Ana Fargabar Hare Haren 'Yan Bindiga, Gwamna Ya Rantsar da Manyan Sakatarori 5
- Gwamna Caleb Mutfwang ya rantsar da sababbin manyan sakatarori biyar domin sauya fasalin aikin gwamnati a jihar Filato
- Ya bukaci sakatarorin da su kawo sauyi ta hanyar nuna kwarewa, gaskiya da amana don ma'aikatan jihar su yi gogayya da sauran jihohi
- Yayin da gwamnan ke kokarin karfafa shugabanci, a hannu daya, matsalar tsaro ta tilastawa sama da mutane 6,000 tserewa daga gidajensu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Filato - A yayin da jihar Filato ke fama da matsananciyar matsalar tsaro, Gwamna Caleb Mutfwang na ƙoƙarin ƙarfafa shugabanci ta hanyar sauya fasalin ma’aikatan gwamnati.
A ranar 19 ga Mayu, 2025, gwamnan ya rantsar da sababbin manyan sakatarori biyar a Jos, ya bukace su da su kawo tsare-tsaren da za su inganta aikin gwamnati a jihar.

Asali: Facebook
Mutfwang ya nuna muhimmancin samar da shugabanci mai cike da gaskiya da kwarewa, da zai inganta aiki a ma’aikatu, sassa da hukumomin gwamnati, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna ya rantsar da sababbin sakatarori 5
Ya bayyana damuwarsa kan yadda aikin gwamnati ke tafiya a jihar, inda ya ce abubuwa da dama sun lalace a ma'aikatu, hukumomi da sassan gwmanati na tsawon shekaru.
Gwamnan jihar na Filato ya bukaci sababbin manyan sakatarorin da su yi amfani da ƙwarewarsu don kawo sauyi a aikin gwamnati.
“Ina so ku sani cewa kun zo ne a lokacin da abubuwa da dama ba sa tafiya daidai a fannin aikin gwamnati. Wannan ne dalilin da ya sa muke son yin gyara sosai.
“Ina son mu tabbatar da cewa mun canja tsarin, mu gyara shi yadda zai kai matsayin da ma'aikatan gwamnati na jihar Filato za su iya gogayya da sauran jihohi a Najeriya.”
- Gwamna Caleb Mutfwang.

Asali: Facebook
Gwamna zai kawo matsalolin aikin gwamnati
Ya kuma bukaci sababbin manyan sakatarorin da su zama tsani ga ma’aikatan jihar da ke tasowa don su inganta yadda ayyuka ke gudana.
Wannan mataki na ɗaya daga cikin kokarin Mutfwang na sauya fasalin ma’aikatar gwamnati, kamar yadda aka gani a watan Janairun 2025, lokacin da ya ƙaddamar da kwamitin kula da ma’aikata na jihar Filato.
A lokacin, ya jaddada kudurinsa na kawo karshen matsalolin da ke addabar aikin gwamnari, irin su rashin zuwa aiki da sakacin ma’aikata, tare da goyon bayan amfani da fasaha wajen tafiyar da ayyukan gwamnati.
Sai dai hare-haren 'yan bindiga da ake ci gaba da fuskanta a jihar Filato na barazana ga waɗannan ƙoƙari da gwamnan yake yi.
Fiye da mutane 6,000 sun tsere daga gidajensu a ƙaramar hukumar Bokkos, inda wasu suka nemi mafaka a wuraren bauta, sakamakon hare-haren 'yan bindiga.
Mutane 54 sun mutu a farmakin 'yan bindiga
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ‘yan bindiga sun kashe aƙalla mutane 54 a wasu ƙauyuka shida a yankin Bokkos, tare da tilastawa mutane 2,000 yin hijira.
Hare-haren da aka kai ba su da tabbas kan musabbabinsu, amma sun zama mafi muni tun Disamba 2023, lokacin da fiye da mutane 100 suka rasa rayukansu a yankin ɗaya.
Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya umurci hukumomin tsaro da su kamo masu laifin, tare da tabbatar da cewa za su fuskanci “hukunci mai tsanani.”
Asali: Legit.ng