Da Gaske Ana Ta Hayya Hayya tsakanin Peter Obi da NDC kan Kudin Kamfen?

Da Gaske Ana Ta Hayya Hayya tsakanin Peter Obi da NDC kan Kudin Kamfen?

  • Jam'iyyar NDC ta yi magana kan batun cewa akwai sabani tsakaninta da Peter Obi kan kudaden kamfen
  • Mai magana da yawun kwamitin kamfen, Constance Ikokwu, ta bayyana rahotannin saɓani tsakanin jam’iyyar da ɗan takararta a matsayin ƙirƙirarren labari
  • Karyatawar ta zo ne bayan takaddama kan yadda za a sarrafa gudummawar kuɗin kamfen, bayan Aisha Yesufu ta ƙaddamar da shirin tara kuɗi domin takarar Obi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kwamitin kamfen ɗin jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ya musanta rahotannin da ke cewa akwai saɓani tsakanin ɗan takararta na shugaban ƙasa, Peter Obi, da shugabannin jam’iyyar kan kuɗin gudanar da kamfen ɗin zaɓen 2027.

Jam’iyyar ta bayyana cewa Obi bai taɓa ƙorafin ƙarancin kuɗin kamfen ba, kuma bai nuna rashin gamsuwa da yadda take tafiyar da harkokin kuɗin kamfen ɗinsa ba.

Kara karanta wannan

NDC a Kano ta fitar da kwamitin kamfen, ta saka sunan shugaban NNPP a ciki

NDC ta musanta sabani tsakaninta da Peter Obi
Peter Obi na jawabi a wajen taro Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Mai magana da yawun kwamitin kamfen ɗin NDC, Constance Ikokwu, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamban 2026.

Ta ce rahotannin da ke nuna cewa akwai rikici tsakaninsu wani yunƙuri ne na raba kan ’yan adawa gabanin babban zaɓen 2027.

NDC ta musanta zargin saɓani da Obi

Ta ce rahotannin da ke nuna cewa Obi da jam’iyyar na samun saɓani kan kuɗin kamfen ba gaskiya ba ne.

“Ina so na bayyana karara cewa Peter Obi bai taɓa yin ƙorafin rashin kuɗin kamfen ba, kuma bai nuna rashin gamsuwa da jam’iyyar kan batun kuɗaɗen gudanar da kamfen ba.” In ji ta.

Ta ƙara da cewa Obi na ci gaba da jajircewa wajen gudanar da kamfen, kuma tafiye-tafiyensa da ganawarsa da jama’a a sassa daban-daban na ƙasar na nuna ƙudirin da yake da shi na samun nasara a zaɓen 2027.

Jam’iyyar ta yaba da ƙoƙarin Obi

Kara karanta wannan

"Tinubu ya gaza": An kwadaitar da 'yan Najeriya amfanin zaben Peter Obi a 2027

Ikokwu ta ce babu wani ɗan takarar shugaban ƙasa a wannan zaɓe da ke gudanar da kamfen cikin kuzari, jajircewa da ci gaba kamar yadda Obi yake yi.

Ta bayyana cewa yadda yake ziyartar al'ummomi a faɗin Najeriya domin yaɗa manufofinsa ya isa ya nuna irin ƙudirin da yake da shi.

“Mu fayyace wannan batu: babu wani ɗan takarar shugaban ƙasa a wannan zaɓe da ke kamfen da irin kuzari, jajircewa da ƙoƙarin da Obi yake nunawa.
“Ƙudirin da yake da shi na isa ga ’yan Najeriya a sassan ƙasar a bayyane yake, kuma yana yin hakan yadda ya kamata. Kamfen ɗin da aka gudanar zuwa yanzu babban nasara ne.” In ji ta.

NDC ta ce tana da manufa guda da Obi

Mai magana da yawun kwamitin kamfen ɗin ta buƙaci ’yan Najeriya su yi watsi da abin da ta kira ƙirƙirar ce-ce-ku-ce domin haddasa rarrabuwar kai a jam’iyyar, jaridar TheCable ta kawo labarin.

Ta ce dangantakar da ke tsakanin NDC da ɗan takararta na nan daram, kuma dukkaninsu sun mayar da hankali ne kan samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Kara karanta wannan

Har yanzu Atiku na cikin jerin 'yan takarar shugaban ƙasa a shafin INEC? Bincike ya gano gaskiya

A cewarta, burinsu shi ne su ba ’yan Najeriya wata sahihiyar madadin shugabanci.

"Dangantakar jam’iyyar da ɗan takararta ta ta’allaka ne kan wata manufa guda, wato lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027 da kuma samar wa ’yan Najeriya sahihin zaɓin shugabanci.
“Waɗanda ke ƙoƙarin ƙirƙirar rikicin da ba shi da tushe kada su ɗauki burinsu a matsayin gaskiya. Muna tare, mun mayar da hankali, kuma mun ƙuduri aniyar samun nasara.” In ji ta.
NDC ta yi magana kan sabani da Obi
Peter Obi na jawabi a wajen taron jam'iyyar NDC Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Shugaban NDC ya magantu kan Obi

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) na ƙasa, Moses Cleopas, ya yi magana kan Peter Obi.

Moses Cleopas ya bayyana ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen shugaban kasa na 2027, Peter Obi, a matsayin fatan Najeriya na farfaɗo da tattalin arziki da sake gina ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng