Kotu Ta Yanke wa Dan Uwan Ciyaman da Wasu Mutane 3 Hukuncin Kisa, Za a Rataye Su

Kotu Ta Yanke wa Dan Uwan Ciyaman da Wasu Mutane 3 Hukuncin Kisa, Za a Rataye Su

  • Kotun jihar Ebonyi ta yanke wa wasu mutane hudu hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda sun kashe wani Chinonso Elom a Ebonyi
  • Wadanda aka yankewa hukuncin su ne; Anthony Elom, Chibueze Onwe, Chukwuemeka Ugah da Uchenna Odono, ’yan Ohaukwu
  • Alkalin kotun, Esther Otah, ta ce duk da Anthony ne ya harbe Elom, sauran sun hada baki da shi, don haka kowa na da hannu a kisan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ebonyi - Babbar kotun jihar Ebonyi ta yanke wa mutum hudu hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda laifin kashe wani matashi, Chinonso Elom, mai shekara 26.

Kotun ta samu wadanda ake tuhuma da laifin hada baki da kuma kashe Elom wanda aka fi sani da “Oscar” a cikin jihar.

Kotu ta yanke wa mutane 4 hukuncin kisa bayan samunsu da laifin kashe dan shekara 26
An yanke wa mutane 4 hukuncin kisa a Ebonyi. Hoto: Sani Hamza/Staff
Asali: Original

An kashe marigayi Elom a ranar 5 ga watan Fabrairu, 2023 a garin Ngbo da ke karamar hukumar Ohaukwu a jihar Ebonyi, inji rahoton Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar ta tattaro cewa marigayin da kuma mutanen da aka yankewa hukunci duk 'yan karamar hukumar Ohaukwu ne a shiyyar Kudu-maso-Gabas ta Najeriya.

Yadda mutanen 4 suka yi kisan

Mutanen da aka yanke wa hukuncin sun hada da Anthony Elom (wanda aka fi sani da Tidy), Chibueze Onwe (Chief oo), Chukwuemeka Ugah (Parity), da Uchenna Odono.

Uchenna kanin shugaban karamar hukumar Ohaukwu ne mai suna Ikechukwu Odono, kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito.

An gano cewa a ranar 5 ga Fabrairu, 2023, wadannan mutum hudu sun hau wata motar Sienna dauke da tambarin wata jam’iyya mai tasiri a jihar sannan suka nufi titin Ndulo Umuogudu Akpu.

Sun tsaya a gaban wurin kasuwancin marigayin, kusa da kasuwar Okwo Ngbo, inda suka bukaci Chinonso Elom ya bayyana musu inda dan uwansa yake, wanda suka samu sabani da shi a baya.

An cafke mutum 4, an kai su kotu

Saboda gaza ba su bayanan da suke bukata, sai suka yi kokarin tilasta masa shiga motar. Da ya ki, sai Anthony Elom ya harbe shi da bindiga a kansa inda ya mutu nan take.

Mutuwarsa ta tayar da hankulan matasan kabilar Ngbo da suka fito yin zanga-zangar lumana suna neman a kama wadanda suka aikata laifin.

’Yan sanda sun cafke mutum hudu daga cikin wadanda ake zargi, yayin da na biyar, ThankGod Onwe, ya tsere, kuma aka gurfanar da su a gaban kotu bisa laifin kisan kai.

Kotu ta yanke wa mutum hudu hukuncin kisa ta hanyar rataya a Ebonyi
Taswirar Najeriya da ke nuna jihar Ebonyi. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Hukuncin da kotu ta yankewa mutanen

Alkalin kotun, Mai shari’a Esther Otah, a ranar Laraba ta bayyana cewa kotu ta samu isasshen shaidu daga masu gabatar da kara da kuma shaidun da suka tabbatar da cewa mutanen hudun sun kashe Elom.

Mai shari’a Esther Otah, ta ce ba a samu hujjojin kare kai daga wadanda ake tuhuma da za su wanke su daga laifin ba.

Mai shari’a Otah ta kara da cewa binciken da aka yi akan bindigar da aka kwato daga hannunsu ya tabbatar da cewa ita ce aka yi amfani da ita wajen kashe Elom.

Ta ce ko da yake Anthony Elom ne ya harbe shi, amma dukkaninsu suna da hannu dumu-dumu saboda sun hada baki wajen aikata wannan danyen aiki.

Alkalin ta jaddada cewa dukkansu za su fuskanci hukuncin laifin da suka aikata, duk da cewa mutum daya ne ya harba bindigar da ta kashe Elom.

Za a rataye mutane 5 a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kotun jihar Kano ta yanke wa mutum biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe Dahare Abubakar da suka zarga da maita.

Masu laifin sun bi Dahare zuwa gonarta a kauyen Dadin Kowa, Wudil, inda suka daba mata wuka sau da dama har ta mutu a ranar 15 ga Nuwamba, 2023.

Sai dai kotun ta wanke Nabi’a Ibrahim, wadda ake tuhuma ta shida, bayan da shaidu suka tabbatar ba ta cikin yankin a lokacin da aka aikata kisan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.