Tsohon Gwamna Ya Nemi a Dakatar da Sarkin Daura kan Zargin Taba Baturiya
- Tsohon gwamnan Kaduna, Kanal Abubakar Dangiwa Umar (mai ritaya), ya buƙaci Gwamna Dikko Umar Radda na Katsina ya dakatar da Sarkin Daura
- Dangiwa ya nemi a dakatar da sarkin ne domin gudanar da bincike kan zargin cin zarafin wata mata ’yar ƙasar waje da ake dangantawa da shi
- Ya ce idan bincike ya tabbatar da zargin, ya kamata a sauke sarkin daga kan karagarsa ba tare da ɓata lokaci ba domin kare martabar masarautar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Kaduna, Kanal Abubakar Dangiwa Umar (mai ritaya), ya buƙaci Gwamnan Katsina, Dikko Umar Radda, ya dakatar da Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk.
Kanal Abubakar Dangiwa Umar (mai ritaya) ya yi kiran ne sakamakon zargin cin zarafin wata baƙuwa 'yar yawon buɗe ido.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa Dangiwa ya yi wannan kira ne a cikin wata wasiƙa da ya aika wa gwamnan, bayan yaɗuwar wani bidiyo a kafafen sada zumunta da ake zargin yana nuna sarkin yana aikata abin da bai dace ba ga wata mata farar fata.
Dalilin neman dakatar da sarkin
A wasiƙar, tsohon gwamnan ya buƙaci Gwamna Radda ya dakatar da sarkin nan take har sai an gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa da gaskiya kan zargin.
Ya ce idan aka tabbatar da zargin, hakan zai zama cin zarafin mutunci, iko da nauyin da ke rataye da sarautar gargajiya.
Dangiwa ya bayyana cewa sarautar sarki tana ɗauke da nauyin kare ɗabi’a, al’adu da tarihi, don haka ana sa ran wanda ke riƙe da ita ya kasance mai kamun kai da halin kirki.
Karin bayani daga Dangiwa
Tsohon gwamnan ya jaddada cewa dakatar da sarkin yayin da ake gudanar da bincike ba yana nufin an riga an same shi da laifi ba ne.

Kara karanta wannan
Zargin cin zarafi: Sarkin Daura ya shiga matsala bayan yaɗuwar bidiyonsa a Intanet
Ya ce matakin zai nuna cewa babu wani mutum, ko da kuwa yana da matsayi ko iko na gargajiya, da ya fi ƙarfin doka da yin hisabi kan ayyukansa.
Ya ƙara da cewa dakatarwar za ta taimaka wajen kare martabar masarautar Daura tare da bai wa hukumomin da abin ya shafa damar gudanar da bincike ba tare da katsalandan ba.

Source: Original
Dangiwa ya kuma buƙaci gwamnatin Katsina ta tabbatar da cewa lamarin bai rikide zuwa ce-ce-ku-ce a bainar jama’a ba, ko kuma ya ƙara ɓata martabar sarakunan gargajiya.
Maganar da Amnesty ta yi
A wani labarin, kun ji cewa ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International a Najeriya ta buƙaci hukumomi su gudanar da bincike kan zargin cin zarafin wata baƙuwar yawon buɗe ido da ake yi wa Sarkin Daura, Faruk Umar Faruk.
Ƙungiyar ta bayyana zargin a matsayin abin tayar da hankali, inda ta buƙaci gwamnatin jihar Katsina da ’yan sanda su gudanar da bincike mai zaman kansa da gaskiya domin tabbatar da an yi wa kowa hisabi.
A cikin saƙon da ta wallafa a shafinta a ranar Lahadi, Amnesty International ta ce lamarin wata dama ce ga gwamnati ta nuna cewa babu wanda ya fi ƙarfin doka a Najeriya.
Asali: Legit.ng
