Sanatan Zamfara Aka Kama a Bidiyo Yana Sumbatar Wata Mata? An Gano Gaskiya
Abuja - A kwanan baya, majalisar dattawa ta fuskanci matsin lamba daga jama'a bayan da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta zargi shugaban majalisar, Godswill Akpabio, da yunkurin cin zarafinta ta fuskar jima’i.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Asali: Twitter
A watan Fabrairu, 2025, Sanata Natasha, ta zargi Akpabio da yin yunkurin lalata da ita ba tare da amincewarta ba a shekarar 2023, zargin da Akpabio ya musanta.
Ko a shekarar 2016, Sanata Remi Tinubu, uwar gidan shugaban kasa na yanzu, ta zargi tsohon sanata, Dino Melaye da ikirarin zai yi lalata da iya har ta yi ciki, a cewar rahoton Reuters.
Wannan sabon zargi na Natasha ya kara rura wutar fushin jama'a, inda mutane ke neman gaskiya da adalci, musamman dangane da karin wakilci na mata da kare mutuncinsu a majalisa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana zargin sanata da lalata da mata a ofishinsa
A daidai lokacin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce, wani shafin Instagram mai suna @sorosokegossip ya wallafa bidiyo a ranar 14 ga Mayu, 2025, wanda ya nuna wani mutumi da ake zargi sanata ne yana sumbatar wata mata.
Taken bidiyon ya ce:
“An kama Sanata Sahabi Alhaji Yau, wakilin mazabar Zamfara ta Arewa, yana sumbatar wata mace a ofishinsa da ke majalisar tarayya, Abuja. Shi ya sa suke mara wa Akpabio baya.”
Daga ranar 15 ga Mayu, 2025, mutane sama da 4,400 suka nuna alamar 'sha'awar' bidiyon, mutane sama da 950 sun yi sharhi sannan mutane sama da 2,800 sun yada shi.
Wasu masu amfani da shafin sun gaskata zargin tare da caccakar ‘yan siyasa, yayin da wasu suka bayyana cewa bidiyon tsoho ne kuma ba shi da nasaba da sanatan da ake magana a kai.
Bincike kan bidiyon 'sanatan' Zamfara
Domin tabbatar da asalin bidiyon, shafin Dubawa ya gudanar da binciken “waiwayen baya na Google” ta hanyar amfani da hotuna da bidiyon da ke kan manhajar.
Sakamakon binciken ya nuna cewa bidiyon ya fara bayyana a watan Disamba, 2016. Rahotanni daga wancan lokaci sun nuna cewa mutumin da ke cikin faifan bidiyon shi ne hakimin ƙaramar hukumar Bodinga da ke jihar Sokoto, inda aka ce matar da ke cikin bidiyon matarsa ce, kuma ita ta ɗauki bidiyon.
Bayan bayyanar bidiyon a 2016, ya jawo ce-ce-ku-ce, inda daga bisani su biyun suka bayyana nadama tare da bayar da haƙuri ga jama’a.
Binciken kwatanta fuska da hotunan jikin mutumin da ke cikin bidiyon da na Sanata Sahabi Yau ya nuna bambanci a bayyane, duk da cewa suna da salon gashi da gemu iri ɗaya.

Asali: Twitter
Sanatan Zamfara ya yi martani kan bidiyon
Don ƙarin bayani, an duba shafin X na sanatan (@Danmadaminkaura), a ranar 14 ga Mayu, 2025, Sahabi Yau ya fitar da sanarwa game da bidiyon, yana mai cewa:
“Sanarwa: Hankalina ya kai kan wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta da ake cewa ni ne a cikinsa. Ina jaddada cewa ba ni bane. Za a ɗauki matakin doka kan duk wanda ya ƙi gogewa ko ya ci gaba da yada shi.”
Bidiyon ya ci gaba da yawo a wasu kafafe kamar Facebook da WhatsApp, musamman a wasu rukuni da aka sha kamawa da yada labaran ƙarya ko na jita-jita.
Sanatan ne a bidiyon?: Abin da bincike ya nuna
Zargin cewa Sanata Sahabi Yau ne ke cikin bidiyon da ke nuna wani mutum yana sumbata da shafa jikin wata mace a majalisar tarayya ƙarya ne.
Bidiyon ya samo asali ne tun shekarar 2016, inda aka tabbatar da cewa wani basarake ne daga jihar Sokoto tare da matarsa, ba Sanata Sahabi ba.
Wannan lamari wani salo ne na yaɗa ƙarya da gurbataccen bidiyo domin batar da jama’a da kuma tayar da zaune tsaye a harkar siyasa.
An yi auren diyar Sanata Sahabi Yau
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hotunan bikin kamun Ummi Sahabi Yau, diyar sanatan Zamfara ta Arewa, da angonta Muhammad Auwal, sun janyo hankalin jama’a.
Amaryar ta fito cikin shigar alfarma mai ɗaukar hankali lokacin da ta shirya ɗaura aure da masoyinta, Muhammad Auwal, wanda ya kasance rabin ranta.
Bikin ya samu halartar kyawawan ‘yan mata, samari masu salo, da ‘yan uwa na kusa da amarya da ango, inda suka nuna farin ciki da murnar wannan rana ta musamman.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng