'Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 15 a Kebbi, 37 Sun Mutu a Hatsarin Jirgin Ruwa

'Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 15 a Kebbi, 37 Sun Mutu a Hatsarin Jirgin Ruwa

  • 'Yan bindiga sun kai sabon hari kauyen Waje a jihar Kebbi, inda suka kashe manoma 15 tare da jikkata wasu uku a gonakinsu
  • Gwamnatin jihar ta aika da tallafi ta hannun mataimakin gwamna domin taimakawa iyalan mamatan tare da daukar matakin tsaro a yankin
  • A jihar Kwara, mutane 37 sun mutu a hadarin jirgin ruwa yayin dawowa daga kasuwa a Neja, sakamakon daukar mutane fiye da kima

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kebbi - Ana zargin ‘yan bindiga da kai hari kauyen Waje da ke karamar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi, inda suka kashe manoma 15 tare da jikkata wasu uku.

Mataimakin gwamna, Sanata Umar Tafida, wanda ya wakilci Gwamna Nasir Idris a ziyarar ta’aziyya ga hakimin Waje, ya nuna alhini game da lamarin.

'Yan bindiga sun kashe manoma 15 a Kebbi, gwamnati ta kai dauki
Jami'an 'yan sanda suna rangadi domin tabbatar da tsaro. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Gwamnati ta kai dauki garin da aka kashe manoma

Ya kuma sanar da bayar da tallafi daga gwamnatin jihar domin taimaka wa iyalan wadanda abin ya shafa, inji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Tafida ya ce wannan tallafi alamar kokarin gwamnati ne wajen sassauta radadin wannan masifa ga dangin mamata da wadanda suka jikkata.

Ya kuma tabbatar wa da al’ummar yankin cewa gwamnatin jihar za ta dauki matakan da suka dace wajen magance matsalar tsaro domin manoma su koma gona cikin kwanciyar hankali.

Yadda 'yan bindiga ke matsa wa garin Waje

Hakimin Waje, Hon. Bala Danbaba, ya yaba wa gwamnatin jihar bisa ziyarar da kuma tallafin da ya kira da wanda ya zo cikin lokaci kuma mai amfani.

Ya bayyana cewa yankin Danko Wasagu na makwabtaka da jihohin Neja, Zamfara da Sokoto, wanda hakan ke sanya su fuskantar hare-hare daga ‘yan ta’adda.

Ya roki gwamnati da ta dauki kwararan matakan tsaro domin toshe hanyoyin da maharan ke amfani da su.

Shugaban karamar hukumar Danko Wasagu, Alhaji Hussaini Aliyu Bena, ya tabbatar da mutuwar manoma 15 da raunata wasu uku a harin da aka kai.

Kwara: Mutum 37 sun mutu a hadarin jirgin ruwa

A wani labarin na daban, akalla ‘yan kasuwa 37 sun mutu sakamakon hatsarin jirgin ruwa a yankin Gbajibo-Mudi da ke jihar Kwara.

Rahotanni sun ce ‘yan kasuwar na dawowa ne daga kasuwar mako-mako da ke jihar Neja a ranar Alhamis lokacin da hadarin ya auku.

Jirgin, wanda aka ce yana daukar mutane 100 kadai, ya dauki mutane fiye da kima a ranar, inda aka danganta hatsarin da cikar kogin da kuma yawan fasinjoji.

Jirgin ruwa ya kife da sama da mutane 100, akalla mutane 37 sun mutu a Kwara
Jirgin ruwa ya yi hatsari da 'yan kasuwa a Kwara. Hoto: Zagazola Makama
Asali: Facebook

Yawan hadurran jiragen ruwa a Gbajibo Mudi

Jaridar Punch ta ruwaito cewa tsohon shugaban karamar hukumar, Mahmoud Gbajibo, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar.

Gbajibo ya ce tawagar ceto ta masu iyo sun samu nasarar gano gawarwakin mutane 37 daga cikin kogin bayan afkuwar lamarin.

“Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Alhamis, lokacin da ‘yan kasuwa ke komawa gidajensu daga kasuwar Gbajigbo Mudi da ke jihar Neja,” in ji Gbajibo.

A shekarar da ta gabata, wani jirgin ruwa mai dauke da mutane fiye da 200 ya kife a wannan yankin na Gbajibo Mudi.

'Yan bindiga sun kashe manoma a Kebbi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai mummunan hari kan manoma a jihar Kebbi da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Bena da ke karamar hukumar Danko/Wasagu, inda suka yi awon gaba da mutane 16, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Sai dai wasu daga cikin waɗanda aka sace sun samu nasarar kubuta, yayin da ake ci gaba da kiran gwamnati da ta ƙarfafa matakan tsaro a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.