Yadda Gwamnoni 5 Suka Yi wa Atiku Buƙulu, Aka Hana PDP Samun Nasara a Zaben 2023
- Wani sabon littafi ya tona yadda ake zargin Nyesom Wike da gwamnonin G5 sun haɗa kai da su Bola Tinubu domin a raunana PDP
- ‘Yan G5 sun ƙarfafi takarar Peter Obi a jihohin da PDP ke da ƙarfi domin karkatar da ƙuri'un da Atiku Abubakar yake sa ran samu
- Dabarar ta taimaka wajen rarraba ƙuri'un 'yan adawa, abin da ya amfani Tinubu wajen lashe zaɓen, a cewar littafin Simon Kolawole
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - An samu sababbin bayanai kan yadda tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, da abokan siyasarsa suka yaki jam’iyyarsu a 2023.
‘Yan G5 a PDP sun yi aiki da Bola Tinubu domin kassara Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa da ‘dan takaransu na jam’iyyar PDP ya zo na biyu.

Source: Getty Images
An yi amfani da Peter Obi wajen cin zabe
The Cable ta ce abin da ya faru kuwa shi ne sun yi wannan ne ta hanyar ƙarfafar Peter Obi wanda ya tsaya takarar shugaban Najeriya a jam'iyyar LP.
‘Yan adawar sun yaƙi jam’iyyar PDP a wasu jihohin da ake ganin Atiku Abubakar yna da ƙarfi saboda kawai a gyara wa Bola Tinubu hanyar nasara.
‘Yan siyasar sun yi wasu ganawar sirri a biranen London da Paris saboda APC ta yi galaba a 2023.
Littafi ya tona dabarar da G5 suka yi
Simon Kolawole wanda marubuci ne ya shaida haka a littafin da ya rubuta: Winning Formula: The Inside Story of Nigeria’s 2023 Presidential Election.
An tsara cewa za a fara sayar da littafin ga jama'a a ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamba 2026.
A cewar littafin, Wike da abokansa a PDP sun haɗa kai da wasu gwamnonin jam'iyyar APC domin tsara dabarar zaɓe da za ta raunana Wazirin Adamawa.
Dabarar ta ƙunshi taiimakon Peter Obi a jihohin da PDP ke da ƙarfi, musamman inda ake ganin takarar Musulmi da Musulmi ba za ta kai labari ba.
Abin mamaki shi ne, Obi bai cikin wannan lissafi, kuma mai yiwuwa bai san cewa ana amfani da farin jininsa, an yi wasa da hankali da masoyansa ba.
Ganawar sirrin 'Yan G5 a London da Paris
A cewar Kolawole, dabarar ta samo asali ne bayan Atiku ya doke Nyesom Wike a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar PDP da aka yi a watan Mayun 2022.
Sannan aka yi watsi da shi, aka zaɓi Gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa a matsayin abokin gami.
Shawarar da su Atiku suka dauka shi ya fara jawo rashin jituwa tsakaninsa da ɓangaren Wike, kuma wannan ya taimaki Tinubu da jam’iyyarsa ta APC.
Mutanen Wike sun kunshi Gwamnonin jihohi - Samuel Ortom na Benue, Seyi Makinde na Oyo, Okezie Ikpeazu na Abia da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.
A ɓangaren Tinubu kuma, akwai gwamnonin APC: Atiku Bagudu na Kebbi, Mohammed Badaru Abubakar na Jigawa da Babajide Sanwo-Olu na Legas.
Marubucin ya ce na karshensu shi ne Kayode Fayemi wanda ya taba yin gwamna a jihar Ekiti.
Duka ɓangarorin biyu sun riƙa gudanar da tarukan tsara dabaru a wurare daban-daban, ciki har da London da Paris, domin APC ta ci zaben shugaban ƙasa.
An fahimci Atiku Abubakar ne babban ƙalulaben APC
Bayan nazarin manyan 'yan takarar, sun fahimci Atiku ne babban abokin hamayyar Tinubu a zaɓen.
Duk da cewa Obi yana samun karɓuwa sosai a tsakanin matasan kudancin Najeriya, sun lura cewa ba zai iya zama shugaban Najeriya a ƙarƙashin LP ba.
Don gana suka shiga shirya yadda za a lalata ƙuri'un PDP ta hanyar ƙarfafa mutane su zaɓi Obi a yankunan da Atiku yake sa ran samun nasara da kyau.
Lissafin da suka yi shi ne, ƙuri'un da Obi zai samu maimakon Atiku za su amfani Tinubu a ƙarshe, ko da kuwa jam’iyyarsa ba ta lashe waɗannan jihohin ba.
An samu Gabriel Ortom ya taimaki Peter Obi
Ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da masu goyon bayan Tinubu suka gano shi ne tikitin Musulmi da Musulmi, wanda ya jawo adawa daga wasu Kiristoci.
Saboda haka, mutanen Tinubu suka ba da shawara Gabriel Ortom, gwamnan Benue mai yawan Kiristoci, ya mara wa Obi a LP baya a maimakon Atiku.
A cewar Kolawole, abin da mutane da dama suka ɗauka a matsayin rashin fayyace matsayar Ortom kafin zaɓen, a zahiri wani ɓangare ne na dabarar siyasar.
Da sakamako ya fito kuwa Obi ya samu ƙuri'u 308,372 a Benue, inda ya zo na biyu bayan Tinubu, sai shi Atiku da ya yi takara a PDP ya samu ƙuri'u 130,081.
Idan aka kwatanta da zaɓen shugaban ƙasa na 2019, Atiku ya samu ƙuri'u 356,817 ne a jihar Benue.
Gwamnonin G5 sun mara wa Obi baya a Plateau
Littafin ya ce haka su Wike suka yi a jihar Plateau a 2023, wadda ita ma take da yawan Kiristoci.
Dama an gaya masu tikitin Musulmi da Musulmi ba zai karbu a Pleateau ba. A madadin haka sai suka taimaki LP don hana Atiku samun ƙuri'un da yake so.
Atiku, wanda ya samu ƙuri'u 548,665 a 2019, ya tashi da 243,808 kacal a 2023 shi kuwa Obi ya ci jihar da ƙuri'u 466,272, APC mai ƙuri'u 307,195 ce ta biyu.
Wike ya goge raini da abokan rikicin PDP
Kolawole ya ƙara nuna an yi irin wannan dabara jihohin Edo, Delta da Cross River, inda ake zargin Wike ya yi amfani da tasirinsa wajen kawo cikas ga Atiku.

Kara karanta wannan
Magana ta kare: Jam'iyyar adawa ta yanke shawara, ta umarci mabiyanta su zaɓi Tinubu a 2027
Tsohon gwamnan jihar Rivers yana da saɓanin siyasa da Okowa, mataimakin Atiku, da kuma Godwin Obaseki, wanda a lokacin shi yake Gwamna a jihar Edo.
Atiku da ya lashe Edo, Delta da Cross River a 2019 ya zo na uku a Edo da Cross River a 2023, sannan ya zo na biyu da tazara mai yawa a jihar Delta.
Obi kuwa ya lashe dukkan waɗannan jihohi uku kamar dai yadda ‘yan G5 suka tsara da APC. Ana zargin shi duk bai san yadda ta kaya a bayan fage ba.

Source: Getty Images
'Yan takaran 2027 sun gamu da tasgaro
Ana da labari cewa sabuwar baraka ta kunno kai a shirin 'yan adawa na tsayar da ɗan takara guda wanda shi za a bari ya gwabza da Bola Ahmed Tinubu.
Wannan takaddama ta kunno kai ne a daidai lokacin da shugabannin adawa suka sake ƙarfafa ƙoƙarinsu na cimma matsaya kan ɗan takara daya a 2027.
Zuwa yanzu babu wanda yake son ya goyi bayan wani tsakanin su Atiku Abubakar da Peter Obi.
Asali: Legit.ng



