Tinubu Ya Gamu da Gagarumar Matsala a cikin APC kan Shirinsa na Tazarce a 2027
- Ƙungiyar APC Northern Youths Forum ta ce ba za ta sake tallatawa ko yaƙin neman zaɓen mai girma Shugaba Bola Tinubu ba
- Ƙungiyar ta danganta matsayinta da matsalar tsaro, tsadar rayuwa da kuma zargin cewa gwamnatin Tinubu ta yi watsi da yankin Arewa
- Shugaban ƙungiyar ya zargi gwamnatin Tinubu da nuna son kai wajen rabon mukamai, yana mai cewa ta fifita na kusa da madafun iko
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Wata ƙungiyar siyasa mai suna APC Northern Youths Forum ta bayyana cewa za ta janye goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmad Tinubu a ƙoƙarinsa na neman wa’adin mulki na biyu a zaɓen 2027.
Sai dai ƙungiyar ta jaddada cewa mambobinta ba za su fice daga jam’iyyar APC mai mulki ba, amma za su yi aiki wajen ganin Tinubu bai sake komawa kan karagar mulki ba a Kano da sauran jihohin Arewa.

Kara karanta wannan
"Tinubu bai fi ya lashe jihohi 2 ba"; An yi sabon hasashe kan zaben shugaban kasa

Source: Facebook
Ƙungiyar matasan APC ta sauya matsaya kan Tinubu
The Guardian ta ce da yake magana da manema labarai ranar Asabar, 21 ga watan Nuwamban 2026 a Kano, sakataren ƙungiyar, Comrade Umar Chanji, ya ce matsalar tsaro, tsadar rayuwa da abin da ya kira sakaci da yankin Arewa ne suka sa suka ɗauki wannan mataki.
Umar Chanji ya ce ƙungiyar ta ƙunshi shugabanni da wakilai daga jihohin Arewa 19. Ya bayyana cewa ba za su ƙara tattara jama’a, tallatawa ko gudanar da kamfen domin neman wa’adin mulki na biyu na Tinubu ba.
Ya ce wannan mataki ya zo ne duk da irin gudummawar da mambobin ƙungiyar suka bayar wajen samun nasarar APC a zaɓen 2023, jaridar Tribune ta kawo labarin.
Ƙungiyar ta koka kan matsalar tsaro da tattalin arziki
Umar Chanji ya ce matakin nasu ya samo asali ne daga abin da suka bayyana a matsayin gazawar gwamnatin Tinubu wajen magance manyan matsalolin da ke addabar ’yan Najeriya, musamman mazauna Arewa.

Kara karanta wannan
APC ta bayyana gaskiyar da ta yarda da ita kan matsalar rashin tsaro a gwamnatin Tinubu
Ya bayyana rashin tsaro a matsayin ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka sa suka janye goyon baya, yana zargin gwamnatin tarayya da gaza kare rayuka da dukiyoyin jama’a yadda ya kamata.
Ya lissafa Katsina, Sokoto, Zamfara, Neja, Filato, Nasarawa, Benue, Kaduna, Kebbi, Bauchi, Taraba da Kogi a matsayin jihohin da ke fuskantar barazanar tsaro.
Hazalika ya kuma haɗa da Babban Birnin Tarayya Abuja, yana mai cewa ana ci gaba da samun kashe-kashe da lalata al’ummomi a waɗannan yankuna.
Ƙungiyar ta kuma soki manufofin tattalin arzikin gwamnatin tarayya, musamman cire tallafin man fetur, ƙarin haraji da kuma abin da ta kira rashin cika alkawuran gyaran matatun man Najeriya.
Matasan sun tambayi amfanin cire tallafin man fetur
Sakataren ƙungiyar ya kuma soki yadda gwamnatin Tinubu ke karɓar sababbin basussuka domin gudanar da ayyuka, duk da cewa ta cire tallafin man fetur.
“Mun damu da tsadar rayuwa da kuma ci gaba da karɓar basussuka. An gaya mana cewa an cire tallafin man fetur ne domin a samu ƙarin kuɗaɗen gudanar da tattalin arzikinmu.
“Yanzu da aka cire tallafin man fetur, har yanzu muna karɓar basussukan ƙasashen waje. Ina amfanin kuɗaɗen da aka samu daga cire tallafin?” In ji shi.
Chanji ya kuma yi zargin cewa an yi watsi da matasan Arewa da suka yi aiki tuƙuru wajen tallata takarar Tinubu a zaɓen 2023 bayan da APC ta samu nasara.
Ya yi nadamar yadda wani kwamishina mai ci a Kano, wanda ya gayyaci ƙungiyar domin tattauna matsalolin da suke fuskanta, daga baya ya yi watsi da su.
Haka kuma ya musanta zargin cewa wasu ne ke ɗaukar nauyin ƙungiyar domin ta janye goyon baya ga Tinubu, yana mai cewa mambobinta da kansu ke ɗaukar nauyinsu.
An zargi gwamnatin Tinubu da son kai
Shugaban ƙungiyar, Alhaji Mustapha Tinubu, ya zargi gwamnatin Tinubu da nuna son kai wajen tafiyar da al’amuranta, yana mai cewa tana fifita mutanen da ke kusa da masu madafun iko.
“Bayan duk sadaukarwar da muka yi domin kawo wannan gwamnati kan mulki, sai aka yi watsi da mu. Gwamnati ta fi mayar da hankali kan waɗanda ke kusa da ita, maimakon waɗanda suka yi aiki da gaske domin samun nasararta.” In ji shi.
Shugaban ya yi kira ga shugabannin APC na ƙasa, jihohi da ƙananan hukumomi, da kuma matasan Arewa da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar, da su sake duba goyon bayansu ga neman wa’adin mulki na biyu na Tinubu.

Kara karanta wannan
2027: Sanatan Kano ya faɗawa Tinubu gaskiya kan ƙalubalen da APC za ta fuskanta a Arewa
Sai dai ƙungiyar ta fayyace cewa janye goyon bayanta ga Tinubu ba yana nufin za ta daina goyon bayan sauran ’yan takarar APC a yankin Arewa ba.

Source: Facebook
An shirya wa Tinubu addu'a
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya isa birnin Legas a ranar Asabar, 21 ga Nuwamba, domin halartar addu’a ta musamman da iyalansa suka shirya domin neman masa albarka.
Shugaba Tinubu ya isa Legas ne bayan halartar gangamin yakin neman zabensa na jam’iyyar APC a birnin Ibadan, babban birnin jihar Oyo, a ranar Asabar.
Asali: Legit.ng
