Wata Sabuwa: Gwamnatin Kano Ta Dakatar da Haska Labarina da Wasu Fina Finai 21
- Hukumar tace fina-finai ta Kano ta dakatar da haska fina-finan Hausa 22 bisa zargin saba wa al’adu da ɗabi’un Musulunci a jihar
- Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ya ce doka ta ba su hurumi, kuma suna aiki da jami’an tsaro da malamai don tabbatar da bin ƙa’ida
- An ce ana haska fina finan ba tare da izinin hukumar ba, sai aka dakatar da haska wasu, ciki har da Labarina, Garwashi da Dadin Kowa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - A ranar 19 ga Mayu, 2025, hukumar tace fina-finai ta Kano ta sanar da dakatar da haska fina-finan Hausa 22, lamarin da ya tayar da kura.
Hukumar ta umarci masu shirya fina-finai da masu haƙƙin mallaka su dakatar da haska fina-finan a dandalin YouTube da gidajen talabijin nan take.

Asali: Facebook
An dakatar da haska fina-finan Kannywood 22
Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ya shaida Arewa Radio Kano cewa matakin ya zama dole domin dakile abubuwan da suka saba wa al’ada da ɗabi’un Musulmi a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matakin ya biyo bayan wasu dokoki na baya da hukumar ta sanya, na haramta “Bikin Kauyawa” da ake yi yayin bukukuwan aure a jihar.
Hukumar tace fina finan ta ce doka ta ba ta hurumin tabbatar da cewa dukkannin fina-finai da sauran kayan dab'i sun dace da koyarwar addini da al’adu.
Abba El-Mustapha ya bayyana haɗin gwiwar hukumar da jami’an tsaro da shugabannin addini domin tabbatar da bin doka da samun goyon bayan jama’a.
Fina-finan Kannywood 22 da aka hana haskawa
Wannan doka na daga cikin sababbin dokokin da majalisar dokokin jihar Kano ta amince da su da suka ƙara wa hukumar karfin doka a watan Maris 2025.
Dokar ta baiwa hukumar ƙarin iko kan haramta haska duk wani fim da sauran shirye-shiryen talabijin ko dab'i da bai samu takardar izini kafin a fitar da su ga jama’a ba.
Fina finan da Abba El-Mustapha ya ce an dakatar da haska su su ne:
- Dakin Amarya
- Mashahuri
- Gidan Sarauta
- Wasiyya
- Tawakkaltu
- Mijina
- Wani Zamani
- Labarina
- Mallaka
- Kudin Ruwa
- Boka Ko Malam
- Wa Yasan Gobe
- Rana Dubu
- Manyan Mata
- Fatake
- Garwashi
- Jamilun Jidda
- Shahadar Nabila
- Dadin Kowa
- Tabarma
- Kishiyata
- Rigar Aro
Matakin ya jawo ce-ce-ku-ce, inda masu goyon bayan hukumar ke ganin matakin zai kare tarbiyyar matasa, yayin da wasu kuma ke ganin hakan zai takura masana’antar Kannywood.

Asali: Instagram
Dalilan dakatar da haska fina-finan Hausa 22
Sai dai, hukumar, a wani bayani da shafin Arewa Update ya fitar ya bayyana dalilan da ya sa hukumar ta dauki wannan mataki.
Rahoton ya ce wasu daga cikin fina-finan sun karya dokoki da ka’idojin hukumar, tare da fitar da su ba tare da samun izinin hukuma ko takardar tacewa ba.
Haka kuma, hukumar ta gano cewa fina-finai da dama ba su bi tsarin tacewa ba, inda wasu har an dora su a intanet ba da izini ba.
Hukumar ta ce rashin hadin kai da rashin gabatar da cikakken bayani kan abin da fim ya kunsa na daga cikin matsalolin da aka sanya wa ido.
Ta kara da cewa tana da alhakin tabbatar da cewa kowanne fim ya dace da al’adu, dokoki da kuma kare martabar Kannywood.
Ba wannan ne karon farko da ake dakatar da haska fina-finai ba a masana'antar Kannywood, hakan ya sha faruwa a lokuta mabambanta.
Lokuta da dama gwamnati da hukumomi kan duba yanayin da ke da alaka da bata tarbiyya tare da sanya dokar da za ta gurgunta haska fina-finan.
Kalli hirar da aka yi da Abba El-Mustapha a nan kasa:
Fina finan Kannywood da suka yi tashe a 2024
A wani labarin, mun ruwaito cewa, an samu gagarumin sauyi a harkar Kannywood daga sayar da CD zuwa sinima, YouTube da kuma kokarin shiga manhajojin duniya da dama.
A shekarar 2024, masu shirya fina-finai sun yi kokari matuƙa wajen samar da fina-finai masu kayatarwa da suka fi na baya armashi da salo.
Legit Hausa ta zayyana fina-finai biyar masu dogon zango da suka shahara a 2024, ciki har da Labarina, Gidan Sarauta, Manyan Mata da sauran su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng