'Yan Kwankwasiyya Sun Tunkari Gwamna Abba kan Zarge Zargen da Ya Dora Wa Kwankwaso
- Ƙungiyar Kwankwasiyya ta zargi Gwamna Abba Kabir Yusuf da ƙoƙarin ɗora wa Sanata Rabiu Kwankwaso alhakin sauya sheƙarsa zuwa APC
- Gwamnan ya yi iƙirarin cewa Kwankwaso ne ya tura shi wajen Shugaba Bola Tinubu domin tattauna yiwuwar komawarsu APC
- Ƙungiyar ta ƙalubalanci Abba áada ya gabatar da sahihan hujjoji kan yarjejeniyar da ya ce an cimma a shekarar 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Ƙungiyar Kwankwasiyya ta zargi Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ƙoƙarin ɗora wa tsohon ubangidansa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, alhakin matakin da ya ɗauka na sauya sheƙa zuwa APC.
Ƙungiyar ta mayar da martani ne kan wata hira da gwamnan ya yi, inda ya yi iƙirarin cewa Kwankwaso ne da kansa ya tura shi wajen Shugaba Bola Tinubu domin tattauna wata yarjejeniya da za ta ba su damar komawa APC.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Kwankwasiyya, Habibu Sale Mohammed, ya sanya wa hannu ranar Litinin, kamar yadda Leadership ta rahoto
Sanarwar ta ce:
“Gwamna na da ’yancin bayyana dalilan matakan siyasarsa da kare matakin sauya sheƙarsa, sai dai bai ba shi damar yin manyan zarge-zarge kan wani mutum ba tare da gabatar da sahihan hujjoji ba.”
Kwankwasiyya ta nemi cikakkun bayanai
Ƙungiyar ta ƙalubalanci Abba Gida-Gida da ya bayyana takamaiman bayanai kan yarjejeniyar da ya yi iƙirarin an cimma.
Kwankwasiyya ta ce:
“Idan Gwamna Abba ya dage cewa an yi wannan yarjejeniya, muna ƙalubalantarsa da ya gabatar da hujjojin da za a iya tantancewa.
"Yaushe aka cimma yarjejeniyar? Su waye suka halarta? Waɗanne tawagogi ne suka shiga tattaunawar? Mene ne sharuɗɗan yarjejeniyar? Akwai takardun da ke tabbatar da hakan ko shaidun da ba su da alaƙa da lamarin da za su iya tabbatar da bayaninsa?”
Ƙwankwasiyya ta jaddada cewa tattaunawar siyasa da ganawa ta sirri ba za su zama hujjar cewa Kwankwaso ko dukkan mambobin tafiyar Kwankwasiyya sun amince su yi watsi da akidunsu na siyasa ba.
Ta yi magana kan shari’ar zaɓen Kano
Ƙungiyar ta kuma nemi ƙarin bayani kan iƙirarin Abba cewa an tuntubi Shugaba Tinubu tare da roƙonsa da kada ya tsoma baki a shari’ar da aka ƙalubalanci sakamakon zaɓen Kano na 2023, wadda daga ƙarshe Kotun Ƙoli ta yanke hukunci a kanta.
Ta ce ’yan Najeriya na buƙatar sanin abin da ya faru, tare da yin gargaɗi kan duk wani yunƙuri na nuna cewa ana iya warware shari’a ta hanyar ciniki ko yarjejeniyar siyasa.
Sanarwar ta kuma tambayi dalilin da ya sa ake amfani da yarjejeniyar da ake zargin an cimma tun 2023 wajen kare matakin da gwamnan ya ɗauka na komawa APC a watan Janairun 2026.
Kwankwasiyya ta dage cewa bai kamata a ɗora wa Kwankwaso alhakin matakin da Abba ya ɗauka na shiga jam’iyya mai mulki ba, inda ta bukaci gwamnan ya kare wannan mataki bisa dalilansa.
Zarge-zargen da Gwamna Abba ya yi
Kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya tura shi wajen Shugaba Bola Tinubu domin yin alƙawarin komawa APC.
Abba ya ce sun yi yarjejeniya da Shugaba Bola Tinubu cewa idan bai tsoma baki a shari’ar zaɓen gwamnan Kano ba, za su koma jam’iyyar APC bayan samun nasara.
Asali: Legit.ng


