Shugaba Tinubu Ya Samu Matsala Yana Aske Gemu a Fadar Shugaban Kasa

Shugaba Tinubu Ya Samu Matsala Yana Aske Gemu a Fadar Shugaban Kasa

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa har fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock na fuskantar matsalar katsewar ruwa da wutar lantarki
  • Tinubu ya ce ruwa ya tsaya masa a lokacin da yake aske gemunsa a makon da ya gabata, inda ya yi alƙawarin gyara matsalolin Najeriya
  • Shugaban ƙasar ya kuma buƙaci magoya bayansa su sasanta duk wani rikici a cikinsu tare da ƙara ƙoƙarin jawo masu PVC domin zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa matsalar katsewar ruwa da wutar lantarki da ’yan Najeriya ke fuskanta tana faruwa har a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock, Abuja.

Tinubu ya ce ruwan famfo ya tsaya masa a lokacin da yake aske gemunsa a makon da ya gabata, inda ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta magance matsalolin samar da ruwa da wutar lantarki a ƙasar.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Villa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Vanguard ta rahoto cewa shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin wani taron addu’a da iyalansa suka shirya domin girmama shi a Legas.

Tinubu ya samu matsala a Villa

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba ta makon da ya gabata, lokacin da yake aske gemunsa.

Ya ce:

“A ranar Larabar makon da ya gabata, ina aske gemuna sai ruwa ya tsaya. Ko a fadar shugaban ƙasa ma, ba ku san cewa akwai irin wannan ƙalubale ba.
“Ruwa ya tsaya. Za mu gyara duk waɗannan matsalolin. Babu wuta, babu ruwa, babu wutar lantarki, babu ci gaba.
“Mun fara ne kawai. Za mu iya yin hakan, kuma za mu yi wa Najeriya hakan.”

Tinubu ya nemi a haka kan jama'a

A wajen taron, shugaban ƙasar ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su ƙara himma wajen tabbatar da samun yawan ƙuri’u a babban zaɓen 2027.

Ya ce Legas na da masu rajistar zaɓe miliyan 7, amma samun ƙuri’u 100,000 ko 200,000 daga cikinsu abin damuwa ne.

Tinubu ya buƙaci magoya bayansa su riƙa zagaya unguwanni domin ƙarfafa wa jama’a gwiwar fitar da katunan zaɓensu na dindindin (PVC).

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na yi wa 'yan Najeriya jawabi. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya kuma yi kira ga waɗanda ke da saɓani a cikin tafiyar siyasar APC da su ajiye fushinsu, su sasanta tsakaninsu, su mayar da hankali wajen neman ƙuri’u.

Gwamnonin jihohin Legas, Kwara, Imo, Gombe da Kaduna na daga cikin waɗanda suka halarci taron addu’ar.

Tinubu zai tallafawa manoma

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin shirye-shiryen tallafa wa manoma da inganta samar da abinci a Najeriya.

Gwamnatin tarayya ta kuma bayyana cewa shugaban ƙasar ya amince da sake zuba jarin Naira tiriliyan 1.5 a Bankin Aikin Gona domin ƙarfafa ikonsa na bayar da rance mai sauƙi ga manoma.

Gwamnatin tarayya ta ce matakin na daga cikin alƙawuran yaƙin neman zaɓen Tinubu na 2023, kuma zai taimaka wajen faɗaɗa tallafin noma, bunƙasa samar da abinci da inganta rayuwar manoma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng