'Yan Ta'addan Lakurawa Sun Kai Hari Kebbi, Sun Sace Mata Masu Yawa a Wurin Ibada
- Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan ƙungiyar Lakurawa ne sun kai hari a coci da ke kauyen Zagani, Danko-Wasagu a jihar Kebbi
- Shugaban karamar hukumar, Hussaini Aliyu Bena, ya ce ‘yan ta’addan sun shiga garin daga yankin Zamfara, kuma sun sace mata
- Gwamnatin Kebbi ta tabbatar da sace mutum 10, yayin da aka samu tabbacin cewa ana shirin tura jami'an tsaro domin kokarin ceto su
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kebbi - Wasu ‘yan bindiga da ake zargin 'yan ƙungiyar Lakurawa ne sun farmaki wata coci da ke kauyen Zagani, karamar hukumar Danko-Wasagu a jihar Kebbi.
A yayin farmakin, an ce 'yan ta'addan Lakurawan sun yi awon gaba da wasu mata masu yawa da ke yin ibada a yayin da ake gudanar da taron coci na ranar Lahadi.'

Asali: Facebook
'Yan bindiga sun sace mata a cocin Kebbi
Shugaban karamar hukumar Danko-Wasagu, Hussaini Aliyu Bena, ya bayyana wa Channels Television yadda 'yan ta'addar suka kai wa garin hari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hussaini Aliyu Bena ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kutsa garin da ke dab da iyakar Zamfara, inda suka sace matan da har yanzu ba a san adadinsu ba.
“A halin yanzu ba mu samu adadi ko sunayen su ba saboda matsalar sadarwa da ke yankin. Har yanzu ba a ji daga wadanda suka sace su ba."
- Hussaini Aliyu Bena.
Ya nuna damuwarsa kan yadda hare-haren ‘yan ta'addar ke ƙaruwa, yana ikirarin cewa ‘yan bindigar da ake zargin sun kulla yarjejeniya da gwamnatin jihar Zamfara yanzu sun mayar da Kebbi matsayin jiha mai sauƙin kai hare-hare.
Abin da shugaban karamar hukuma ya ce
Shugaban karamar hukumar ya ce gwamnatin jihar Kebbi ta yi ƙoƙarin tura jami’an tsaro zuwa yankin a bara, amma ambaliya da ruwan sama suka hana hakan.
Sai dai ya bayyana cewa sababbin shirye-shirye sun kammala don sake tura dakarun tsaro da yawa domin kare iyakokin jihar.
Ya ƙara da cewa wasu garuruwa da suka sha fama da hare-hare irinsu Dan Kade da Yar Tasha yanzu sun samu zaman lafiya sakamakon ƙarin dakarun da aka tura.
Shugaban karamar hukumar ya ce har yanzu ba a samu cikakkun bayanai kan sunan cocin ko na wadanda aka sace ba, amma ya ce za a bayyana komai yayin da ake kokarin ceto su.

Asali: Original
Gwamnatin Kebbi ta ce mata 10 aka sace
A nata ɓangaren, gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da cewa kimanin mutum 10 ne aka sace yayin harin.
Da yake magana da maneman labarai a yammacin Lahadi, sakataran yaɗa labarai na gwamna, Ahmed Idris, ya ce an raunata wasu masu ibada a yayin harin.
Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan Kebbi, Nafiu Abubakar, ya ci tura domin ba a samu isar da sako gare shi ba yayin haɗa wannan rahoto.
Kebbi: Lakurawa sun hallaka jami'an Kwastam
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ‘yan ta’addan da ake zargin ‘yan ƙungiyar Lakurawa ne daga kasashen waje sun kai mummunan hari kan jami’an Kwastam a jihar Kebbi.
A yayin harin da ya auku a ƙauyen Bachaka, karamar hukumar Argungu, an kashe jami’an Kwastam biyu tare da wani mutum guda da ke kusa da wurin.
Rundunar ‘yan sandan Kebbi ta tabbatar da harin, tana mai cewa hakan ba zai dakile azamar jami’an tsaro wajen yakar ‘yan ta’adda da kare al’umma ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng