'Yan Ta'adda Sun Sha Azaba, Sojoji Sun Yi Masu Ruwan Wuta a Daji

'Yan Ta'adda Sun Sha Azaba, Sojoji Sun Yi Masu Ruwan Wuta a Daji

  • Sojojin Najeriya sun ce sun kashe ’yan ta’adda 37 tare da lalata motoci huɗu a hare-haren sama tsakanin 16 zuwa 23 ga Nuwamba, 2026
  • Rundunar Operation Hadin Kai ta kai hare-hare shida a wurare biyar, ciki har da Monguno, Kerenoa, Fage da Tumbuma Baba
  • Hare-haren sun kuma lalata wani sansanin ’yan ta’adda tare da dakile wani shiri da ake zargin mayakan ke yi na dasa bama-bamai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa ta kashe ’yan ta’adda 37 tare da lalata motoci huɗu a wasu hare-haren sama da ta kai a yankin Arewa maso Gabas.

Rundunar ta ce hare-haren, waɗanda aka gudanar tsakanin 16 zuwa 23 ga Nuwamba, 2026, sun kuma lalata wani wurin da ’yan ta’adda ke amfani da shi wajen shirya hare-hare.

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda
Dakarun sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Hedikwatar Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ne ya bayyana hakan ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamban 2026 a shafin Facebook.

Haka kuma, ayyukan sun taimaka wajen dakile wani shiri da ake zargin mayakan ke yi na haɗa bama-baman da ake dasawa a kan hanyoyin da sojoji ke bi.

Wuraren da sojoji suka kai hare-hare

Ya ce sashen rundunar sojin sama na Operation Hadin Kai ya gudanar da hare-hare shida a wurare biyar cikin yankin da take gudanar da ayyukanta.

A cewarsa, an gudanar da hare-haren ne bisa sahihan bayanan sirri da kuma sa ido na musamman ta amfani da jiragen leƙen asiri.

Wuraren da aka kai hare-haren sun haɗa da ƙaramar hukumar Monguno, Kerenoa da Fage da ke ƙaramar hukumar Marte, da kuma yankin Tumbuma Baba a ƙaramar hukumar Kukawa, duk a jihar Borno.

Goni ya ce a wani hari na farko da aka kai bisa bayanan sirri, binciken da aka gudanar bayan harin ya tabbatar da kashe ’yan ta’adda 10, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.

An lalata sansanin ’yan ta’adda da motoci

Ya bayyana cewa a wani samame na daban ranar 17 ga Nuwamba, na’urorin sa ido na sojoji sun gano wani wurin da ’yan ta’adda ke taruwa a Arina Chiki.

A cewarsa, bayanan sirri sun nuna cewa mayakan na shirin kai hari kan wuraren da sojoji ke amfani da su wajen kare kansu.

Goni ya ce sojojin sun kai wa wurin hari da makamai masu inganci, inda binciken da aka yi daga baya ya tabbatar da lalata ginin da aka farmaka. Ya ƙara da cewa ba a sake ganin wani motsi a cikin ginin ba bayan harin.

Haka kuma, ranar 20 ga Nuwamba, na’urorin sa ido sun gano motocin ’yan ta’adda guda biyu da aka ɓoye kusa da wani itace a Kerenoa. Sojojin sun kai musu hari ta sama tare da lalata motocin biyu.

A wannan rana, an kuma gano wata motar ’yan ta’adda a wani wurin da ake zargin ana haɗa bama-bamai a yankin Fage.

Goni ya ce bayanan sirri sun nuna cewa mayakan na shirin dasa bama-bamai a kan hanyar da sojoji ke amfani da ita.

Ya ce rundunar ta kai wa motar hari nan take tare da lalata ta, lamarin da ya dakile ayyukan da ake zargin mayakan ke shirin yi na amfani da bama-bamai.

An kashe wasu ’yan ta’adda 8 a Kukawa

Goni ya ce an sake samun nasara ranar 23 ga Nuwamba a yankin Tumbuma Baba da ke ƙaramar hukumar Kukawa.

Ya bayyana cewa wani samame da aka gudanar bisa bayanan sirri ya gano tare da lalata wata motar ’yan ta’adda.

A yayin aikin, an ga wasu mutane biyu da ake zargin ’yan ta’adda ne suna fitowa daga wani gini da ake amfani da shi wajen samar da muhimman abubuwan rayuwa.

Ya ce jami’an sa ido sun ci gaba da bin sawun mutanen har zuwa wani wuri da suka haɗu da wasu ’yan ta’adda shida a ƙarƙashin bishiya. Bayan wasu mayaka sun ƙara shiga cikin ƙungiyar, sojojin suka kai musu hari ta sama.

Goni ya ce binciken da aka gudanar bayan harin ya tabbatar da kashe dukkan ’yan ta’adda takwas, ba tare da an sake ganin wani motsi a wurin ba.

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda a Borno
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Amurka ta yaba wa sojojin Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa Amurka ta yaba wa rundunar sojin Najeriya kan ceto mutane 125 da aka yi garkuwa da su, tare da lalata sansanonin ’yan ta’adda yayin hare-haren soji da aka gudanar a sassa daban-daban na ƙasar.

Amurka ta kuma yaba wa dakarun sojojin na Najeriya kan ƙwato makamai da kuma gano tare da kawar da bama-bamai da aka binne a wurare daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng