Abin da Muka Sani kan Batun APC Ta Rubuta Wasika ga INEC don Tabbatar da Nasarar Tinubu

Abin da Muka Sani kan Batun APC Ta Rubuta Wasika ga INEC don Tabbatar da Nasarar Tinubu

  • APC ta yi magana kan wasiƙar da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta, wadda aka ce Nentawe Yilwatda ya rubuta wa INEC
  • Wasiƙar mai kwanan watan 22 ga Nuwamba, 2026, ta yi zargin cewa APC na son INEC ta yi amfani da ikonta wajen tabbatar da nasarar Tinubu
  • Jam’iyyar ta ce tana goyon bayan zaɓe cikin gaskiya, adalci da ’yanci, kuma ya kamata nasara ta fito daga ƙuri’un ’yan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta musanta sahihancin wata wasiƙa da ake zargin shugabanta na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya rubuta wa hukumar INEC.

Wasiƙar ta yi zargin cewa shugaban APC ya buƙaci INEC ta tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

APC ta yi magana kan batun rubuta wasika ga INEC
Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, na jawabi a wajen taro Hoto: Prof Nentawe Yilwatda
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, mai ba shugaban APC shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Abimbola Tooki, ya bayyana wasiƙar a matsayin ƙarya da kuma wani yunƙuri na bata sunan shugabannin jam’iyyar.

Ya ce an yaɗa takardar ne a kafafen sada zumunta da nufin ɓata sunan shugabancin APC da kuma raunana amincewar jama’a ga hukumomin dimokuraɗiyya.

Abin da wasiƙar ta ƙunsa

Wasiƙar da ake yaɗawa tana ɗauke da kwanan wata 22 ga Nuwamba, 2026, kuma an ce an aika ta ne ga shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan.

Takardar da ba ta da sa hannun wanda ya rubuta ta, ta nemi haɗin kan hukumar zaɓen gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

A cewar abin da ke cikin wasiƙar, shugabancin APC na sa ran INEC za ta yi amfani da tsarin gudanarwarta da sauran hanyoyin aikinta wajen tabbatar da ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Sai dai jam'iyyar APC ta ce ba Farfesa Nentawe Yilwatda ne ya rubuta wasiƙar ba, kuma ba ta fito daga ofishinsa ba.

APC ta ce wasiƙar ƙirƙirarriya ce

A cikin sanarwar, jam’iyyar ta ce takardar ba ta da alaƙa da shugaban jam’iyyar ko ofishinsa, tana mai cewa ba ta dace da tsarin sadarwa da APC ta saba amfani da shi ba.

Sanarwar ta ce:

"Jam’iyyar All Progressives Congress ta yi Allah-wadai da wata wasiƙa da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta, wadda ake zargin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, ya rubuta wa shugaban INEC.”

APC ta ƙara da cewa wasiƙar na ɗauke da zarge-zargen ƙarya da ke nuna cewa jam’iyyar na son hukumar zaɓe ta yi amfani da ikonta wajen tabbatar da nasarar Tinubu.

Ta bayyana takardar a matsayin wata takardar bogi da aka ƙirƙira domin ɓata sunan shugaban jam’iyyar, APC da tsarin dimokuraɗiyya.

Jam’iyyar ta kuma ce rashin sa hannu ko wata alamar tabbatar da sahihancin wasiƙar ya nuna cewa an ƙirƙire ta ne domin yaudarar jama’a.

Abin da APC ta ce kan sahihin zaɓe

APC ta yi kira ga waɗanda suka ƙirƙira wasiƙar da su fito fili su tabbatar da zarge-zargen da suka yi, maimakon ɓuya a bayan sunayen da ba a sani ba.

Ta ce ba za ta bari wasu boyayyun mutane da masu yaɗa bayanan ƙarya su jawo shugabancinta cikin abin kunya ba.

Jam’iyyar ta jaddada cewa tana goyon bayan gudanar da zaɓe cikin lumana, gaskiya, ’yanci da adalci a babban zaɓen 2027.

Ta ce tana mutunta ’yancin INEC da kuma damar ’yan Najeriya na zaɓar shugabanninsu ba tare da tsoratarwa, maguɗi ko katsalandan ba.

APC ta kuma ce Tinubu ya sha nuna goyon bayansa ga tsarin dimokuraɗiyya ta hanyar kira ga ’yan Najeriya, musamman masu cancantar kaɗa ƙuri’a, da su mallaki katin zaɓensu na dindindin (PVC).

A ƙarshe, jam’iyyar ta buƙaci ’yan Najeriya da kafafen yaɗa labarai su yi watsi da wasiƙar, tana mai cewa za ta shiga zaɓen 2027 da kwarin gwiwa.

APC ta ce ba ta rubuta wasika ga INEC ba
Mai girma Bola Ahmed Tinubu a wajen yakin neman zaben APC Hoto: Stanley Kingsley Nkwocha
Source: Facebook

Sowore ya soki Shugaba Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Omoyele Sowore, ya soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan katsewar ruwan da aka samu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar AAC ya bayyana lamarin a matsayin gazawar magance wata muhimmiyar buƙata ta more rayuwa a cibiyar gwamnatin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng