'PDP Za Ta Rasa Jihohin da Take Mulki a 2027': Jagoran Igbo Ya Fadi Matsalar Atiku

'PDP Za Ta Rasa Jihohin da Take Mulki a 2027': Jagoran Igbo Ya Fadi Matsalar Atiku

  • Dr. Nwachukwu Anakwenze ya gargaɗi PDP da kada ta sake tsayar da Atiku Abubakar tikiti a 2027, domin za ta rasa sauran jihohinta
  • Jagoran na Igbo ya nemi jam’iyyar da ta fito da sababbin shugabanni masu kwarewa da hangen nesa, wadanda za su iya kayar da APC
  • An nada Anakwenze a matsayin mai riƙon sarautar Abagana, inda ya yi alƙawarin horar da matasa da cigaba da ayyukan tallafi da ya saba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra - Tsohon mai neman takarar shugaban kasa, kuma tsohon shugaban kungiyar Igbo ta duniya, Dr. Nwachukwu Anakwenze, ya gargaɗi jam’iyyar PDP.

Dr. Nwachukwu ya gargadi PDP da kada ta kuskura ta sake tsayar da Alhaji Atiku Abubakar a matsayin dan takara a zaɓen shugaban kasa na 2027.

Jagoran Igbo ya ce PDP za ta rasa jihohin da take mulkinsu idan ta ba Atiku tikiti a 2027
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar. Hoto: @atiku
Asali: Getty Images

'Atiku ne matsalar PDP' - Nwachukwu

A cewar jagoran na Igbo, PDP za ta rasa rasa sauran jihohin da take mulki idan ta har ta ba Atiku tikitin takara, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr Nwachukwu ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a Abagana, karamar hukumar Njikoka a jihar Anambra, inda aka nada shi sabon mai riƙon sarautar yankin.

Tsohon mai neman takarar ya buƙaci PDP ta tsayar da masu jini a jika da ke da basirar iya kayar da jam’iyyar APC mai mulki a zaben mai zuwa.

Ya bayyana cewa:

“Ni ‘dan PDP ne. PDP na cikin matsala ne saboda mutane irin su Atiku ba sa son jam’iyyar ta yi nasara. Shi ne ɗaya daga cikin masu hana ta cigaba.”

Matsalar da ke hana Najeriya ci gaba

Dr Nwachukwu ya jaddada bukatar jam'iyyar ta samar da 'yan takara “da suka sha bamban da na yanzu, wadanda ke da kwarewa ta musamman wajen kawo canji mai ma'ana.”

Ya nuna damuwa kan yadda Najeriya ke da albarkatu masu yawa amma har yanzu ba ta samun cigaba ba saboda rashin shugabanni nagari.

Ya kuma soki yadda iko ke hannun wasu da ke fifita ƙabilanci da addini fiye da muradun kasa, yana mai cewa:

“A Najeriya, mutanen da ya kamata ace su na daure a gidan yari kan laifuffukan da suka aikata ne ke zartar da shawarwarin da suke tafiyar da rayuwar jama’a.”
An gargadi PDP da ta ka da ta kuskura ta tsayar da Atiku a matsayin dan takararta na 2027
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar. Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Dr. Anakwenze ya samu sarautar Abagana

Dr. Anakwenze ya karɓi matsayin mai riƙon sarautar Abagana ne bayan rasuwar sarkin garin, Mai martaba Igwe Patrick Mbamalu Okeke.

Gwamnatin jihar Anambra ta mika masa takardar tabbatar da nadin sarauta ta hannun ma’aikatar kananan hukumomi, sarautu da al’amuran jama’a.

Ya yi alƙawarin yin amfani da wannan damar wajen dora matasan Abagana kan turbar iya shugabanci na gari, inda ya nuna shirinsa na karɓar cikakken ikon sarautar idan al’umma suka ga ya cancanta.

Wanda ya fi cancanta PDP ta ba tikiti a 2027

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar PDP ta bukaci Alhaji Atiku Abubakar da ya janye niyyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027.

Ƙungiyar ta danganta faduwar darajar PDP da rawar da Atiku ya taka, musamman yadda ya jagoranci sauya shekar wasu gwamnoni biyar zuwa APC a 2014.

PDP 100 Percent ta jaddada cewa Kudu na da matasa ƙwararru da za su iya fafatawa da Bola Tinubu a 2027, tana ambato Gwamna Seyi Makinde a matsayin misali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.