An Taso Gwamnati a Gaba, Ana So Dole Tinubu Ya Tsige Matawalle da Ministoci 2

An Taso Gwamnati a Gaba, Ana So Dole Tinubu Ya Tsige Matawalle da Ministoci 2

Abuja - Matsalar tsaro da ta wutar lantarki da ke ƙara ta’azzara a Najeriya ta haifar da rashin jin daɗi a cikin jama’a, wanda ya kai ga ƙara yawan kiraye-kirayen korar wasu manyan ministocin gwamnati.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kungiyoyi sun nemi Tinubu ya tsige ministocin tsari da na wuta
Ministan wuta, Adelabu | Shugaba Bola Tinubu | Ministan tsaro, Badaru. Hoto: @BayoAdelabu, @SundayDareSD, @Mohammed_Badaru
Asali: Twitter

Ministocin da ake magana a kansu sun haɗa da ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar; karamin ministan tsaro, Bello Matawalle; da kuma ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu.

Kungiyoyi daban-daban, masana, da ƙungiyoyin fararen hula sun bayyana damuwarsu game da aikin ministocin, inda suke zarginsu da rashin iya aiki, da kuma gaza magance ƙalubalen ƙasa masu muhimmanci.

A wannan rahoto, mun kawo cikakken nazari kan waɗannan kiraye-kiraye da aka yi na tsige ministocin, da kuma dalilan da aka bayar:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Ministan tsaro: Mohammed Badaru Abubakar

Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya fuskanci suka saboda tabarbarewar yanayin tsaro, musamman a Arewacin Najeriya, inda ƙungiyoyin ‘yan tawaye irin su Boko Haram da ISWAP suke ci gaba da yin barna.

Kiraye-kirayen korarsa sun samo asali daga zargin rashin iya aiki, zarge-zargen ba da kwangila, da kuma gaza shawo kan tashin hankulan da ke ƙaruwa.

  • Kungiyar Neja Delta (NDYC)

Kungiyar matasan Neja Delta (NDYC) ta fito fili ta nemi Shugaba Bola Tinubu da ya kori Badaru, tana mai kafa hujja da hare-haren da ake kai wa sansanonin sojoji a jihar Borno.

A cewar ƙungiyar, ‘yan ta'addan sun kai hari tare da kwace kayan aiki na soja masu muhimmanci, ciki har da tankuna, wanda ke nuna babbar gazawa a dabarun tsaro.

NDYC ta zargi Badaru da fifita bukatunsa na kashin kansa da na siyasa fiye da tsaron ƙasa, tana zarginsa da bayar da kwangilolin tsaro bisa siyasa maimakon cancanta, inji rahoton Vanguard.

Kungiyar ta nuna cewa akwai matsala ta tsarin gudanarwar aiki a cikin ma’aikatar tsaro, inda son rai na iya hana gudanar da ayyuka yadda ya kamata.

  • Kungiyar matasan Yarabawa ta AYPN

Kungiyar matasan Yarabawa ta AYPN, ta goyi bayan zargin NDYC, inda ta bayyana Badaru a matsayin “dan kwangilar wasu tsiraru a ma’aikatar tsaro.”

Mun ruwaito cewa, AYPN ta goyi bayan sukar da Hon. Yusuf Gagdi, ɗan majalisar tarayya daga jihar Plateau, ya yi wa shugabancin Badaru a zauren majalisar wakilai.

Yayin da shugaban AYPN, Olatunji Fadare, ya bayyana ma’aikatar tsaro a matsayin “kashin bayan tsaron Najeriya,” ya zargi Badaru da rashin iya aiki da kuma rashin himma wajen magance rikicin tsaro.

Kungiyar ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya sake fasalin tsarin tsaro, ya fara da korar Badaru, tana gargadin cewa rashin daukar mataki na iya lalata amincin jama’a ga ikon gwamnati na kare rayuka da dukiyoyi.

  • Opialu Fabian, mai sharhi kan tsaro

Mai sharhi kan tsaro, Opialu Fabian, ya nemi Badaru ya yi murabus da kansa, saboda tabarbarewar tsaro da rashin isassun bayanan sirri, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Sukar Fabian ta dace da damuwa mai zurfi game da gazawar sojoji wajen hana hare-haren ‘yan tawaye, kamar yadda aka shaida a harin da aka kai sansanonin sojoji.

Ya bayar da hujjar cewa yawan kasafin kuɗi da aka ware wa sashen tsaro a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu bai kawo canji mai ma’ana ba, wanda ke nuna rashin gudanar da ayyuka a matakin mafi girma.

  • Ethics Vanguard da sauran kungiyoyin fararen hula

A ranar 12 ga Mayu, 2025, Ethics Vanguard, wata ƙungiya mai rajin kare gaskiya, ta nemi a kori Badaru nan take, tana mai cewa ko kadan bai san aikinsa ba.

Bayanin ƙungiyar, wanda aka yaɗa a kafofin sadarwa na zamani kamar X, ya nuna ƙaruwar rashin tsaro a matsayin shaidar rashin dacewar Badaru ga mukamin minista.

Sauran ƙungiyoyin fararen hula sun kuma sukar ministan, inda suka nuna cewa asarar kayan aikin soja da ƙaruwar ƙarfin ‘yan tawaye a ya isa ya sa a sallame shi daga aiki.

2. Ministan Jiha na Tsaro: Bello Matawalle

Bello Matawalle, karamin ministan tsaro, shi ma ya fuskanci suka daga jama'a, inda aka yi ta kiraye-kirayen korarsa, duk da cewa Tinubu bai amsa wadannan kiraye-kiraye ba.

An nemi Tinubu ya sallami Bello Matawalle saboda zargin rashawa da matsalar tsaro
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle. Hoto: @Bellomatawalle1
Asali: Twitter

Zarge-zargen da ake yi wa Matawalle sun fi mayar da hankali kan zamaninsa na gwamnan jihar Zamfara da kuma rashin iya ba da gudummawa mai ma’ana ga tsarin tsaron Najeriya.

  • Kungiyoyin fararen hula

A watan Oktoba 2023, gamayyar kungiyoyin fararen hula masu rajin kare gaskiya sun nemi a kori Matawalle, saboda zargin zamba a lokacin da yake gwamnan jihar Zamfara.

Kungiyoyin sun zarge shi da yin almubazzaranci da kuɗin jama’a da kuma gaza magance ‘yan fashi a jihar, wadda ya har yanzu ta'addanci ya ki karewa a jihar.

Duk da waɗannan zarge-zarge, Matawalle ya ci gaba da rike mukaminsa bayan sake fasalin majalisar ministoci a watan Oktoba 2024, wanda ke nuna cewa Tinubu bai dauki zarge-zargen a matsayin dalilin da zai sa a kore shi ba.

  • Kungiyar matasan Tinubu (TYN)

Kungiyar matasan Tinubu (TYN), wata ƙungiya mai goyon bayan jam’iyyar APC mai mulki, ta nemi a kori Matawalle a matsayin wani ɓangare na yunƙurin tabbatar da gaskiya.

Kungiyar ta bukaci Tinubu ya yi amfani da shirin sake fasalin majalisar ministoci don bincikar zargin alakar Matawalle da ‘yan fashi a jihar Zamfara da kuma zargin almubazzaranci da kuɗi.

Kiran TYN ya nuna matsin lamba a cikin jam’iyyar APC don magance zarge-zargen da ake yi wa manyan mukarraban gwamnati, musamman waɗanda ke da alaƙa da gazawar tsaro.

  • Martanin gwamnati kan jita-jitar korar Matawalle

A watan Afrilu 2025, jita-jita ta yaɗu a kafofin sada zumunta cewa Tinubu ya kori Matawalle, tare da Badaru da Adebayo Adelabu.

Sai dai fadar shugaban kasa, ta hannun Bayo Onanuga, mai magana da yawun Shugaba Tinubu, ya ƙaryata waɗannan rahotanni, da kiransu da 'labaran ƙarya'.

Kungiyar Guardians of One Nigeria (GON) ta kuma kare Matawalle, tana nuna ziyararsa ta aiki a jihar Borno tare da babban hafsan tsaro, Janar Christopher Musa, a matsayin shaida na himmarsa wajen magance rashin tsaro.

Duk da kare shi da aka yi, ana ci gaba da tattaunawa kan bukatar korar Matawalle, inda masu suka ke jayayya cewa zarge-zargen rashawa da ake yi masa ya lalata amincinsa a matsayin ministan tsaro.

Rashin samun ci gaba mai ma’ana wajen shawo kan ‘yan fashi, musamman a Zamfara, ya ci gaba da haifar da buƙatun korarsa daga minista.

3. Ministan wutar lantarki: Adebayo Adelabu

Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya fuskanci suka mai tsanani saboda ci gaba da rugujewar tushen wutar lantarki na ƙasa, rashin daidaiton wutar lantarki, da kuma ƙaruwar farashin wutar lantarki.

Ana so Tinubu ya sallami Adebayo Adelabu, ministan wuta saboda tabarbarewar wuta da durkushewar tashar wuta ta kasa
Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu. Hoto: @BayoAdelabu
Asali: Twitter

Waɗannan batutuwan sun sa ƙungiyoyi da yawa suka nemi ya yi murabus da kansa, yayin da wasu ƙungiyoyi suka kare shugabancinsa.

  • Kungiyar marubuta ta HURIWA

A watan Maris, 2025, kungiyar marubutan kare hakkin dan Adama (HURIWA) ta nemi Tinubu ya kori Adelabu, inda ta zarge shi da rashin iya aiki da fifita tafiye-tafiyen ƙasashen waje fiye da magance rikicin wutar lantarki.

Kungiyar ta nuna rugujewar tushen wuta da ake yawan samu, wanda aka ruwaito sama da 10 a shekarar 2024, a matsayin shaida na gazawar shugabancin ma'aikatar wuta a ƙarƙashin Adelabu.

HURIWA ta kuma soki ƙaruwar farashin wutar lantarki, wanda ya kara nauyi ga ‘yan Najeriya yayin da ake cikin wahalar tattalin arziki, inda ta ce manufofin Adelabu sun ƙara jefa mutane a wahala.

  • Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC)

Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta shiga cikin masu kiran a kori Adelabu a watan Janairu 2025, tana mai zargin cewa bangaren wutar lantarki yana gab da rugujewa gaba ɗaya.

NLC ta nuna yawaitar rushewar tushen wutar lantarki, wanda ke kawo cikas ga ayyukan tattalin arziki da rayuwa, a matsayin alamar rashin iya aikin Adelabu.

Kungiyar ta kuma soki kasafin kuɗin da aka ce za a ware don wayar da kan jama’a kan biyan kuɗin wutar lantarki, inda ta ce ya kamata a ware kuɗin don inganta samar da wuta.

  • Cibiyar CHRICED

A watan Afrilu, 2025, cibiyar haƙƙin dan Adam da ilimin jama’a (CHRICED) ta nemi a kori Adelabu, saboda tabarbarewar tushen wutar lantarki da kuma kudin da ake ware wa fanni a kasafi.

Cibiyar ta yi suka musamman kan ware kuɗi don sanya karamar tashar sola a Aso Villa, yayin da ta ce ƙasar ke fuskantar ƙarancin wutar lantarki.

CHRICED ta bayar da hujjar cewa irin waɗannan shawarwari da ake yanke wa na nuna rashin daidaituwa tsakanin manufofin ministan da bukatun talakawan Najeriya.

  • Gamayyar kungiyoyin COCOP

Sai dai kuma, gamayyar kungiyoyin COCOP ta kare Adelabu, tana kwatanta kiraye-kirayen korarsa a matsayin kuskure da kuma shirin siyasa kawai.

Kungiyar COCOP ta nuna ci gaba a sashen wutar lantarki, kamar yunƙurin inganta tashoshin watsa wutar lantarki da ƙara ƙarfin samar da wutar lantarki, inji rahoton Premium.

COCOP ta bayar da hujjar cewa ƙalubalen sashen wutar lantarki sun samo asali kafin a ba Adelabu mukami kuma suna buƙatar mafita na dogon lokaci.

Ƙalubalen sashen wutar lantarki, ciki har da rugujewar tushen wuta da ƙaruwar farashin wutar lantarki, sun ƙaru saboda matsin tattalin arziki, inda farashin kaya a Najeriya ya kai 23.71% a watan Afrilu 2025, a cewar COCOP.

An nemi Tinubu ya sake korar ministoci

A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban kungiyar masu kananan sana'o'i na kasa, Dr Femi Egbsola ya ce akwai bukatar duba wasu ministocin da ba su kokari a sallame su.

Dr Femi Egbsola ya kara da cewa idan aka yi dubi ga tattali da yanayin tsaro a Najeriya za a tabbatar da cewa har yanzu akwai sauran aiki.

Shi ma shugaban Intellectual Edge Service, Dr Olusegun Ogundare ya nemi Tinubu ya sallami karamin ministan tsaro, Bello Matawalle da ministan makamashi, Adebayo Adelabu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.