bayansa su tanadi katin zaɓensu na PVC, su ci gaba da wayar da kan jama’a daga mazabu zuwa mazabu.
Atiku ya musanta jita jitar janyewa daga takarar shugaban kasa a zaben 2027
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya musanta jita-jitar cewa ya janye takararsa ta shugaban ƙasa a zaɓen 2027, yana mai bayyana labarin a matsayin ƙarya.
Atiku ya ce babu wani mataki da ya ɗauka na janyewa daga takarar, kuma burinsa shi ne ya lashe zaɓen da za a gudanar a ranar 16 ga Janairu, 2027.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da daraktan yaɗa manufofin kamfen ɗinsa, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Lahadi, 22 ga Nuwamba, 2026.
A cikin sanarwar, Atiku ya ce babu wata ƙungiya da za ta iya yanke masa shawarar janyewa.
Atiku ya musanta janye takara
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa wasu da ke ikirarin magoya bayansa ba su da ikon yin magana a madadinsa ko sanar da cewa ya janye daga takara.
Ya ce sanya hotonsa ko sunansa a kan allon tallata wani abu ba ya tabbatar da cewa mutumin da ya yi hakan magoya bayansa ne.
Atiku ya kuma yi zargin cewa masu yaɗa wannan labari na cikin wata ƙungiyar siyasa da ke fama da sauya sheƙar mambobinta.
A cewarsa, waɗannan mutane na amfani da dabarar APC ta gabatar da wasu a matsayin magoya bayan ɗan takarar da suke son ɓata wa suna.
Ya zargi masu yaɗa labarin da yi wa Tinubu aiki
Atiku ya ce duk jam'iyyar siyasar da ke yaɗa ƙaryar cewa ya janye daga takara, tana taimaka wa Shugaba Bola Tinubu ne.
Ya bayyana cewa irin wannan labari na ƙoƙarin kawar da babban abokin hamayyar shugaban ƙasar daga cikin masu neman kujerar shugaban ƙasa.
“Duk wanda ke yaɗa ƙaryar cewa na janye daga takara, yana yi wa Tinubu aiki ne. Idan ba na cikin jerin masu takara, to Bola Tinubu zai iya jiran a miƙa masa mulki ba tare da hamayya ba.
“Amma ina cikin wannan takara domin samun nasara, kuma ’yan Najeriya za su samu damar zaɓar wanda suke so,” in ji Atiku.
Atiku ya ce kamfen ɗinsa zai ci gaba
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce kamfen ɗinsa mai taken Affordable Life na ci gaba da isa ga al'ummomi a sassa daban-daban na Najeriya.
Ya bayyana cewa manufar kamfen ɗin ita ce mayar da hankali kan matsalolin da iyalai ke fuskanta, musamman yunwa da talauci.
A cewarsa, matsalolin ba kawai ana tattauna su a kafafen sada zumunta ba ne, domin suna bayyana a kasuwanni, gidaje da sauran al'ummomi.
“Yunwa da talauci ba sa cikin kafofin sada zumunta kawai. Suna cikin kasuwanninmu, gidajenmu da kowace al'umma da iyalai ke fama da wahalar sayen abinci da biyan kuɗin sufuri.
“Shi ya sa kamfen ɗinmu ke zuwa kowane lungu da saƙo na Najeriya. Ba na buƙatar wani ya janye takara domin ni, kuma ba zan janye wa kowa ba,” in ji shi.
Asali: Legit.ng