Dubu Ta Cika: An Cafke Kasurgumin Mai Garkuwa da Mutane Yana Shirin Tafiya Hajji

Dubu Ta Cika: An Cafke Kasurgumin Mai Garkuwa da Mutane Yana Shirin Tafiya Hajji

  • Jami’an DSS sun cafke Yahaya Zango, wani mai garkuwa da mutane da ake nema ruwa a jallo, yana shirin tafiya aikin Hajji ta Abuja
  • Yahaya Zango ya nemi ɓoye kansa a sansanin alhazan Abuja, amma jami'an DSS suka gano shi, tare da cafke shi cikin gaggawa
  • Jama’a sun caccaki lamarin a intanet, inda wasu ke tambayar Yahaya abin da zai fadawa Allah game da zuwa Hajji da kudin ta'addanci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A ranar Lahadi, 18 ga Mayu, 2025, jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun kama Yahaya Zango, wani shahararren mai garkuwa da mutane, a sansanin alhazai na Abuja.

An kama Yahaya Zango ne yayin binciken tsaro da ake yi na yau da kullum ga mahajjatan da ke shirin tafiya aikin Hajjin bana zuwa Saudiyya.

Jami'an hukumar DSS sun cafke fitaccen mai garkuwa da mutane a sansanin alhazan Abuja
Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) suna a bakin aiki. Hoto: @OfficialDSSNG
Asali: Facebook

Jami'an DSS sun cafke mai garkuwa da mutane

Yahaya Zango, mazaunin unguwar Paikon-Kore a ƙaramar hukumar Gwagwalada da ke Abuja, yana cikin jerin mutane da hukumomin tsaro ke nema ruwa a jallo kan zargin hannu cikin garkuwa da mutane da dama, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiyar tsaro daga sansanin alhazan ta bayyana cewa Yahaya Zango ya yi ƙoƙarin ɓoye kansa cikin sahun mahajjata, inda ya gabatar da fasfonsa kuma ya tsaya a layin tantancewa a sansanin da ke kusa da filin jirgin sama.

Sai dai jami’an DSS, da suka yi amfani da bayanan sirri da ƙwararrun hanyoyin tantancewa, sun gano shi tare da cafke shi cikin gaggawa, kuma suka fitar da shi daga sansanin.

Wani babban jami’i daga hukumar jin daɗin alhazai, wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa, ya tabbatar da kama Zango, yana mai jami’an tsaro sun dade suna farautarsa.

"Me za ka fada wa Allah?" - Kawu Garba

Wannan kamun ya sake fayyace matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta, musamman a Arewacin ƙasar, inda garkuwa da mutane da hare-haren ‘yan bindiga ke ƙara ta’azzara.

Yunkurin Yahaya Zango na tserewa ƙasar da sunan zuwa aikin Hajji ya nuna yadda masu aikata laifi ke amfani da irin wadannan damarmakin don ɓoye kansu daga hukumomi.

Wasu masu amfani da dandamalin X sun bayyana ɓacin ransu kan lamarin, inda @KawuGarba ya bayyana jefi Yahaya da tambaya:

"Ta yaya zaka yi garkuwa da mutane, ka kashe su, ka karɓi kudin fansa, sannan ka yi amfani da kuɗin wajen zuwa aikin Hajji?
"Me za ka faɗa wa Allah a gabansa?”

Shi ma @ZagazOlaMakama ya bayyana damuwa kan lamarin, yana zargin cewa akwai yuwuwar wasu ‘yan bindiga hudu sun tsara su bi ta Abuja don zuwa aikin Hajji.

An cafke kasurgumin mai garkuwa da mutane yana shirin tafiya aikin Hajji
Alhazan Najeriya suna hawa jirgin sama da zai yi jigilarsu zuwa Saudiyya don aikin Hajji. Hoto: @nigeriahajjcom
Asali: Facebook

'Yan sanda sun nesanta kansu daga kamen

Kakakin rundunar ‘yan sandan FCT, SP Josephine Adeh, ta bayyana cewa aikin DSS ne kadai, inda ta nesanta rundunarsu da wannan kama, inji rahoton Leadership.

A halin yanzu dai, DSS ba ta fitar da wata sanarwa ba kan lamarin, lamarin da ya bar jama’a cikin jiran ƙarin bayani ko kuma yiwuwar kama wasu da ke da alaƙa da shi.

Kamen Zango na zuwa ne a dai dai lokaci da Najeriya ke fuskantar ƙalubalen tsaro mai tsanani, inda garkuwa da mutane da ta’addanci ke ƙara yawa.

An cafke jagoran masu garkuwa da mutane

A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar ‘yan sanda ta ceto mutanen da aka sace a Katsina, Akwa Ibom, Rivers, da Taraba, tare da kama wadanda ake zargi da laifuffuka.

An samu nasarar kwato makamai da dama, ciki har da bindigu kirar AK-47, rigar kariya daga harsasai, da kayan sojoji a jihohi.

Haka zalika rundunar ta yi nasarar cafke wani shugaban masu garkuwa da mutane tare da mai ba 'yan bindiga bayanai a jihar Taraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.