Tashin Hankali: Mutane da Dama Sun Mutu da Aka Yi Yunkurin Kashe Sanata a Wurin Kamfe

Tashin Hankali: Mutane da Dama Sun Mutu da Aka Yi Yunkurin Kashe Sanata a Wurin Kamfe

  • Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, ya tsallake wani hari da ake zargin an shirya domin kashe shi a wurin kamfe a jihar Delta
  • Mutane huɗu sun mutu, yayin da wasu huɗu suka samu munanan raunuka a harin da aka kai masa a Uduere, ƙaramar hukumar Ughelli ta Arewa
  • Kwamitin kamfen y ce maharan sun yi ta harbi a kusa da sanatan, yayin da wani ganau ya tabbatar da cewa an harbi mutane a cikin taron

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Delta, Nigeria - Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa kuma ɗan takarar kujerar sanatan Delta ta Tsakiya a ƙarƙashin jam’iyyar NDC, Sanata Ovie Omo-Agege ya tsallake rijiya da baya.

Sanata Omo-Agege ya sha da kyar a wani harin da ake zargin yunkurin kisan gilla ne a lokacin rangadin kamfen a Uduere, ƙaramar hukumar Ughelli ta Arewa ta jihar Delta.

Kara karanta wannan

Abin da matasa suka yi wa Dauda Kahutu Rarara a masallacin Abuja ya fusata jigon APC

Omo-Agege.
Tsohon mataimakin shugaban Majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege Hoto: Ovie Omo-Agege
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa mutane huɗu sun mutu, yayin da wasu huɗu suka samu munanan raunuka a harin da ya faru a lokacin yakin neman zaben NDC.

Ƙwamitin yakin neman zaben Omo-Agege, a cikin wata sanarwa da mai ba ta shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunny Areh, ya fitar, ta ce wasu ’yan bindiga sun buɗe wa sanatan da tawagarsa wuta daga kusa.

Ya bayyana cewa maharan sun bude wuta ne yayin da yake jawabi ga taron jama’ar da suka taru domin tarbarsa.

A cewar kwamitin, Omo-Agege ya tsira daga harbin bindigar, inda ta ce harsasan sun wuce kusa da kansa.

Mutane huɗu sun mutu a harin

Ƙungiyar ta bayyana sunayen biyu daga cikin waɗanda suka mutu a matsayin mataimakanta, Moses Anaughe da Akima Efemena Umukoro.

Ta kuma ambaci sunayen waɗanda suka jikkata, wato Cif Evance Ivwurie, Chuks Erhire, Tobore Agba da Ayodo Wanogho, inda ta ce suna karɓar kulawar likitoci.

Kara karanta wannan

Rashin imani: Yan bindiga sun rutsa sarki da wasu bayin Allah suna cikin Sallah

Ƙungiyar ta ce shaidun gani da ido sun yi zargin cewa an ji maharan suna ihu suna cewa, “Omo-Agege muke son kashewa.”

Ta bayyana lamarin a matsayin yunkurin kisan gilla da aka shirya kai tsaye kan sanatan, ba rikicin siyasa ba.

Ganau ya tabbatar da harbin

Sai dai wani bidiyo da bazu kafafen sada zumunta ya nuna wasu magoya bayan NDC kwance cikin jini a ƙasa a wani asibiti da ba bayyana sunansa ba.

Delta.
Taswirar jihar Delta da ke Kudancin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Da aka tuntubi wasu shaidun gani da ido, ɗaya daga cikinsu mai suna Pius Eguono ya ce:

“Dukkanmu an harbe mu ne a cikin taron, amma an kashe Efemena Umukoro. Ina gudu domin tsira da raina.”

Gwamnan Delta ya gargaadi yan siyasa

Kun ji cewa Gwamna Sheriff Oborevwori ya soki ’yan siyasar da ke kai ’ya’yansu ƙasashen waje domin tsaro, amma suke amfani da yaran wasu wajen rikicin siyasa.

Gwamnan ya bayyana wannan hali a matsayin rashin adalci ga al’umma, inda ya bukaci shugabannin siyasa su kare matasa maimakon jefa su cikin haɗarin da ba dole ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262