Ganduje Ya Yi Kamu: Ɗan Majalisar Wakilai da Wasu Ƙarin Mutane 1000 Sun Koma APC

Ganduje Ya Yi Kamu: Ɗan Majalisar Wakilai da Wasu Ƙarin Mutane 1000 Sun Koma APC

  • Hon. Sunday Umeha, dan majalisar Udi/Ezeagu, ya fice daga LP zuwa APC a wani taro da aka gudanar a Igboeze ta Kudu, jihar Enugu
  • 'Dan majalisar, Sunday Umeha, ya ce ya bar LP ne saboda rikicin cikin gida, tare da tabbatar da cewa APC za ta fi kawo ci gaba ga mutanensa
  • Hakazalika, Chief Joshua Ogbonna da mutane 1,000 na LP sun koma APC, wanda ke nufin cewa jam'iyyar mai mulki ta kara karfi a Enugu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Enugu - Jam’iyyar APC a jihar Enugu ta karɓi dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Udi/Ezeagu, Hon. Sunday Umeha daga jam'iyyar LP.

Sunday Umeha, wanda aka zaɓa a karkashin LP, ya sanar da sauya shekar sa zuwa APC a wani taron gangami da aka yi a karamar hukumar Igboeze ta Kudu.

Dan majalisar wakilai, Sunday Umeha ya sauya sheka daga LP zuwa APC
Dan majalisar wakilai daga jihar Enugu, Sunday Umeha. Hoto: @SundayUmeha
Asali: Twitter

Enugu: Mutane 1000 sun fice daga LP zuwa APC

A wajen taron, babban ɗan kasuwa kuma jigon LP, Chief Joshua Ogbonna, ya jagoranci mambobin jam’iyyar fiye da 1,000 zuwa APC, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake bayani kan dalilin halartar gangamin APC a wajen mazabarsa ta Udi/Ezeagu, Hon. Sunday ya ce ya yi hakan don nuna goyon baya ne ga abokinsa Chief Ogbonna.

Ya kuma bayyana cewa za a gudanar da wani babban gangami a Ezeagu don ƙaddamar da shi cikin APC a hukumance a 'yan kwanaki masu zuwa.

Dan majalisar ya tabbatar da cewa tuni ya fice daga LP tare da yin rajista da jam'iyyar APC a matakin gunduma a hukumance.

Dalilin dan majalisar wakilai na komawa APC

Ya bayyana rikicin cikin gida da ke addabar LP a matakin jiha da ƙasa a matsayin daya daga cikin dalilan da suka sanya ya bar jam’iyyar zuwa APC.

Sunday ya zama ɗan siyasa na farko mai rike da mukamin dan majalisa da APC ta samu tun kafuwar jam’iyyar a jihar a 2014, yana mai cewa ya shiga APC ne don kawo ci gaba wa al’ummar sa.

Ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta fi PDP amfani ga kabilar Ibo a matakin ƙasa, inda ya kafa misalai da aikin babban titin Enugu-Onitsha.

The Cable ta rahoto cewa ya kuma ambato titin Enugu-Port-Harcourt da gadar Najeriya ta biyu a matsayin manyan ayyukan da jam’iyyar APC ta aiwatar a yankin Ibo.

Dan majalisar wakilai daga Enugu ya sauya sheka daga LP zuwa APC
Taswirar Najeria da ke nuna jihar Enugu. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

APC ta yi maraba da masu sauya sheka a Enugu

Da yake jawabi yayin tarbar masu sauya sheƙar, shugaban APC na jihar Enugu, Barr. Ugochukwu Agballah, ya ce APC na shirin karɓar mulki daga PDP a a 2027.

Agballah ya ce mulkin PDP na shekaru 26 ya jefa jama’a cikin kunci ta hanyar haraji mai yawa, kwace filaye da rushe hanyoyin dogaro da kai don gina tashoshin mota da ya kamata a bar wa ƙananan hukumomi.

Ya gode wa Barista Peter Okonkwo daga Nsukka bisa bai wa jam’iyyar ofishin yaƙin neman zaɓe na yankin Enugu ta Arewa da kuma taimakawa wajen rushe tsarin LP a Igboeze ta Kudu.

'Yan majalisu 2 daga Enugu sun koma PDP

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jam’iyyar PDP ta samu karin mabiya a jihar Enugu cikin kasa da sa’o’i 24, bayan Hon. Dennis Agbo ya fice daga jam’iyyar LP.

Hon. Mark Chidi Obetta da Hon. Malachi Okey Onyechi sun sanar da sauya shekar su zuwa PDP, jam’iyyar da ke rike da ragamar mulki a jihar.

Shugaban PDP ya karɓe su hannu bibbiyu, yana mai cewa akwai karin fitattun ‘yan siyasa da za su biyo baya cikin jam’iyyar nan kusa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.